Connect with us

LABARAI

Boko Haram Ta Ɓarnata Dukiyar Sama Da Tiriliyan Ɗaya A Borno

Published

on


Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

Gwamnatin Jihar Borno ta bayyana cewa ta dalilin matsalar tsaron da ta biyo bayan tada ƙayar baya na ƙungiyar Boko Haram ta yi asarar kimanin gidaje miliyan ɗaya da ɓarnata dukiyar da bata gaza naira tiriliyan ɗaya da ɗigo tara(N1.9tr) ba, a ƙananan hukumomi 27 dake faɗin jihar; cikin shekaru shidan da suka shuɗe.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin sakataren din-din-din a hukumar sake farfaɗo da sake gina garuruwa da yankunan da matsalar tsaro ta shafa a Jihar Borno, wato Alhaji Yerima Saleh a sa’ilin da yake zantawa ad manema labarai a babban birnin jihar dake Maiduguri.

Tun da fari, Alhaji Saleh ya bayyana cewa yan ƙungiyar sun ƙone garuruwa dubu casa’in da tmanin da shida, da ɗari huɗu da hamsin da uku (986, 453); ajujuwa 5, 335 da cibiyoyin kiwon lafiya 201. Sauran sun ƙunshi riyojin samar da ruwan sha 1, 630 da cibiyoyi da na’urorin bayar da wutar lantarki ɗari bakwai da ashirin da shida( 726 ) dake faɗin Jihar Borno.

Alhaji Saleh ya kuma ƙare bayyana cewa, ƙari ga hakan akwai ofisoshi na daban har guda ɗari takwas(800) da wannan ja’ifar ta shafa da suka ƙunshi gidajen yari, ofisoshin yan-sanda da makamantan su da yan ƙungiyar suka ƙone a jihar. Yayin da ya nuna cewa wannan ya haifar da sakamako maras daɗi ga al’ummar Jihar Borno dama ƙasa baki ɗaya.

“waɗannan rushe-rushe da ƙone-ƙonen sun jawo dole gwamnatoci haɗi da ƙungiyoyin bayar da tallafi su shigo domin bayar da agaji. Sannan kuma wannan tu’anatin ya afku ne a cikin ƙananan hukumomi 22 daga cikin 27 da wannan jiha ta Borno take dasu.” Inji shi.

Sakataren ya bayyana cewa, domin rage kaifin raɗaɗin wannan matsalar ne ya sanya gwamnatin Jihar Borno ta ƙirƙiro wannan ma’aikatar wadda aka ɗamƙa mata nauyin bin bahasin girman matsalar wadda kuma za taɗauki matakin sake gina waɗannan muhallan tare da aikin sake dawo da al’ummar garuruwan su na asali.

Haka kuma ya ce kawowa yanzu wannan ma’aikatar ta sake gina muhallan da aka rusa a cikin ƙananan hukumomi 14 dake Jihar Borno. “Gwamnatin Jihar Borno ta sake gina gidaje 25, 000 a cikin yankunan da jami’an tsaro suka yana. Yayin da a garin Bama kawai an sake gina gidaje sama 10,000, sa’ilin nan kuma a Gwoza aka kammala gina sama da gidaje 7,000.”

Bugu da ƙari kuma ya bayyana ɓangarorin da aikin nasu ya shafa, irin su ajujuwa, cibiyoyin kiwon lafiya, ofisoshin yan-sanda, hanyoyi da kasuwanni, kotuna da kwata, masallatai da coci-coci da makamantan su; a garuruwan da aka yanto daga mayaƙan.

“mun ƙuduri aniyar sake guna garuruwan Bama da Dikwa da Ngala. Yanzu haka zancen da ake ciki, wannan aikin ya doshi matakin kammalawa zuwa tsakanin kashi 50 zuwa 75 cikin ɗari.” Ya tabbatar.

Bugu da ƙari da cewa wannan aikin yana ci gaba da gudana a garuruwan ƙananan hukumomin Jihar Borno da suka ƙunshi Mafa, Dikwa, Ngala, Damboa, Chibok, Askira Uba, Mobar, Biu da Hawul.

Alhaji Yerima ya nusar da cewa gwamnatin jihar tana iya ƙoƙarin ta wajen ganin ta tallafa wa al’ummar jihar waɗanda wannan rikici na Boko Haram ya rutsa dasu a jihar.

“gwamnatin Jihar Borno haɗi da gwamnatin tarayya tare da ƙungiyoyin bayar da tallafi suna aiki kafaɗa da kafaɗa dangane da wannan matsala wadda matsalar tsaro ta haifar a Jihar Borno dama arewa maso-gabas baki ɗaya”. Ta bakin sakataren din-din-din.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI