Connect with us

RA'AYINMU

Rashawa: Rawar Da Lauyoyi Za Su Iya Takawa

Published

on


Jim kaɗan da karɓar ragamar mulkin ƙasar nan, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi wani kira mai cike da hikima da jan hankali ga lauyoyin ƙasarsa, inda ya buƙace su da kada su yarda su haɗa kai da gurɓatattun mutane su riƙa kare su a kotuna duk lokaci da a ka gurfanar da su a gaban kuliya, ya na mai ƙarawa da maimakon haka, kamata ya yi su ɗora masu kawo mu su ayyukan kare su a gaban kotuna bisa wata almundahana da su ka tafka kan tafarkin nadama da kuma wanke kansu daga zunubin da su ka ɗauka na jama’ar ƙasa ta hanyar sace dukiyar amana da a ka ba su. Buhari ya yi wannan kira ne a lokacin gudanar da taron ƙungiyar lauyoyi ta Nijeriya (NBA) a shekarar da ta gabata.

Haƙiƙa wannan kira da jan hankali ba ƙaramin hangen nesa ne a cikinsa ba duba da yadda lauyoyi ke hana ruwa gudu a kotuna wajen haifar da tafiyar wahainiya da kawo cikas a yayin gudanar da shari’u na cin hanci da rashawa; lamarin ya yi matuƙar taimakawa wajen kasa hukunta waɗanda su ka cancanci a hukunta a kotuna, saboda ruwan kuɗin da su ke yiwa lauyoyinsu su na kare su ta fuskar jinkirta shari’a.

Buhari ya yi matuƙar yin hange a nan, domin yawancin shari’ar da za a gudanar lauyoyi su na iya fahimta ko gane ƙarshenta tun ma kafin a je ko ina. To, idan su ka fahimci cewa wanda su ke karewa ba shi da gaskiyar da zai iya kare kansa, sai su tsiri shigo da tarnaƙi da gabatar da roƙe-roƙe a gaban alƙali don jinkirta shari’ar. A irin hakan sai ka ga an shafe shekaru masu ɗimbin yawa ba tare da an iya hukunta wanda a ke tuhuma ɗin ba, domin a ƙa’ida kowane mutum a ke tuhuma ya cancanci a ba shi cikakkiyar damar kare kansa. To, sai su yi amfani da irin wannan saɗara su ɗaurewa marasa gaskiya gindi har a ɗauki lokacin da shari’ar za ta shiririce.

Idan har lauyoyi su na kishin ƙasar nan kuma su na son su ga cewa, sun bayar da gudunmawarsu wajen ganin an ceto Nijeriya daga masifar da ta tsinci kanta na cin hanci da rashawa, to su ma sai sun bayar da tasu gudunmawar ta fuska yiwa marasa gaskiya ƙememe! Ashe kenan ba talaka kaɗai a ke buƙata ya bayar da tasa gudunmawar a ranar zaɓe ba, ba ɗan sanda kawai a ke buƙata ya bayar da tasa gudunmawar a yaƙi da cin hanci ba, ba kuma alƙalai kaɗai a ke buƙatar su bayar da tasu gudunmawar ba, a’a, hatta lauyoyi su na da irin tasu gudunmawar mai muhimmancin gaske.

A wannan lokacin, Shugaba Buhari ya ce, “na yi imanin cewa doka, da ’yan majalisa, da lauyoyi, da kotuna da hukumomin tabbatar da doka dukkanninsu su na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen ganin canjin da a ke so ya tabbata ya zamo gaskiya.”

Haƙiƙa mu na goyon bayan wannan kira, kuma mu na fata zai shiga kunnuwan waɗanda lamarin ya shafa, idan har su na so tarihi ya tuna da su a matsayin waɗanda su ka dafa a ka taimaka wajen dawo da Nijeriya kan tafarki mai kyau!

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI