Connect with us

MANYAN LABARAI

Sheikh Ɗahiru Bauchi Ya Musuluntar Da Aljani

Published

on


Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

A kwanakin baya ne dai shahararren malamin ɗarikar nan, Shaikh Ɗahiru Usman Bauchi ya musuluntar da wani aljani mai suna Chineke wanda aka canza masa suna zuwa Muhammadu Mustapha.

Musuluntar na aljanin ya biyo bayan shiga jikin wani matashi mai suna Babangida da ke da zama a unguwar ƙofar Wambai a cikin garin na Bauchi a kwanakin baya.

Da ya ke musuluntar da aljani Chineke, Shaikh Dahiru ya umurce sa da ya maimaita duk wata kalmar da ya ji ya bayyana ta, inda ya bashi kalmar shahada daga farko har ƙarshe a yayin da aljanin ke amsawa gami da maimaita wa.

Bayan da ya kammala bashi kalmar shahada, wato shiga cikin musuluncin, Shaikh Ɗahiru Bauchi ya tambayi aljanin shin ya taɓa shiga addinin kirista ko yaya? Inda aljanin ya amsa da cewa “Ni kirista ne, a ciki ‘yan uwana suke”.

Sai Shaikh Ɗahiru ya sake umurtarsa da ya ce yi imani da Annabi Isa, Annabin Allah ne inda aljanin ya maimaita kuma ya ce ya amince da hakan. Daga bisa sai Shaikh Dahiru ya fassara masa kalmomin da ya bayyana su da harshen larabci “A cikin wannan larabci ka ce ka tabbata tun daga zuciyarka har zuwa bakinka ka yarda cewa Allah shi kaɗai ne Ubangijin da ya halicci sama da ƙasa, ya kuma halicci komai da kowa”.

Shaikh Bauchi ya ci gaba da cewa “Ka ce ka kuma yarda Annabi Muhammadu bawan Allah ne kuma Manzon Allah, Allah ya aikosa da wannan addinin na Islam”. Ya bayyana wa aljanin

Daga nan ne kuma sai ya tambashi aljanin shin mene ne sunansa a da sai aljanin ya amsa da cewa sunansa Cineke. Nan take Shaikh Dahirun ya tambayeshi wacce suna ya ke so a cikin sunayen musulmai? Sai aljanin ya ce duk wanda ka bashi yana so kuma ya aminta da shi, daga nan ne kuma Shaikh Dahirun ya ce daga yau ka ce sunanka Muhammadul Mustapha, aljanin ya amsa ya kuma yi godiya.

Hakazalika, Shaikh Dahiru Bauchi ya yi masa addu’ar Allah tabbatar da shi a bisa wannan addinin na musuluncin ya kuma tabbatar da musulman a cikin addinin musulunci “Daga yanzu za ka je ka yi wanka, bayan kai ma aljanun da suka shiga ɗarikar tijjaniyya sun fi dubu biyar waɗanda muke tare da su”. in ji Shehin

Da  ya ke amsa wa manema labaru bayan baiwa aljanin musulunci: aljanu suna iya kallon mutane, amma mutane basu iya kallon aljanu ta yaya ne za a iya tabbatar da ya amshi musuluncin nan? Sai Shaikh Dahiru ya amsa da cewa “tun dam un yarda da Alkur’ani, duk abun da Alkur’ani ya faɗa gaskiya ne akwai mala’iku bamu ganinsu kuma mun yi imani da su, suna tare da mu suna ɗaukan maganganunmu suna rubutawa, kuma mun yi imani da hakan, suna kuma ɗakan aiyukanmu suna rubutawa, duk da mu bamu ganinsu amam mun yi imani da hakan. Haka su ma aljanu akwai su alkur’ani ma ya bayyana mana, saboda haka yarda da maka’iku dole ne”. a cewar Shaikh Dahiru

Shi dai wannan aljani mai suna Cineke wanda ya canza suna zuwa Muhammadu Mustapha ya yi magana kowa na jinsa cikin murya ƙasa-ƙasa.

 

 

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI