Connect with us

LABARAI

Ƙungiyar Tuntuɓa Ta Makiyaya Ta Ɗauki Matakan Haɗin Kai

Published

on


Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Ƙungiyar tuntuɓa ta makiyaya da ta ƙunshi ƙungiyoyin ‘Miyatti Allah Cattle Beaders Of Nigeria’ da Miyatti Allah Kautal-Hore da ƙungiyar makiyaya ta Gan-Allah bisa jagoranci Arɗo Abdullahi Adamu Babayo, babban darakta mai kula da ilimin ‘yayan makiyaya ta jiha. Ta sha alwashin daƙile yawan tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma domin samun zaman lafiya. Babban daraktan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara wa shugaban riƙo na gidan radiyon jihar Neja, Bishop Andrew Achanya.

Arɗo Babayo ya ce,  sun kafa wannan ƙungiyar tuntuɓa ne don haɗa kan makiyaya da manoma da shiga tsakani akan matsalolin makiyaya da jami’an tsaro. Ya ce,  wannan haɗakar ba za ta goyi bayan kowanne makiyayi da bai da gaskiya ba, domin ko a kwanakin nan akwai wata matsala da ta taso a ƙaramar hukumar Shiroro inda aka ƙona ruggar fulani, wanda wannan wani manaƙisa ne na kawo saɓani tsakanin makiyaya da manoma, bayan dogon bincike sai muka fahimci ‘yan ta’adda ne suka shigo don kawo wani husuma wanda kuma mun daƙile shi, daman tun farko waɗannan makiyayan suna kotu da manoman yancin kuma kotu ta tabbatarwa wannan manoman da mallakin wajen amma kuma ba su cewa makiyayan su tashi ba, sai gaya ‘yan ta’adda sun shigo don kawo husuma.

Arɗo Babayo ya ce,  yanzu haka sun yi nisa wajen daƙile harkar beli wanda suka fahimci kusan shi ne jigon jefa ‘yayan makiyaya a halin da suke ciki, don haka ba za su lamunci ta’addanci ba ko kawo maƙarƙashiyya a zaman lafiya da ake yi a jihar nan. Duk wanda aka kama da laifi zamu yi tsaye wajen ganin an hukunta su, don haka duk wani abu da ya shafi gwamnati zai tafi a ƙarƙashin wannan haɗaka ne, amma ba mu hana duk wata ƙungiya yin ayyukan da ya da ce ba.

Daga cikin yarjejeniyar mu shi taushe duk wata kafa da zai baiwa baƙon makiyayi damar shigowa jihar nan, domin mun fahimci baƙin da ke shigowa su ne ke yawo ɗauke da makamai, mun yi zama da shugabannin tsaro a jihar nan, akan zasu ba mu goyon bayan daƙile duk wani baƙon makiyayi har sai mun tsaftace kan mu.

Saboda haka dukkanin waɗannan ƙungiyoyin na makiyaya sun tafi kura-kuran da suke tafkawa a daƙile shi, domin a Najeriya ne kawai ‘yan sanda ke karɓan kuɗi har sama da dubu ɗari a matsayin kuɗin beli kuma duk wannan na tafiya kafaɗa da kafaɗa da waɗannan ƙungiyoyin wanda mun dakatar da shi, saboda haka a ƙarshe sai aka jefa ‘yayan makiyaya akan fashi da makami da garkuwa da mutane, don haka matsayin da shugabannin mu suka ɗauka akan rashawa lallai ne zamu daƙile shi koda kuwa da jinin jikin mu.

Babayo ya ce,  maganar gaskiya waɗannan shugabannin fulanin sun san ‘yan fashi, sun san masu garkuwa da mutane, amma babban matsalar yadda jami’an tsaro kamawa kuma suna sake su, shi yasa kowa bai son faɗi kowanne mai laifi. Yanzu haka da kafa wannan ƙungiyar mun kama masu laifi mutum arba’in da biyar kuma suna gidan kaso.

Yanzu haka mun sanar da mutanen mu cewar duk inda wani marar gaskiya yake su sanar da mu kuma lallai zamu kai su inda za a hukunta su, ya ce,  ba da jimawa ba mun kama wani makiyayi da bindiga ƙirar AK7 ƙirar ingila kuma da harsasai kuma yana hannun jami’an tsaro, don haka lallai a jihar Neja ba zamu sanya ido zaman lafiya da ci gaban ƙasa na taɓarɓarewa ba.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI