Connect with us

TATTAUNAWA

Zuwa Makka A Mota: Irin Tashin Hankalin Da Na Gani -Hajiya Jummai

Published

on

Tun cikin Shekarun 1993 zuwa 95, wasu ƙungiyoyin addinin Musulunci da rukunin jama’a da gwamnatoci sun fara yunƙurin shirya tafiya aikin Hajji ta mota, inda aka yi ta gwaji cikin shekaru uku, amma ganin wahalar da ke ciki ta fi ribar tafiyar yawa, dole aka bar wannan shiri. Wakilinmu MU’AZU HARƊAWA ya kasance cikin irin wannan tafiya a shekarar 1995, ya samu halarta, kuma ya sake jarraba ta a shekarar 2007 a ƙashin kansa. Amma kasancewar yaƙe-yake sun yi yawa a hanya, tsakanin ƙasar Chadi har zuwa Sudan, don haka ya fahimci tun a wancan lokacin tafiyar na cike da haɗari.

Bayan haka kuma kimanin shekaru bakwai zuwa takwas rikicin Boko Haram ya sake fitowa ya lalata wannan hanya. Madadin a baya tafiyar a wa huɗu daga Maiduguri zuwa Njamena, babban Birnin ƙasar Chadi, yanzu ya koma tafiyar kwanaki uku daga Kano zuwa Daura a fice, a nufi Zindar a ɓulla zuwa Diffa a cikin Nijar, kafin a shiga ƙasar Chadi.

Saboda kuwa ‘Yan Boko Haram sun kashe hanyar Maiduguri zuwa Gamboru zuwa Potocol, a wuce Kusseri kafin a shiga Ngueli a ƙasar Chadi a shiga birnin Njamena. Duk da irin wahalar da ke cikin wannan tafiya Hajji ta Mota, tun daga wancan lokacin har zuwa wannan lokaci akwai mutanen da suke bayyana aniyarsu ta bin wannan hanya daga Nijeriya, kamar yadda wasu ke shiga cikin haɗari suke bin ƙasar Nijar zuwa Libya su hau jirgin ruwa mara inganci ba tare da wasu takardu ba su ƙetare zuwa turai.

Wakilinmu ya ci karo da wata mata a lokacin Umrah, mai suna Hajiya Jummai Mohammad daga Borno, a unguwar Sharie Sittin da ke Makka wacce ta bi wannan hanya ta samu shiga Makka ɗin. Saboda jin irin wahalhalun da ta sha a Sudan, da Yemen da sauran wurare kafin ta kai ga shiga ƙasar Saudiyya, hakan ya sanya shi rubuta mana wannan hira mai cike da darussa don amfanin jama’ar da suke son bin wannan hanya, saboda hakan zai sa mutum ya san irin wahalar da zai shiga idan ya ɗauki wannan niyya, saboda ya san irin halin da ake fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance: Hajiya Jummai kamar yadda na san haɗarin hanyar nan da wahalarta, yaya taku tafiyar ta kasance a ƙarƙashin dillalan Sufuri?

Assalamu alaikum, a lokacin da muka ƙudiri niyyarwannan tafiya, mun haɗu da dillalan tafiyar shekaru shida da sukagabata, suka ce mu bi ta wannan hanya ta fi sauƙi kan farashin Nairadubu 150, alhali a jirgi kuma ana biyan Naira dubu 300 wato kaga rabinkuɗin jirgi kenan.

Amma wasu har naira dubu 130 suna karɓa,yarinyata da ke goyekuma na biya mata naira dubu 30 a matsayin nata kuɗin tafiyar. Sunkuma ce za su kawo mu Saudi Arabia cikin makonni biyu, amma sai da mukashekara biyu bamu isa Saudiya ba.

A karon farko bayan mun bar Maiduguri sun kawo mu Gamborun Ngalakan iyaka da dare tun daga nan muka fara da rashin sa’ar, masauki kawaiya zama jidali.

Bayan mun yi Sallar isha mun sha ruwa sai aka kawobabbar mota ta kwashe mu zuwa Kusseri a cikin Kamaru, da karfe uku nadare muka iske wani kogi aka ce mu sauka mu haye da ƙafa motar za tagewaye, ga kaya ga duhun dare ga goyo, tun daga nan na fara fahimtarza a sha wahala cikin wannan tafiya, muka shiga ruwa har ƙirjinmu muka haye.

Bayan motar ta gewayo mun shiga sai jami’an tsaro suka riƙe muaka kawo mu Caji ofis aka sauke mu aka shiga da motar aka ce mu biyanaira dubu uku kowa muka biya,da rana aka kai mu wajen manyansusuka sa hannu. Maimakon mu wuce sai aka sake kawo babbar mota mu wajen70 da ‘yan sanda aka wuce damu zuwa wani ofis cikin ƙasar Kamaru, tundaga nan muka fahimci tafiyar ba ta izini muke yi ba.

Don sun ce mana mune ɓarayin ƙasa masu tafiya ba izini daga nan aka dawo da mu Gamboru, sannan muka ga dillalinmu ya aiko aka sake sanya mu a wata motar muka shiga aka sake bi da mu ta gefen kogin da muka wuce tun farko. Muka sake haye wani kududdufi nan aka ajiye mu har magriba.

A nan muka yi tunanin wannan wajen akwai namun daji kar su zoshan ruwa da dare wani abu ya samu wani, sai muka tashi muka kama hanyabayan magriba zuwa wani gari mai suna Fotokol, har mutanen garin sukayi ta kawo mana kunu da abinci.

Daga wannan gari sai masu babur sukazo suka ce za su shiga damu Kamaru amma kowa sai ya bada naira dubuuku, saboda mun matsu muka bayar wasu daga cikinmu saboda santsi daaka fara daukarsu har suka yi haɗri wata ta karye.

Ga yunwa gakishirwa kwanaki biyu har tafiyar ta fara fita ranmu, ga kayanmu damotar can a wajen ‘yan sanda, sai daga ƙarshe suka ce kowa ya zo yaɗauki kayansa muka je muka yi ta ɗiba muka shiga wata motar zuwaNjamena cikin ƙasar Chadi.

Don tsabar neman kuɗi da cuta irin ta Agent wato dillalin safararmutane, suka kawo mota suka haɗa ƙarfi suka kawo Bos zuwa Abeshetsakiyar Chadi, wajen zaman mutum biyu mutane uku suka cusa muka shigamuka bar Njamena bayan sallar magariba.

Amma kasancewar wannan wajeana gyaran hanya ga kuma cunkoso a motar ga kaya a sama ya fi ƙarfinmotar ana cikin tafiya ba daɗi da muka zo wani tudu kafin motar ta

gangara sai ta rinjayi direban ta faɗi ta kife da mu, Allah ya sa ba agudu sosai, nan Allah ya takaita ba mai gajeran kwana aka fitar da muamma wasu sun kakkarye musamman wasu ‘yan ƙasar Chadi ne sun samuraunuka.

Wannan yarinyata kuma sai da aka fasa gilashi aka jawota tanagoye, kuma nauyin Lodin kayan saman motar da su baburan hawa da ke kaisune suka hanata ci gaba da gungurawa ta tsaya waje guda aka kawo watamotar muka shiga muka wuce zuwa Abeshe.

Bayan kwana guda muka wucezuwa Adre ƙarshen iyakar Chadi, muka kwana guda, shine garinda kan iyaka da Sudan, bayan mun sha wahalar da bata misaltuwa.

Daga Adre suka kawo babbar mota Daf suka kwashe mu zuwa Eljineinacikin ƙasar Sudan tafiyar da bata wuce Kilomita 20 ba sai da mukakwana shida ga zafin rana ga wahala duk anata kewaye-kewaye da yake batafiyar ka’ida suke yi damu ba.

A Eljinaina kwananmu uku muka yi tasayar da kayan da muka taho da su irin su goro da ‘yan kunnayenmu nagwal ga wanda ke da shi don samun guzurin ci gaba da tafiya.

 

Na san a wannan lokaci ana yaƙi a Darfur cikin Sudan, ta yaya ku ka isa Khartoum babban birnin Sudan?

Mun bar Nijeriya tun ranar biyar ga Azumi, amma sai wajen 26 muka isa Khartoum . Don a karon farko zaka ga duk yadda ‘yan gudunhijirar suka yi bukkoki gwamnati suka tsugunar da su, ga kuma garuruwankan hanya a ƙoƙƙone sojoji ta ko ina a tare mu a nan a wuce a gewayenan a shige, wani lokaci a yi rashin sa’a sai an ba sojojin ‘yan tawaye ko na gwamnati maƙudan kuɗi kafin a wuce, da haka muka isa Khartoum.

lokacin Bizar Fasfunanmu wato iznin shiga ƙasar Saudiyya nagab da ƙarewa, don basa nuna fasfon a kan hanya saboda kar su biyakuɗin ka’ida mai yawa na takardu a Kamaru da Chadi. Kuma cikin wannan tafiya akwai ‘ya’yan Agent namu da matarsa uwaryaransa duk da su muka yi, sunansa Madu Kur babarbarene ɗan Maiduguri.

Da daddare sai ya ce damu zai faɗa mana gaskiya kuɗin hannunsa ya ƙarekuma saura kwanaki biyu a yi sallah, don haka duk wanda ke da kuɗinhawa jirgin sama ya hau ya ƙetare don idan aka yi sallah Biza ta ƙare.

idan mutum kuma yana da wanda zai buga ya aiko masa kuɗi daga Saudiyyaya buga.  Amma saboda waje ya ƙure haka muka rungumi ƙaddara muka haƙura yasamamana waje babban fili muka zauna tunda dama shi yana shigowa Sudan ya san mutane.

Cikinmu ga tsoffi haka muka zauna muka yi tabauta shekaru biyu mune wanki da hannu mune aikin gona muna boyi-boyi, da sauran aikin wahala, muna ta neman kuɗin da zamu biya mu hayo zuwaSaudiyya, ko mu koma Nijeriya, don tafiyar duk ta fita daga ranmu.

Sai kawuni kana wanki ba adadi kafin a baka Jine dubu naSudan wanda baiwuce Naira ɗari biyu ko uku ba.

Haka muka shekara biyu wasu har sukayi ta aure, amma akasarin maza da aka yi sallah sai suka koma gidaNijeriya, amma mu mata haka muka zauna muka yi ta wahala har shekarabiyu muka samu  abin da muka samu.

Muna zaune sai wani mai suna Umar ya bamu labarin akwai wanda keaiki a Kasala wani gari a Sudan ga duk mai son wucewa zuwa Jizan cikinƙasar Yemen daga nan sai a kai mutum zuwa Saudiya, garin kuma yana canwajen Bahar Maliya.

Da jin wannan labari sai muka nuna sha’awa akaɗaure kaya muka bi ƙungiya da ɗan guzurin da muka samu suka kwashe mua cikin mota zuwa wani daji mai cike da ɓarayi suka ajiye mu.

Idan sunzo sun tambayemu abinci ko ruwa sai mu basu don an ce idan mun hanasuza su kashemu.

Muna zaune a wannan daji na Kasala wata rana da dare aka kawoakori kura aka zubamu zuwa bakin Bahar Maliya kuma bamu isa wajen basai takwas na safe akace ga jirgi za mu shiga mu tafi.

Mun zaci za muga Jirgin ruwa babba irin wanda muka saba gani a hoto sai aka kawoƙaramin Jirgi kwale-kwale da rumfa da inji a baya, wanda kowa ya ganshi aka ce zai shiga tekun Bahar Maliya da mutane to an san akwaikasada cikin lamarin.

Haka aka lodamu kamar masu tafiya lahira ba matakala sai an turamutum kuma kafin akai wajen da jirgin yake ruwa har iya kirji hakamuka yi ta gudu muka shiga kamar a silima munkai mu 120.

Wannan jirgiciki ga wari ga ƙunci mata na ƙasa maza na samansu haka aka burga akashiga maliya da mu idan ruwa ya yi toroko sai ya tashi sama har cikinjirgin, ga manyan kifaye suna tashi sama a cikin ruwan suma kamar za sushigo cikin jirgin manya-manya wasu kamar awakai.idan sun miƙe samaruwa ƙasa ruwa, sai da muka kwana huɗu muna tafiya ko ina shuɗi baalamar ƙasa ko kukan tsuntsu ko wani abu sai sarautar Allah muke kalloa cikin teku.

Wani abin mamaki da ikon Allah muna cikin tafiya bayan magribawani bawan Allah yana zaune kamar wani abune ya ja shi sai muka jizundum kawai a cikin Bahar Maliya ya faɗa, muka yi kururuwa masu tuƙajirgin suka ce ba yadda suka iya,  don ba mai iya shiga wannan ruwa koda rana ne balle tsakiyar dare, haka Allah ya karɓi ran wannan mutummuka wuce.

Don wannan mutum ana hira da shi har yana cewa yau kwananmubiyu a wannan ruwa ko yanzu mun yi shahada, kuma ɗan Nijeriia ne, amma aSudan yake zaune.

Haka muka yi ta fafiya ba abinci na azo a gani sai abin da kashiga dashi sai kuma ruwa da masu jirgin suka zo da shi a jarkoki idanka buƙata su ɗan samma, haka muka yi ta tafiya ko sallah ba yaddazakayi baka ci ba balle ka nemi zagawa.

Sai a kwana na huɗu muka samuwani tudu a tsakiyar teku sai muka tsaya suka buga waya sai aka turowasu ƙananan jirage masu gudun masifa su shida suka zo aka riƙa mannasu a jikin wannan babban jirgin da muka taho da shi tsawonsa kamarɗaki muka riƙa tsalle muna faɗawa cikin ƙananan jiragen maza sunataimakonmu muna miƙo yaranmu kowane ya ɗauki mutane 20.

Ni jirgin da muka shiga direban ya cika sabga har mai ya ƙare yabuga musu waya wani ya juyo ya kawo aka zuba duk a tsakiyar teku mukaci gaba da tafiya.

Da yake direban wani watsatstsene duk da wannanwahalar da muke ciki ya samu wata ‘yar Habasha a ciki suna ta hira,Mai yasake ƙarewa muka tsaya a wani tsibiri ba komai wajen saisu dodon koɗi da ƙaguwa muka sauka kan tsibirin, muka yi ta wanke jikiya buga waya aka sake kawoMai muka wuce zuwa ƙasar Yemen, aka ce karmu sauka akwai jami’an tsaro mu jira sai dare yayi,sai da daren yayi muka sauka ruwahar iya ciki muka haye muka isa kan ƙasa.

 

Da kuka isa Yemen to sai kuma wace hanya kuka ka bi zuwa Makka?.

Ai kasan tun da duk tafiyar bata Ƙa’idabace haka nanmu ka yi ta fama da ‘yan hauma-hauma nanma suka buƙaci mu biya kuɗimaƙudai zuwa Jizan cikin Saudiya, har sai da muka biya kuɗi sau huɗuduk ba a kai mu Jizan ba ga cuta a wajen Yamanai komai kake so sai daika aike su,kuma idan sun karɓi kuɗinka ba za ka sake ganinsu ba, kuɗinka ya tafi.

Dahaka muka isa har kan iyaka aka ɓoyemu cikin wani gida kafin dareya yi a lura da yadda yanayi yake sannan a ƙetare da mu.

Mu dai awannan tafiya mu 18 motar ta kwaso zuwa kan iyakar Yemen da Saudiya.

Haka aka tara mota huɗu a wajen muka kwana biyu aka loda mu aka tafiaka sake dawowa aka ce akwai bincike a hanya suka dawo da mu muka sakejira, daga baya suka fita da mu ta cikin daji ga duwatsu ga kaya.

Ga kwazazzabai suka kwashe mu muna sauri da ƙafa cikin dare ta dajiwai za a kai mu wani gari mu shiga motar Makka haka muka yi ta tafiyahar muka gaji muka yi ta watsar da kayayyakinmu, duk takalma sunyayyanke ƙafarmu, ta ko ina ƙayoyi ne har ƙarfe goma na safe, kumaidan mun hango wutar mota a daren sai mu ɓoye mu faɗi ƙasa idan sun wuce mu tashi mu ci gaba.

Ƙasarsu ga laushi ba irin tamu ba, harƙwauri haka muka kwana biyu muna tafiya ko takalmi babu, ƙafafu harjini su ke yi.

Da haka suka yi mana jagora zuwa wani gida inda suka ɓoye mu, to a nan kuma wanda ke da ‘yan uwa a Makka sai ya buga waya idan kuma kanada kuɗi ka biya don a ɗaukeka zuwa Makka a Mota kan farashin JakarSaudiya Uku, wato Riyal 3000 daidai da naira dubu 120.

A lokacin yarokuma ko yau aka haifeshi riyal 500 za’a biya masa, idan kumababba nemace ko namiji Riyal 1000.

Dillalan suna da mutanensu a Saudiya idan kana da mutum sai su je su karɓada sun karɓa sai a sa ka mota idan kuma kana da kuɗi shike nan sai kabiya a ɗauke ka cikin hanzari don basa son mutane su zauna a wurinsaboda jami’an tsaro suna kawo sumamesu kama mutane.

Kuma wani abintakaici idan sun kwashi mutane maimakon su kai su Makka, idan baka yisa’a ba sai su sake kai su wani ƙauyen, kamar yadda  suka yi mana sukaajiye mu cikin wani gida a wani ƙauye muka kwana biyu ko ruwan shababu balle abinci.

Sai daga baya muka bada kuɗi suka kawo mana gurasa da madara a cikin wannan ƙauye muka ci muka fita zuwa cikin wani ƙauye sukataimakemu da abinci.

A cikin wannan daren sai ga wani ya zo ya sake ce mana mu fita awannan gida ko ya kira mana hukuma, kuma duk cikin ƙasar Saudiya ne, anan ne wata mata ‘yar Maiduguri mai suna Sadiyya da ɗanta Mu’azzzam.

Haka muka neme su muka rasa saboda wahala, dama tana cewa bata dalafiya tunda muka taso a Sudan muka haɗu da ita, kuma inajin ta faɗita rasu ne, don mutane da yawa suna rasuwa a wannan hanya tsakaninSudan da Yemen wasuma Jirginsu yake kifewa duk su hallaka.

Kai! in taƙaita maka labari a cikin ƙasar ta Saudiya haka muka yi tatafiya mu yi gaba mu dawo baya har sai da muka kwana 17 sannan  muka isa inda muka hau motar Makka.

Tunda da dare ake tafiya idan rana ta yisai a nemi waje a ƙauye a fake, wata rana har ruwa ya sauƙa ya yi manadukan tsiya, sannan wani bawan Allah ya kai mu wani gida ya ajiye mu,aka kai mu Jizan a cikin Saudiya aka ɓoye mu a wani gida aka kawomana ruwa muka wanke jikinmu muka huta.

Me wannan gida ya ɗeboƙananan motoci biyar aka kwashe mu zuwa wani kwari don wani ya ce zaiyi mana cune azo a kamamu duk tafiyar mu ta zama ta banza.

Daga wannan gari Kamisbishek aka kwashe mu zuwa wani dutse canaka boye mu,  don kar azo a kama mu haka dai muka yi ta shan wahala dukdon kaucewa jami’an tsaron Saudiya don kada mu yi wahalar banza, daga ƙarshe Allah ya taimake mu aka kawo mana wani direba mara tsoroya ɗauko mu zuwa Ta’if duk inda ya ga akwai mushkila sai ya kauce yashiga daji haka ya ajiye mu a wani gida,cikin dare ya sake zuwa yakwashe mu daga Ta’if muka yi shahada kai tsaye muka nufi Makka.

Allahmarufin asirin bawa ya hayo da mu ba tare da wani dogon bincike ba, kwananmu 25 cikin wahala daga Sudan zuwa Makka. Alhali duk anayi mana komai a rufe ne bamu san duk za mu shiga wannan wahala ba.

Idan da mun sani ba za mu taɓa shiga wannan haɗariba, sai mu zauna a gida har lokacin da Allah zai kira mu mu zo ta jirgin sama.

Don haka na ke kira ga gwamnati ta ɗauki mataki kan dillalai sufurimasu shirya irin wannan tafiya a hanasu zuwa Saudiya ko masu shiga Turai, don mukan mun ga mutuwa muraran amma Allah ya kawo mu, Allah kawai ya sanwahalar da muka sha wallahi.

Kuma mutane su nisanci bin wannan hanya, gara su tara kuɗi su bi jirginsama shi ya fi musu alheri, don nisan kwana ne ya kawo mu wannanlokaci a yi wa kai Ƙiyamullaili don mutane da yawa sun mutu, kuma hargawarwaki za ka riƙa gani a kan hanya.

Don Allah shugabanni kuma sutaimaka su gyara mana ƙasa don mutane su riƙa zama a gida ba tare dasuna tafiya Turai ko irin waɗannan ƙasashe suna shan baƙar wahalaba.

Haƙiƙa akwai gawarwaki a kan hanya na wanda suka mutu, wani lokacikuma ƙasusuwan mutane za ka gani sun mutu, wai a hakan ance mu mun zocikin daɗi, don akwai wanda ya zubar da yaransa da matarsa a hanya daƙyar ya iso Makka shi kaɗai kuma sun halaka har abada sai ko a hadu aƙiyama.

Wani lokaci kuma har faɗe ‘yan Yeman suna yi wa mutane,maza a yimasu fyaɗe mata ma a yi musu. Akwai jirgin ruwan da aka ce ya kife dukya kashe mutanen da ke cikinsa lokacin tafiyar tamu kamar yadda keaukuwa ga masu tafiya Turai da Libya.Kuma banda wahalar da muka sha, wannan tafiya ta ci yafi Milyan,saboda kuɗin da na bar gida da su da wanda na yi ƙodago na samu aSudan na kamo hanya da wanda dangina da ke Saudiya suka aika mini don awuce da ni daga Yemen wallahi! idan an tattara na kashe sama da NairaMilyan guda ga baƙar azaba, don haka jama’a a yi hattara da wannanhanya babu  alheri cikinta, kowa ya zauna inda Allah ya ajiye shikurum.

Saboda idan zan baka irin wahalar da na sha sai ka gaji daɗauka, don haka sai ko a misalta kurum, don wannan tafiya ba ta dabanbanci da ta masu zuwa Turai, don haka sai dai mu gode wa Allah kawaida ya kawo mu har wannan lokaci a raye. Da fatan idan kunne ya ji jikiya tsira Allah ya wuce mana gaba amin.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!