Connect with us

LABARAI

Shugaban Kwalejin Sharar Fage Ta Kano Ya Kama Aiki

Published

on


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Sabon shugaban Kwalejin share fagen shiga jami’a ta Kano. Dakta Sunusi Yakubu ya sha alwashin zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ci gaba da haɓakar Ilimi mai nagarta a makarantar.

Dakta Sunusi Wanda tsohon dalibi ne na makarantar kuma malami da yayi koyarwar sama da shekaru 10 a Kwalejin kafin ya koma ƙarin karatu a jami’a. Ya ce, a matsayinsa na wanda yake bada gudummawa na ci gaban ilimi ba’a Kano kaɗai ba, wanda aka dauko shi yanzu daga jami,ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil,yaga ya dace ya dawo kwalejin share fagen shiga jami,a ta Kano,dan ci gaba da bada gudummuwar haɓɓaka ilimi.

Sabon Shugaban kwalejin yayi nuni da cewa wannan kalubalene gareshi da akace yazo ya raya wannan kwalejin da tsofaffin malamansa suka rike,amma da yardar Allah zai dora daga inda suka tsaya.

Dakta Sunusi Yakubu yace zasuyi ƙoƙari na ɗaukar matakai daban-daban na ilimi da suke ganin za su ƙara faɗaɗa ci gaban ilimi a wannan makaranta.

“Zamu tabbatar da ingancin Ilimi da ake koyar wa. Dama malamai da ɗaliban wannan makarantar jajirtattu ne wajen tabbatar da samun shaidar karatu mai inganci, za mu ci gaba da inganta ilimi, don wannan makaranta ta ɗore akan haka wajen bada ingantaccen ilimi da samun shaidar jarabawa mai inganci” Inji Dakta Sunusi.

Ya ce, za su faɗaɗa wannan makaranta ta wuce yadda take tare da bai wa ma’aikata da malamai dukkan haƙƙinsu, amma wannan yanada alaka ne da abin da ake dashi a ƙasa. Daidai abin da ake dashi za’a share musu hawaye dashi daidai gwargwado, domin saida hakki isasshe sannan kowa zai sami cikakkiyar dama ya gudanar da aikinsa.

Dakta Sunusi Yakubu, ya yi kira ga ma’aikatan Kwalejin na kowane mataki su bashi cikakkiyar haɗin kai da zai kai ga samun nasarar ci gaba da bunƙasar makarantar.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI