Connect with us

NAZARI

YAU DA GOBE: Tarihin Asalin Wasan Bare-Bari Da Fulani

Published

on

Daga Sadiƙ Tukir Gwarzo, RN,

08060869978

Tarihi ya nuna cewar bukasar shahararriyar maɗaukakiyar daular borno ta bare-bare ta soma yin kasa ne tun bayan rasuwar Sarkinsu Mai Idris Alooma a wuraren karni na goma sha shidda zuwa na sha bakwai. Don haka ya zamana daular ta rinka asarar manyan garuruwan da suke karkashinta sakamakon yadda karfin ikonta ke dusashewa.

Ana wannan yanayi, sai kuma fulani suka soma jihadi a shekarar 1804. Don haka bayan yake-yakensu yayi kamari, sai ya zamana suna tashi zuwa garuruwa domin cinsu da yaki, sai data kai har masarautar borno sun riska da yaki.

An ce a shekarar 1808 ne Fulani suka ɗwace cibiyar masarautar Bare-bari dake garin Ngazargamu, inda suka kone garin tare da korar mayakan bare-bari.

A shekarar 1814 kuma sai babban malami a daular borno mai suna shehu Muhammadul Amin Alkanemi ya jagoranci kafa sabuwar daular bare-bari a wani gari mai suna Kukawa. Sannan ya haɗa runduna gami da soma taimakon sarkinsu mai suna Mai Dunama Lefiagi.

Daga baya Bayan sarki Mai Dunama yaso halaka Muhammadul Amin Al-kanemi saboda hassadar farinjininsa a wurin jama’a amma bai samu nasara ba, sai Al-kanemin ya zamo sarkin borno mai cikakken iko ba rmtare da zubda jini ba, don haka ya shiga kalubalantar fulani da suka hanasu sakat ta hanyar yakarsu da kuma aikewa da wasikun ilimi yana tuhumar Shugaban fulani shehu Usmanu akan cewa don me zai shiga yaki da daular Borno alhali tafi shekaru ɗari takwas da karɓar musulunci kuma da sunan yakin musulunci?

To a haka dai akace aka rinka kwafsawa da yaki da kuma rubuce-rubuce na wasiku har zuwa rasuwar shehu Usmanu ɗan fodio, yayin da ɗansa Muhammadu Bello ya gaje shi a shekarar 1826 inda yaki ya kara tsamari a tsakaninsu.

To ance babu jimawa kuma bayan kowa yasha wuya a hannun ɗanuwansa, sai kuma aka yanke shawarar yin masalaha. Anan akayi sulhu, aka bar bare-bari da birninsu, amma dai sun rasa ikon wasu yankunan da abaya suke hannunsu izuwa hannun fulani.

Ance a inda wasan kabilun biyu ya shigo shine dirkakowar mayakin nan daga sudan zuwa yankin borno, watau Rabeh, wanda yazo ya kwace daular borno gaba ɗaya, tare da azabtar da bare-bari har tasa sarkin bare-bari ya gudu daga masarautarsa neman mafaka. Fulani ne akace suka rinka tunkarar Rabeh da yaki suna fafatawa, har izuwa lokacin da sojojin faranshi sukai masa tara-tara suka hallaka shi.

Don haka wuyar da bare-bari suka sha a hannun Rabeh, ya zamo rabinta basu sha-ba a yakinsu da fulani, don haka fulani suka rinka tsokanarsu idan an gansu ana cewa ‘ga Rabeh nan’, sukuma sai kaga sun hargitse kamar ɓera ya hango kyanwa. Daga baya da suka gane tsokana ce sai suma suke mayar da martani, har kuma abin ya zamo wasan tsokana.

Amma dai ance har zuwa yau, babar-bare ya yadda ya sanyawa ɗansa suna Usmanu, amma ba ya sanya sunan Rabeh ko Rabi’u.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!