Connect with us

LABARAI

Dokar Ta-ɓaci Kan Ilimi A Sakkwato: ‘Yan Bautar Ƙasa Na Taka Muhimmiyar Rawa

Published

on


Daga Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto

Kashi 95 cikin 100 na Jami’an Shirin Hidimar Bautar Ƙasa (NYSC) a Sakkwato suna aiki ne a sashen ilimi domin bayar da gudunmuwa ga shirin ɗaukin gaggawa kan ilimi da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ƙaddamar shekaru biyu da suka gabata.

Ko’odinetan shirin NYSC na Jihar Sakkwato, Musa Abubakar ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai yana mai cewar daga cikin matasa ‘Yan Bautar Ƙasa 2, 000 zuwa 2, 700 da ake turowa a Jihar Sakkwato a kowace shekara kashi 95 daga ciki suna aikin koyarwa ne a makarantu daban-daban da ke cikin Ƙananan Hukumomi 23 da ke a Jihar.

Ya ce mafi yawan jihohi jami’an bautar ƙasa ne ke riƙe da sha’anin koyarwa a makarantu.

“A jihohi da dama kashi 60, 70 zuwa 80 na malaman da ke koyarwa a makarantu matasa ne ‘Yan Hidimar Bautar Ƙasa. Babu wata jiha a Nijeriya wadda tsarin ilimin ta ya wadace ta ba tare da dogara ga Jami’an NYSC ba. Hasalima idan da a ce Hukumar NYSC ta janye jami’anta a tsayin watanni shida kacal da illar da hakan za ta yi ba ƙarama ba ce a faɗin ƙasa.” Inji shi.

Ya kuma bayyana cewar shirin NYSC shiri ne da aka kafa da zummar samar da haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’umma, don haka ba za a an cimma wannan manufar ba domin shirin abu ne na ɗorewa wanda ake yi a kodayaushe.

Ko’odinetan ya kuma bayyana cewar jami’ansu da ke aiki a fannin lafiya suna gudanar da aikin su yadda ya kamata mafi yawa a cikin ƙauyuka waɗanda galibi ‘yan asalin jiha ba za su iya zuwa su yi aiki a can ba.

A kan irin dangantakar da ke akwai tsakanin Hukumar NYSC da Gwamnatin Jihar Sakkwato kuwa, shugaban ya bayyana cewar dangantakar kyakkyawa ce.

“Muna da kyakkyawar dangantaka da Gwamnatin Jihar Sakkwato. Gwamnatin jiha ta na kula da jami’an NYSC yadda ya kamata, ta na ba su kuɗin alawus na wata-wata cikin lokaci. Hasalima Gwamnatin ta ƙara adadin kuɗin da take ba su da manufar ƙarfafa masu guiwa.”

Ya ce “A yanzu haka jihohi ƙalilan ne ke baiwa Jami’an Hidimar Bautar Ƙasa alawus a wata. Jihar Sakkwato ba wai ta na ba su kuɗaɗen ba ne kawai ba a’a, ta na biya cikin lokaci yadda ya kamata.”

Shugaban ya kuma bayyana cewar a ƙarƙashin jagorancinsa ya aiwatar da abubuwa da dama domin inganta jin daɗi da walwalar jami’an na NYSC.

“Yana da kyau jama’a su riƙa ɗaukar Jami’an Bautar Ƙasa a matsayin ‘ya’yan su, su riƙa kulawa da su yadda ya kamata a ƙoƙarin da suke yi na sauke nauyin da aka ɗora masu.” Ya bayyana.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI