Connect with us

RAHOTANNI

Ƙyautar Mota Ta Tarwatsa Jam’iyyar APC A Taraba

Published

on

Daga Aliyu Idris daudawa

Akwai alamun da ke nuna cewar wata matsala ta taso a reshen jam’iyyar APC Ta jihar Taraba, saboda kuwa wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar, waɗanda suke nuna goyon bayansu ga Ministar Harkokin Mata, Aisha Alhassan, sun buƙaci tsohon shugaban jam’iyyar na jihar, Hassan Arɗo da ya dawo da motar da tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya bashi kyauta.

Bincike ya nuna shi Arɗo, wanda shi babban mai goyon bayan Hajiya Aisha ne, yanzu ya samu matsala ne da ita Ministar Harkokin Matan, sai hakan ya sa suka kafa wata ƙungiya wadda suka sa ma suna ‘Integrity Group’, wannan ƙungiya dai kwanan ne suka nisanta kansu da kalaman da Ministar ta yi, wanda hakan ya sa jam’iyyar a jihar a na yi mata wani gani-gani. Amma har ila yau waɗansu da har yanzu suna ba Ministar goyon baya, sun kafa kwamiti wanda zai kawo ƙarshen rikita-rikitar, a dalilin bada kyautar motar.

Arɗo wanda ba da daɗewa bane aka bashi muƙamin  Jakada, zuwa ƙasar Trinidad da Tobago. A tattaunawarsa da majiyarmu, ya ce;  “an aiko mani da wasiƙa inda aka buƙace ni da cewar tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar yana son in maido da motar  da ya bani kyauta.

Takarda ta farko daga ofishin APC na Taraba ta ke , an kuma rubuta ta a ranar 9 Satumbar 2017, Mista Solomon Jadana ne ya sa hannu a takardar. Shi ne shugaban shiyya, amma sai aka ce wai Sakataren jam’iyya ne.” in ji shi

Sauran mambobin kwamitin kamar yadda shi Arɗon ya bayyana, sun haɗa da Haladu Yakubu wani lauya, Sani Mamman Posa, Aliyu Umar Bali, da kuma Godin Ɓillana.

Takarda ta biyu kamar yadda a cewarsa; “An ce ta fito ne daga Atiku Abubakar, Abdullahi Nyako ne ya sa hannu a kanta, an kawo mani ita, na lura an rubuta ta ne a ranar 27 ga Satumbar 2017’’.

Ya ƙara jaddada cewar “Ni na san kawai domin ina goyon bayan Buhari, shi yasa duk suke mani haka. Wannan ne ma dalilinmu na kafa ƙungiyar Integrity group’’.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakin sa, Abdullahi Ade wanda shi ne shugaban matasa na jam’iyyar, ya ce, su kawai suna buƙatar ya dawo da motar ne, saboda ba shi aka ba, ta jam’iyya ce.

Ɗaya daga cikin jiga-jigan ‘Integrity Group’, Iliyasu Mu’azu ya bayyana cewa ɓangaren Ministar Matan na son kawo saɓani da ɓata jam’iyyar ne a jihar, saboda kuwa ɓangaren sun yi niyyar barin APC.

Ya ce, “mu muna goyon bayan Buhari, ita kuma tana nuna sai mai gidanta na siyasa Atiku, ƙiri ƙiri muka faɗa mata mu bamu yin Atiku, ko da Atiku ya amshi motarshi wannan ina shakkun haka, mu ‘yan ƙungiyar integrity, a shirye muke mu sawo ma Ambasada Arɗo wata mota’’.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!