Connect with us

LABARAI

’Yan Jarida 300 Asibitin ATBUTH Ya Yi Wa Aikin Ido

Published

on


Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Sashin kula da lafiyar Ido ‘Ophthalmology’ na asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi  ya ƙaddamar da wani aikin duba lafiyar ido kyauta a Jihar Bauchi, inda suka ƙaddamar da aikin a jiya laraba a sakatariyar ‘yan jarida da take Bauchi.

A bisa haka ne ma suka fara yi wa ‘yan jarida sama da 300 aikin na duba lafiyar idanuwansu. sun duba lafiyar idanun ‘yan jaridar gami da bai wa waɗanda suke da lalura magunguna domin kare su daga samun matsalar idanu.

Shugaban ‘Nursing’ a sashin kula da lafiyar idanu na asibitin, Nuhu Malam Nuhu ya bayyana wa wakilinmu dalilinsu na yin wannan aikin, ya ce akwai ranar kallo ta duniya wanda ake yinsa a dukkanin duniya, ya bayyana cewar ita ranar gani “A bisa haka ne muka haɗa hanu da ƙungiyar ‘yan jaridu, sai muka ga ya dace mu fara duba lafiyar idanunsu mu ga idan da masu matsala sai mu duba abun da ya kamata mutum ya yi domin ya kiyaye idonsa”.

Ya ce babbar hikimarsu na yin hakan dai shi ne domin haɗa kai da ‘yan jaridan wajen yaɗa wannan lamarin domin jama’a su tashi tsaye domin neman lafiyar idanunsu, ya ce idan mutane suka je asibiti domin duba ladiyar idanunsu hakan zai taimaka wajen ƙara musu kuzarin kallo.

Da ya ke bayyana irin abubuwan da suka yi aiki da su wajen duba lafiyar idon ‘yan jaridan ya ce sun yi amfani da kwararrun ma’aikatan ido, da kuma ingattatun kayyakin aiki domin gano matsalar ido don shawo kanta “mun zo da abubuwa da yawa, amma babbar abun da muka zo da ita shine shawarwari, domin wani abun ma ba magani ya ke da buƙata ba, idan ka zo muka yi maka bayani muka baka shawarori hakan zai taimaka maka. Na biyu kuma mun zo da wasu maguguna da za mu ce zamu baiwa kowa ba; amma dai mun duba yanayin idon mutum sai mu ga mene ne ya kamata mu ba shi. Sannan mun zo da tabarau na duba karatu ba na yawo da shi haka ba, mun lura ‘yan jarida aiyukansu sun shafi rubutu da karance-karance da sauransu sai muka ga ya dace mu raba ma wasu musamman waɗanda shekarunsu ya ɗan ja domin su kula da lafiyar idanunsu, da kuma magunguna da suka shafi ƙaiƙayin ido da sauransu”. In ji Jami’in

“Mun samu wasu da idanunsu ke buƙatar agajin gaggauwa, mun rubuta musu cewar su je su nemi babban likita domin dubiya na gaba”.

Da ya ke zantawa da mu, Kwamared Ibrahim Muhammad Malam Goje shugaban ‘yan jarida na jihar Bauchi ya nuna farin cikinsa a bisa yanda aka yi wa mambobinsa aikin duba lafiyar idon a wannan ranar “Gaskiya wannan haɗaka ya zo a lokacin da ya dace, kamar yanda ka sani aikin jarida a wannan lokacin yana tafiya ne da mu’amala da na’ura mai kwakwalwa da kuma farin takarda a don haka muna fuskantar matsalar ido sosai. Mun jima muna wannan tunanin, sai aka zo maganar wannan rana ta kula da lafiyar ido na duniya sai muka ga dacewar mu yi mu’amala da wannan sashin kula da lafiyar ido, wannan dalilin ne ya sa muka gayyato wannan sashin domin kula da mambobinmu”. In ji NUJ

Da ya ke bayyana matsalolin da suka fuskanta ya ce “kasantuwar mun yaɗa sanarwa a gidajen rediyo hakan ya sanya wasu da dama suka yi ta bulbulowa sun ɗauka kowa da kowa ne, idan ka duba wani dole ne kawai ka sauraresa. Wannan kawai shi ne matsalar da muka samu, amma mambobinmu sun bada haɗin kai sosai, wajen zuwa akan lokaci da kuma bin dokokin masu aikin”. A cewarsa

Daga bisani kuma ya kirayi mambobin nasa kan tabbatar da kula da lafiyar idanunsu a kowani lokaci “za mu ci gaba da neman kwararru a sashin ido domin suke ci gaba da duba lafiyar idon mambobinmu lokaci bayan lokaci. Ina kuma kira ga ‘yan jarida da suke kula da lafiyar idanunsu”. In ji sa

Kabiru Garba, muƙaddashin sakataren NUJ reshen Bauchi kuma ɗaya daga cikin wanda suka ci moriyar shirin ya bayyana cewa “an fara wannan aikin da mataikamin shugaban ‘yan jarida sai ni na biyu baya, ni da aka zo kaina ban samu wata matsala ba; daman ina da matsalar ido, bayan da suka dubani sai suka ce ya kamata su bani gilashi domin amfanin yau da gobe”. A cewar Kabir

Da yake kuma bayyana yanayin aikin ya ce “An raba gilashi wa ‘yan jarida sama da 100, an kuma bada maguguna wa mutu kusan 100, an kuma maida wasu zuwa asibiti domin a yi musu aiki kusan 100. A takaice an duba ‘yan jarida 300 a yau, aikin ya gudana cikin kwanciyar hankali” inji shi

Tun da fari a lokacin ƙaddamar da shirin, Jami’ar da ta jagoranci wannan aikin Dr. Hafsat Isa ta bayyana muhimmacin da ke cikin kula da lafiyar ido da kuma muhimmancin da aikin zai yi wa manema labaru “mun duba cewar su ‘yan jarida kullum suna ta’ammuli da na’urar kwamfuta da sauransu sai muka ga ya dace mu ƙaddamar da wannan aikin da fara dubasu”. A cewarta

Shi dai ranar gani ta duniya wacce ake yinsa a dukkanin ranar 12 ga watan Oktoban kowace shekara, taken bikin na bana dais hi ne ‘Ka yi abun da za ka yi kallo ya yi tasiri’. A bisa haka ne sashin kula da lafiyar ido na asibitin suka fara gudanar da shagulgulan wannan rana tun a jiya 11 ga watan, domin faɗakarwa gami da duba lafiyar jama’a kyauta.

Daga cikin abubuwan da ‘yan jaridan suka ribanta har da gilasa, da kuma magunguna a yayin da wasu kuma aka turasu zuwa asibiti domin ganin babban likita.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI