Connect with us

MANYAN LABARAI

Dokar Gwamnati: Ta Hana Likitocinta Aiki A Asibitin Kuɗi

Published

on


Ba Za Ta Biya Kwanakin Yajin Aiki Ba

Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja

Gwamnatin tarayya ta fara bin matakan hana likitocinta ci gaba da zuwa yin wasu ayyukan a asibitocin kuɗi. wanda wannan ba sabon abu bane a tsakankanin likitocin Nijeriya.

Bayanan waɗannan dokoki da ake ƙoƙarin zartaswa sun fito ne daga bakin Ministan Lafiya, Isaac Adeƙole, da takwaransa Ministan ayyuka, Chris Ngige. Waɗanda suka shaida wa manema labarai cewa wannan wani mataki ne da gwamnatin tarayya ta ɗauka a taron majalisar zartaswar da aka gudanar jiya.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta kawo wannan dokar ne don ta magance yawaitar ma’aikatar bogi da ake fama da su. Musamman ma waɗanda ke shiga yajin aiki ba tare da cike sharuɗɗan yin yajin aiki kamar yadda doka ta tanada ba. Da kuma likitocin da ke zirga-zirga a tsakankanin asibitocin kuɗi domin yin wasu ayyukan nasu na daban.

A ta bakin gwamnatin, baya ga dokar daina biyan kwanakin yajin aiki, sannan akwai batun cewa a lokutan da ma’aikata za su kwashe suna yajin aiki ba za a ƙirga wannan kwanakin cikin kuɗaɗen fansho ɗinsu ba, kamar yadda Chris Ngige ya bayyana.

Ministan ya ce, wannan doka ce da tuntuni akwai ta a dokokin cinikayya, wanda kuma yayi kira ga ma’aikatu da ƙungiyoyin ƙwadago da su bibiyi dokokin don fahimtar yadda lamarin yake.

Ya ce; “Akwai lamurra da dama da muka tattauna su yau a zaman majalisar zartaswa. Dama kuma majalisar ta umurci Sakataren Fadar Gwamnati da ya samar da kwamitin da zai bibiyi lamuran ma’aikatan gwamnati. wannan kwamitin an samar da shi ne a ranar 27 ga watan Afrilun 2016.

“Wannan kwamitin an assasa shi ne ƙarƙashin jagorancin Sakataren Fadar Gwamnati, da taimakon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa. Daga cikin membobin kwamitin akwai Shugaban Biyan Albashi na Ƙasa, ma’aikatar ayyuka, ma’aikatar lafiya Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha, ofishin atoni janar na ƙasa. Wannan rahoton da suka samar, a yau mun duba shi.

“Rahoton ya bayyana cewa a ƙaddamar da dokar da ke cewa ba za a biya ma’aikatan da suka tafi yajin aiki ba. Shi wannan wani doka ne da yake rubuce a dokar sasanci tsakanin ‘yan ƙwadago.” Inji Ngige

Minista Ngige ya ƙara da cewa, da ganin yanayin yadda ake tafiya yajin aiki a yanzu, ana yi ne domin a kawo cikas ga gwamnatin Buhari.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI