Connect with us

RAHOTANNI

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Kaɗa Ƙuri’ar Amince Wa Shugabancin Buhari A Adamawa

Published

on

Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

Wani taron masu ruwa da tsaki a Jihar Adamawa sun kaɗa ƙuri’ar amincewa shugaba Muhammadu Buhari, ya ci gaba da mulkin Nijeriya a karo na biyu.

Da yake bayyana sakamakon taron masu ruwa da tsakin shugaban kwamitin bayyana sakamakon taron Sanata Silas Jonathan Zungina, ya ce taron ya amince da sakamakon taron ne bisa abin da ya gani na irin shugabancin shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce,  sun gamasu da mataka da gwamnatin tarayya ke ɗauka wajan yaƙi da cin hanci da rashawa, da samar da tsaro da kuma hanyoyin da takebi wajan haɓaka tattalin arziƙin ƙasar, ya ce wannan yasa suka amince da shugabancin shugaban.

“wannan taron ya amince shugaba Muhammadu Buhari ya ci gaba da shugabanni a karo na biyu, bisa  yaƙi da cin hanci da rashawa, samar da tsaro musamman a rewa maso gabas da hanyoyin da shugaba Buhari ke bi wajan farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa”.

Ya ce,  batun samar da wutar lantarkin da gwamnatin tarayyar ke ƙoƙarin samarwa a garin Mambila ta ƙaramar hukumar Sardauna a jihar Taraba, abun a yaba da baiwa shugaban goyon baya ne domin cimma nasaran shirin.

Haka kuma taron masu ruwa da tsakin ya kuma kaɗa ƙuri’ar amince wa da shugabancin gwamnan jihar Umaru Bindow Jibrilla, da kuma jagorancin APC a jihar, da cewa sun cancanci yabo da goyon bayan jama’ar jihar.

Sukace “gwamnan yayi ƙoƙarin wajan gudanar da ayyukan ci gaban alumna, haka kuma shugabannin jam’iyyar sun takarawar ganin wajan samar da haɗinkai da ci gaban jam’iyyar” inji sanarwar bayan taron.

Tun da farko a jawabinsa shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Abdurrahman Abba Jimeta, ya ce,  Adamawa dama jiha  ce ta aPC jiha ce ta shugaban ƙasar, ya ce,  saboda haka suna tare da Buhari ɗari bisa ɗari.

Batun kaɗa ƙuri’ar wanda Sanata Salis Jonathan Zungina ya kawo, Sanata Binta Masi Garba ta goya mishi baya, Wanda ya kuma samu amincewar ɗaukacin masu ruwa da tsakin jihar dake ɗakin taron.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!