Connect with us

LABARAI

Hatsarin Jirgin Ruwa A Kebbi: Sanata Na’allah Da Aliero Sun Yi Kira Ga Gwamnatin Tarayya

Published

on


Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi

 

A cikin makon da ya gabata ne Sanata Bala Ibn Na’Allah ya gabatar da wata takardar ƙudurin kan kira ga gwamnatin tarayya da kuma hukumomin da ke da alhakin tallafa wa al’ummomin da hatsarin jirgin ruwa ya laƙume rayukan su a cikin wannan wata da muke ciki a Jihar Kebbi.

Sanata Na’Allah, wanda ya  karanta wa majalisar dattawa takardar ƙudurin neman gwamnatin tarayya da kuma hukumomin da abin ya shafa domin tallafa wa al’ummomin da hatsarin jirgin ruwa ya laƙume rayukansu a cikin Jihar Kebbi.

Sanata Bala Ibn Na’Allah, wanda ke wakiltar yankin Kebbi ta kudu, ya ce, duk da cewa wasu  gwamnatotin  Arewacin ƙasar nan sun sadaukar da kai na bada tasu gudummawar sake ginin Kainji Dam domin samar da wutar lamtarki ga Nijeriya . Amma  ga al’ummomin na yankin sa na amfani da jiragen ruwa na katako domin sufurin jama’a ta ruwan kogin Neja  da ke da iyaka da yankunan da ya ke wakilta a majalisar dattawa.

Sanata Bala Ibn Na’Allah ya ci gaba da cewa yawan hatsarin jirgin ruwa da ake samu a jihar ta kebbi ya zama abin tashin hankalin  mutanen yankinsa a Jihar Kebbi, saboda haka  ya zama wajibi gareshi a matsayin wakilin yankunan da abin ya shafa ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ma hukumomin da abin ya shafa domin su shigo ciki domin kawo agaji da kuma gudunmuwar su kan ɗaukar matakin da ya dace domin kare  irin wannan matsalolin hatsarin jirgin ruwa da ake ta samu a yankin da yake wakilta a jihar ta kebbi.

Bugu da kari Sanata ya ci gaba da cewa wannan matsalar hatsarin jirgin ruwa da ake ta samu a yankin sa a duk shekara, amma har yanzu hukumomin da abin ya shafa babu wani mataki da aka ɗauka domin kariyar aukuwar wannan hatsarin jirgin ruwa da ake ta samu a duk shekara .

Wakilin na yankunan da abin ya zama wani tashin  hankali ga jama’ar garuruwan , ya nuna  damuwar sa kan yadda yawan rasa rayuka da ake ta samu a yankin nasa, ya ce  kuma ba a iya sanin  yawan  adadin mutanen da ke  rasa rayuwar su kan hatsarin jiragen ruwa a jihar ta kebbi , saboda babu wata takarda dake nuna mutun nawa ne jirgin ruwa yake ɗauke da su a cikin jigin na ruwa .

Shi ma tsohon Gwamnan jihar ta kebbi kuma a halin yanzu Sanata mai wakiltar mazaɓar kebbi ta tsakiya , Sanata Muhammad Adamu Aliero a lokacin da yake ba da tashi gudunmuwa ga takardar ƙudurin da Sanata Bala Ibn Na’Allah ya gabatar  ga majalisar dattawa , kan wasu yankunan a cikin jihar ta kebbi da suka fama da matsalar ambaliyar ruwa da kuma hatsarin jiragen ruwa saboda yunkurin sake gina  kainji Dam.

Har ila yau Sanata Adamu Aliero ya ci gabata da cewa wannan takardar korafi da Na’Allah ya gabatar a gaban majalisar dattawa ta zo daidai da lokacin da ya kamata saboda irin matsalolin hatsarin jiragen ruwa da ake yawan samu a jihar ta kebbi . Domin jihar kebbi ta yi hasarar rayuka masu yawan gaske da ba asan adadin su ba kamar yadda da Santa Na’Allah ya bayyana tun  farko cewa babu wata takardar mai nuna  cewa ga mutanen nawa  ne jirgin ruw yake ɗauke da su.

Hakazalika ya yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya, jahohin da kuma hukumomin da abin ya shafa da su shigo ciki ga gyaran wannan matsalar ambaliyar ruwa da kuma yawan hatsarin jiragen ruwa da ake yawan samu a jihar ta kebbi domin kare rayuwar mutun ne jihar su ta kebbi ga sake aukuwar wannan lamarin.

A halin yanzu, Sanata Na’Allah,  ya ce “ ya tuntubi mataimakin shugaban ƙasa farfesa  Yemi Osinbajo domin  yin ƙoƙarinsa na magance matsalolin  hatsarin jirgin ruwan da ake yawan samu  a cikin  kogin Neja da ke da iyaka da wasu garuruwan na yankin Kebbi ta kudu, inda yake wakiltar a  majalisar dattawa”.

“Na sadu da Mataimakin Shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, don Neman  biyan bukatun gwamnatin tarayya, a cikin makon  da ya gabata , kan wa annan matsalolin  da suka faru. Ina tsammanin cewa taimako zai zo daga gwamnatin tarayya nan da nan, “inji shi.

Sanatotin biyu sun yi amfami da wannan dama domin mika gaisu war su ta ta’aziyar mutanen da suka rasa rayuwar su kan hatsarin jiragen ruwa da kuma ambaliyar ruwan sama da ake fama da shi a jihar ta kebbi ga  gwamnan Jihar Kebbi da Sarkin Yauri da dukkan iyalan marigayan, wadanda suka rasa ‘yan uwan su.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI