Connect with us

MANYAN LABARAI

Shugaba Buhari Ya Kori Abdulrasheed Maina

Published

on

Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin a kori tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga shirin fanshon kasar, AbdulRasheed Maina.

A cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya bayyana cewa, Shugaba Buhari ya ce a kori Abdulrasheed Maina daga aiki nan take, a kuma yi bincike game da yadda akayi ya koma aikin gwamnati.

Jim kadan, shugaban Buhari ya kuma umurci shugabar ma’aikatan gwamantin tarayyar Oyo-Ita Winifred Ekanem, ta mika rahoton binciken ga ofishin shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Abba Kyari, kafin a tashi daga aiki a yau Litinin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!