Connect with us

MANYAN LABARAI

An Yi Wa Ɗan Shekaru 70 Rajamu Har Lahira A Kano

Published

on


Daga Musa Ahmad, Kano

A jiya ne wani babban alƙalin majistire ta Birnin Kano, ya tasa ƙeyar wasu mutum biyar zuwa gidan yari kafin a ci gaba da sauraron shari’arsu, waɗanda ake zargi da laifin garkuwa tare da jefe wani tsoho ɗan shekaru 70 mai suna Usman Ɗanbuba.

Waɗanda ake zargin sune;  Wada Mohammed ɗan shekaru 30, Ya’u Muhammad ɗan shekaru 22, Musa Inusa ɗan shekaru 35, Sale Buba ɗan shekaru 27 da kuma Sule Garba ɗan shekaru 45.

Kotun ta zarge su da laifuka waɗanda suka haɗa da; shirya ɓarna, garkuwa, fashi da makami, kisa da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Kotun ta ce, an yi garkuwa da Danbuba ne a ranar 18 ga watan Mayu a ƙaramar hukumar Doguwa da ke Jihar Kano. Babban alƙali Aminu Fagge, ya bayar da umurnin cewa a ci gaba da tsare waɗanda ake zargin a gidan yari, har zuwa ranar 23 ga watan nan domin ci gaba da shari’a.

Ɗan sandan da ya shigar da ƙara, waɗanda ake zargin sun yi garkuwa da mamacin ne, inda suka yi masa fashin naira 85,000 da babur ɗinsa. “Bayan sun yi garkuwa da shi, sai waɗanda ake zargin suka ɗauke shi zuwa Tsaunin Shetu da ke dajin Falgore na jihar Kano, sannan suka nemi da a kawo kuɗin fansa naira miliyan biyar.” Inji ɗan sandan

Ya ƙara da cewa, lokacin da iyalan mamacin suka gaza haɗa wannan kuɗin, sai waɗanda ake zargin suka yi wa Ɗanbuba rajamu har lahira a ranar 22 ga watan Mayu.

Ɗan sanda mai ƙara ya zayyana cewa, waɗanda suke zargin sun aikata babban laifi wanda ya saɓa dokar sashe na 97, 17, 15 na dokokin ta’addanci, fashi da makami da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba. Sai dai ya zuwa haɗa wannan rahoton, waɗanda ake zargin sun ƙi amsa laifinsu.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI