Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Lateef Aremu: Ƙasurgumin Dilan Sassan Jikin Ɗan Adam

Published

on

Daga Mustapha Hamid

Da alama ruwa ya fara ƙarewa ɗan Kada ga matsafan da ake zargi da saye da sayar da sassan jikin ɗan Adam a Jihar Ogun, inda ba a yin cikakken mako ba tare da jami’an tsaro sun yi nasarar cafke wani daga cikin su ba.

A yunƙurin da hukumar ‘yan sanda ke yi na kawo ƙarshen su, yanzu haka sun yi nasarar cafke mutum bakwai daga cikin su.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, Ahmad Iliyasu,yayi kira ga al’ummar Jihar da cewa su kwantar da hankulan su, domin kuwa, jami’an ‘yan sandan da ke jihar, ba za su taɓa nuna gajiyawa ba a yaƙin da suke yi da waɗannan miyagun Mutane.

Iliyasau yana magana ne jim kaɗan bayan kama wasu Mutane 7, ‘ya’yan wasu ƙungiyoyin matsafa 3 da suka shiga hannun jami’an tsaro na musamman na tarayya masu yaƙi da ‘yan fashi da Makami ‘SARS’.

Ƙungiya ta farko tana ƙunshe ne da Mutum 2 da suka haɗa da Lateef Aremu ɗan shekaru 67, da kuma Kola Sidipo ɗan shekaru 32 waɗanda suka ƙware wajen yin kasuwancin sassan jikin ‘yan Adam.

Kamar dai yadda kwamishinan ‘yan sandan ya shaida mana, jami’an tsaron na SARS sun yi nasarar cafke Aremu da Sodipo ne bayan rahotannin da suka samu a kan ƙungiyar matsafan da suka gwanance wurin yin amfani da sassan jikin Bil’adama domin yin tsafi.

“Jami’an tsaron SARS sun samu rahoto a kan matsafa waɗanda suka ƙware wurin yin tsafi da sassan jikin bil’adama, bayan samun rahoton ne, sai muka tura wata runduna ta musamman domin bin diddigin su, sai Allah Ya ba mu sa’a, inda muka yi nasarar cafke ‘yan ƙungiyar su 2 a unguwar Owode-Egba da ke Jihar.

“Kolawole Sodipo da Lateef Aremu sun shiga hannun mu, inda muka kama su da Ƙoƙunan kawukan Mutane, da Ƙasusuwan sassan jikin Bil’adama, da Bututun zuba harsasan Bindiga guda 6 mai ƙunshe da harsasai masu rai a cikin su”.

Yayin da yake zantawa da majiyar mu, Aremu ya amsa cewa yana amfani da sassan jikin Bil’adama wurin haɗawa waɗanda suke buƙata ƙulumboto, inda ya ƙara da cewa, wannan mammunar sana’ar tasa ta sama masa da maƙudan Kuɗaɗen da ya iya ya sayi Motoci har guda 15, da Gidaje guda 4.

Aremu, wanda ya bayyana mana cewa shi manomi ne kuma mai sana’ar bada Magungunan gargajiya, amma bai musa cewa yana amfani da sassan jikin bil’adama wurin haɗawa Mutane ƙulumboton tsafi ba.

Ya furta cewa, Ƙoƙon kan Mutum da jami’an tsaro suka kama shi da shi, abokin ta’asar sa ne ya kawo masa,don ya haɗa musu ƙulumboton yin Kuɗi.

“Ni manomi ne, kuma mai bayar da Magungunan gargajiya, mun fara haƙa ramin iza harsashin ginin Gidana ne a Itoko, sai muka ci karo da waɗannan Ƙasusuwan, sai muka tattara su, muka ɗura su a cikin wata Jakka, iya haƙiƙanin abinda na sani kenan, bayan da muka zo za mu haɗa ƙulumboton yin Kuɗin ne, sai shi ya kawo mana Ƙoƙon kan na Mutum”.

“Yadda mu kan yi shine, daddaka Ƙoƙon kan, domin haɗawa da da sauran nahaɗai da suka haɗa da, farar Tantabara, da kuma Sabukun Salo, na kai shekaru 20 ina wannan sana’ar, ba kowane lokaci bane nake amfani da sassan jikin na ɗan Adam, na kan yi ne kawai daga lokaci zuwa lokaci, na mallaki Motoci 15,da Gidaje guda 4 duk a cikin wannan sana’ar wacce na fara yi tun shekarar 1980”.

Sodipo, ɗan shekaru 32,shi ma ya bada labarin irin rawar da yake takawa a ƙungiyar tasu, inda ya furta cewa, “na san Baba (Aremu) ne a matsayin mai bada Maganin gargajiya, saboda ya kan je wurin maigidana, ni ma na samu horin bada maganun gargajiya.

“Wani Mutum ya zo wuri na, ya ce yana so a haɗa masa ƙulumboton yin Kuɗi, sai na tura shi wurin Baba, inda su ka yi yarjejeniya, ya biya shi Kuɗi Naira 75,000, amma sai ƙulumboton da ya haɗa masan bai yi aiki ba, sai Mutumin ya kira ni, yake koka mini, inda na bashi shawarar kawai ya je ya amshi kuɗinsa, shi kuma sai ya nuna mini ba buƙatar sa kenan ba, su yake a sake haɗa masa wani ƙulumboton”.

“Ban san komai dangane da Ƙoƙon kan Bil’adaman ba, ni ban kai masa wani Ƙoƙoƙn kan kowa ba, ni dai na san na ƙwarance wurin bada jalabi ga ƙananan ‘yan Kasuwa, domin samun buɗi a harkokin Kasuwancin su”.

Dangane da hadahadar sassan jikin Bil’adama na Naira 12,000 kuma, Kwamishinan ‘yan sandan ya ce, yayin da suka kai mamaya a kan ƙungiya ta 2 ta matsafan a yankin Totoro a Abeokuta babban birnin Jihar, sun yi nasarar cafke Adebayo Mudassir, da Rashid Abbas, inda suka same su da busassu, da kuma ɗanyun sassan jikin ‘yan Adam da suka haɗa da ƙoƙon kai, Fata, Haƙora, da kuma Ƙadangaru guda 4.

Iliyasu ya shaida mana cewa, an ga Mudassir da Abbas ne ɗauke da wata Jakka cikin yanayi na zargi, yayin da aka tsare su dan bincikar su, sai aka same su ɗauke da Ƙadangaru, da wasu abubuwa haɗaɗɗu na tsafi, inda ya ƙara da cewa, ana zargin Mutanen 2 da aikata laifin kisan kai.

“Sun gwanance wurin kashe Mutane dan aiwatar da tsaface-tsafacen su, jami’an tsarin mu na SARS sun ga wasu Mutum 2 a kan Babur ɗauke da wata Jakka cikin yanayin zargi, inda jami’an tsarin namu suka tilasta musu tsayawa dan bincikan su”.

“Daga cikin abubuwan da aka samu a cikin Jakkar na su sun haɗa da, ɗanyu da busassun sassan jikin bil’adama, yayin da suke amsa tanbayoyin jami’an tsarin namu, sai aka fara zargin cewa maksa Mutane ne, kuma suna da cibiyar su a Totoro da ke Abeokuta.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da Adebayo Mudassiru, Rashid Abbas, abubuwan da aka kama su da su sun haɗa da busassu da ɗanyun sassan jikin bil’adama, Ƙoƙon kan Mutum, Ƙadangaru, da wasu abubuwan ƙulumboton su na tsafi”.

A zantawar sa da wakilin mu, Mudassiru ɗan shekaru 36, wanda ya furta cewa shi mai yin wa’azi ne, ya furta cewa wani tsohon Malamin su ne ya sayar musu da sassan jikin Ɗan Adam ɗin, ya ce, sun sayi fatar mutum ɗin ne, da ƙoƙon Kan da Haƙora guda 12 a kan kuɗi Naira 12,000 kacal.

“Muna kan hanyar mu ne na zuwa Itoku don sayan wasu kayan haɗin, ba a Itoku muka sayi Fatar jikin Bil’adaman ba, mun karɓo shi ne daga wurin wani a Ijemu”.

“Mun san me mu ke ɗauke da shi a cikin Jakkar, Sassan jikin bil’adaman ana yin amfani da su ne wurin yin tsatsuban yin Kuɗi, tabbas mun so mu yi amfani da su ne dan ƙashin kan mu domin jawo hankulan al’umma ya dawo gare mu, mun kai shekaru 5 muna wannan sana’a”.

“Mun sayi sassan jikin ne daga wurin wani mai yin wa’azi, Haƙoran ba su da tsada, ban san yawan adadin su ba, amma a Naira 2000 kacal aka sayar mana da su, mun sayi dukkan sassan jikin Ɗan Adam ɗin ne da suka haɗa da Ƙoƙon Kai, da Fata a kan kuɗi Naira 12,000 kacal”.

“Mun halarci Makaranta a unguwar Ijaye da ke Abeokuta, mun daɗe muna yin wannan abin, abinda mu ke yi shine, muna ƙona sassan jikin Bil’adaman ne, inda muke amfani da Tokar, mu haɗa da Sabulun Salo, da Ruwan Dodon Koɗi, dan mu yi wanka, ba mu kai ga aiwatar da hakan ba dai a aikace, amma dai haka aka koya mana da mu yi, an koya mana cewa mu riƙa haɗa Ƙadangare, sassan jikin Ɗan Adam, Ruwan Dodon Koɗi, da sauran mahaɗai, ba mu san kai tsaye ko ta yaya ƙulumboton ke yin aiki ba, amma illa iyaka abinda aka koya mana kenan”.

A nasa zancen, Abbas ɗan shekaru 33, ya furta cewa, “Mutumin da ya bamu mahaɗan, shi ne dai ya ba mu sassan jikin bil’adaman, shine kuma ya koya mana yadda za mu yi amfani da su don yin siddabarun samun Kuɗin, a kan hanyar mu bayan mun karɓo ne, muka faɗa Komar jami’an tsaro”.

Hukumar ta ‘yan sanda ta furta cewa, ta kama mutum na 3 ɗan ƙungiyar ne da ake zargi mai suna Razaƙ Adenekan mai shekaru 42 jim kaɗan bayan damƙe ‘ya’yan ƙungiyar su 2.

Su ma ‘ya’yan ƙungiya ta 3 ita ma mai ƙunshe da Mutum 2 waɗanda Ma’aikatan wata Maƙabarta ne, waɗanda suka haɗa da Jimoh Olanrewaju, da Baba Tunde Seun waɗanda dukkanin su suna cikin masu gadin Maƙabartar, sun amsa laifin sayar da Kawukan Mutane kowanne a kan kuɗi Naira 10,000, Kwamishinan na ‘yan sanda ya ce, an kama su ne a Maƙabartar Oke-yidi da ke Lantoro,  a Abeokuta yayin da suke tsaka da haƙe wani Ƙabari.

Shi ma a nasa bayanin, Olanrewaju,  wanda ake zargi da kasancewa shugaban ƙungiyar tasu, ya amsa cewa, sun sayar da Kawukan Bil’adama guda 4 ne kowanne  a kan kuɗi Naira 10,000.

“Ba ma buɗe Makarar kowa don ciro Gawa, abinda mu ke yi shine, muna haƙe Ƙaburburan da aka riga aka bizne ne mu ciro su.

Ƙaburburan da ba a sa musu daɓen Siminti ko wata alama ba su mu ke haƙewa, Ƙaburburan suna da wuyar ganewa, amma yayin da mu ke haƙawa, mu kan gane wurin da mu ke yin haƙan, ƙabari ne ko ba ƙabari ba.

“Na taɓa sayar da kan Mutum ga wani Alhaji mai wa’azin addinin Musulunci, shi ma yanzu ya riga mu Gidan gaskiya, an fi sanin sa da suna Alfa, mazaunin Tinubu Street ne da ke ƙaramar hukumar Abeokuta ta Arewa, bai sanar da ni ko amfanin me zai yi da Kan bil’adaman da na sayar masa ba.

“Ina nadamar abubuwan assha da na aikata a baya, jahilci ne ya sa na aikata, dukkanin abubuwan assha da muka aikata a baya mun san jahilci ne tsagwaron sa ya kai mu ga aikatawa”.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: