Connect with us

RAHOTANNI

Tsugune Bata Ƙare Ba A PDP: Kotu Ta Ja Kunnen Makarfi

Published

on

Daga Aliyu Idris Daudawa

Da alamu har yanzu tsugunne bata ƙare wa jam’iyyar PDP ba. Idan aka yi la’akari da umarnin da  wata  Babbar Kotun tarayya wadda ta yi zamanta a Ado- Ekiti ta bayar, inda ta buƙaci jam’iyyar da kada ta bar kwamitin da Cif Makanjuola ke shugabanta sashen Kudu maso Yamma, su halarci babban taron ƙasa, wanda jam’iyyar za ta yi ranar 9 ga Disamba na wannan shekara.

Bugu da ƙari, hukuncin Kotun bai tsaya a nan ba, domin kuwa ta hana ita jam’iyyar ,ko jami’anta, su bar  waɗanda Eddy Olafeso ke shugabanta, su halarci babban taron jam’iyyar, ko kuma su bada wasu sunaye a matsayin wakilai masu wakiltar sashen Kudu maso Yamma. Olafeso dai shi ne shugaban jam’iyyar PDP na sashen Kudu maso Yamma, wanda shugabancin jam’iyyar na ƙasa ya amince da su.

Ogundipe ya shaida wa manema labarai ranar Juma’a a Abuja cewar rashin bin umarnin Kotun ka iya shafar duk waɗansu abubuwa da aka tattauna a taron ƙasa na jam’iyyar PDP wanda za a gabatar ranar 9 ga Disamba.

Ya buƙaci shugaban jam’iyyar na riƙo, Sanata Ahmed Maƙarfi da ya bi umarnin kotu saboda shi ma ai irin wannan ta taɓa shafar shi.

Makanjuola dai ya kawo takarda mai ɗauke da hukuncin da Kotun ta yanke, zuwa Hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa, ranar Juma’a, yayin da shi kuma zaman kotun an yi shi ne ranar Laraba ta makon da ya gabata.  Sunayen waɗanda aka ambata  wajen shigar da ƙarar mai lamba/FHC/AD/CS/18/2017 sun haɗa da, Cif Makanjoula Ogundipe, Cif Adepegba Otemelu, Lanre Orimoloye, Supo Ijabadeniyi, da kuma Femi Carena. Sauran sun haɗa da Hukumar Zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta, Jam’iyyar PDP , Sanata Ahmed Maƙarfi, Ben Obi, Eddy Olafeso, Wunmi Jenyo, Adeola Ogunrinde, da kuma Femi Adetola.

Haka kuma a jerin sunayen akwai, Ojo Williams, Fasiu Bakenne, Philip Aiɓohji, Mrs Oluwaumi Oshinroluke, Biliaminu Ogundele, Femi Makinde, Shugaban Rundunar ‘Yan sanda ta ƙasa, mataimakin Shugaban Rundunar ‘Yan Sanda na shiyya ta biyu, Kwamishinan ‘Yan sanda na Osogbo, Kwamishinan ‘Yan sanda na Oyo, da kuma sashen Hukumar Binciken ƙwaƙaf ta ƙasa.

Haka nan Kotun wadda  mai shari’a Taiwo O. Taiwo ta gargaɗi Sanata Maƙarfi da tawagarshi da su hana ɓangaren da Makanjuola ke shugabanta halarta babban taron jam’iyyar na ƙasa. Bugu da ƙari Kotun ta bayyana waɗanda za su ci gajiyar hukuncin da ta yanke, waɗanda suka haɗa da Alhaji Adewole Adeyanju, da kuma Sanata Buruji Kashamu, bayan haka kuma kada ita jam’iyyar ta hana su halartar babban taro na ƙasa.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!