Connect with us

MANYAN LABARAI

Sanata Ahmed Lawan Na Fuskantar Bore

Published

on


Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Al’ummar mazaɓar ɗan majalisar dattawa mai wakiltar arewacin Yobe (Zone C) a zauren majalisar dattawa kuma shugaban masu rinjaye; Sanata Ahmed I Lawan, sun koka dangane da halin ko-in-kula da yake nuna musu. Jama’ar mazaɓar sun yi ƙorafin tare da zargin cewa sanatan baya taɓuka musu wani abin a zo a gani, duk da halascin da suke nuna masa.

Bugu da ƙari kuma, jama’ar mazaɓar sanatan sun ƙara bayyana damuwar su da cewa da zarar sun zaɓe shi, ya tafi Abuja, ba zasu sake jin ɗuriyar sa ba, ballantana kuma ya saurari koken su ko buƙatun da zai isar musu a zauren majalisar; kamar yadda yake a ƙarƙashin dokar ƙasa, sai idan zaɓe ya ƙarato.

“Muna jin labarai ta kafofin sadarwa, wasu muna gani da idon mu dangane da ƙoƙarin da wasu sanatoci da yan majalisar wakilai ke yiwa al’ummar su. Babban abin mamaki shi ne mun kula kan cewa wasu daga cikin su ba su kai Dr Ahmed Lawan daɗewa ko riƙe muƙamai a zaurukan majalisun tarayyar ba, kuma muna kyautata zaton cewa yadda ake yiwa kowa haka shima ake yi masa. To abinda bamu fahimta ba a nan shi ne, wanne laifi muka yiwa wannan sanata namu da har yake nuna muna halin ko-oho?

Alhaji Muhammed Bulama, Nguru dake Jihar Yobe yana ɗaya daga cikin masu ƙorafin inda ya shaida wa Leadership A Yau cewa; “bisa haƙiƙanin gaskiya ni ɗan jam’iyyar APC ne kuma ɗaya daga cikin mutanen da suka yi ruwa da tsaki wajen zaɓen Sanata Ahmed Lawan, to amma gaskiya ba ma jin daɗin yadda yake tafiyar da siyasarsa a wannan yankin namu. Saboda idan ka duba kusan kowanne ɓangare na jihar Yobe ya ci gaba amma banda namu.

“Ɗauki ɓangaren Potiskum (zone B) da Damaturu (zone A) wallahi duk sun wuce mu ta fuskacin abubuwan ci gaba da more rayuwa da wakilan su suka jawo musu. Sanata Hassan Dambu ya gina babbar asibiti a Potiskum tare da baiwa jama’ar mazaɓar sa ƙwarin gwiwa wajen haɓaka al’amurran kasuwanci, sannan kowanne lokaci yana tuntuɓar jama’ar sa ya ji koke da buƙatun su. Ga Hon Goni Bukar Lawan; ɗan majalisar wakilai ne, amma kowacce shekarar Allah sai ya raba musu kayan ci gaba da bunƙasa tattalin arzikin jama’ar sa. Ya raba wa matasa motoci da babura masu bodi, injinan lambu da sauran su. To shi Sanata Ahmed ina nashi”? Yayi tambaya.

A nashi ra’ayin, babban mai binciken kuɗin a ƙungiyar muryar talaka na ƙasa, Ali Raskwana Gashuwa bayyana cewa yayi, “a matsayinmu na matasa kuma wakilan talakawa, muna kira ga irin su Dukta Ahmed Lawan da cewa su farka daga dogon baccin da suke domin su fahimci cewa yanzu fa kan mage ya waye. Talakawa a jihar Yobe ba zasu sake lamunta da halayyar a ci wawa a tsere ba. Lokaci ya wuce da za a zo ranar zaɓe a yaudari talaka da kuɗi ya jefa ƙuri’ar sa ga mutanen da basu damu dashi ba”.

Jigon muryar talaka ya sake nanata cewa, “an sha talakan Yobe ya warke; musamman na zone C, gaskiya mun gaji da irin wannan. Wannan bawan Allah ( Dr Ahmed) shi ne wakili a wannan yanki na arewacin Yobe tun daga 1999 zuwa yau. Yayi shekaru 8 a majalisar wakilai, ya dawo a majalisar dattawa yanzu yana na biyu, babu wani abin a zo a gani wanda ya yi wa jama’ar da ta zaɓe shi. Kuma iya halasci al’ummar wannan ɓangaren sun nuna mishi, amma ga abinda ya saka muna dashi; ai gobe ba rana ce”. Inji shi.

“Duk da sau tari muna jin wasu na ɓaɓatu da ƙarairayin cewa wai yayi aiki kaza da kaza, to ni kuma ina ƙalubalantar duk wani na jikin sa; a nan zone C ko daga Abuja, da cewa idan ya isa ya zo ya nuna muna aikin da Dukta Ahmed Lawan ya yiwa al’ummar wannan mazaɓa ta zone C. Saboda haka mu ba muna faɗar wannan domin suka ko cin zarafi ba, ko kaɗan, a matsayin mu na yan ƙasa kuma yan jihar Yobe, kuma haifaffun zone C muke wannan magana. Har wala yau, muna da yanci mu tuhume shi, saboda mu yake wakilta, to bai yi mana komai ba”. Ta bakin Raskwana.

Sanata Ahmed Lawan shi ne ɗan majalisar dattawa a yanzu kuma mai wakiltar mazaɓar arewacin Yobe a zauren majalisar. Yankin ya ƙunshi ƙananan hukumomin Bade da Jakusko, Yusufari da Karasuwa da Nguru tare da Machina.

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI