Connect with us

RA'AYINMU

Tsakanin Bankuna Da Kamfanoni Masu Zaman Kansu

Published

on

Kwanan nan wasu labarai suka riƙa yaɗuwa kan yadda wasu bankuna a ƙasar nan suke kullewa kamfanoni masu zaman kansu asusunsu ba bisa ƙa’ida ba, tsawon lokaci su yi ta fama suna bibiyar yadda za a buɗe masu asusun nasu somin su koma ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.

Cikin kamfanonin da suka tsinci kansu kansu a irin wannan badaƙala akwai Cashflow, wanda aka kafa domin tallafawa marasa ƙarfi ta hanyar koya masu sana’a da ba su jari. Sai dai kusan shekaru bakwai asusun wannan kamfani da ke Banki Diamond an kulle shi, saboda haka ba su da ikon gudanar da wata hada-hada. Sun yi iya bakin ƙoƙarinsu don ganin an buɗe asusun amma lamarin ya ci tura, duk da cewa sun bi hanyoyi da suka dace bisa doka don dawo da dukiyarsu da ke neman kuɓ ucewa.

Daga cikin matakan da suka fara ɗauka sun haɗa da garzayawa babbar kotun Abuja, inda kotun ta bada umarni a buɗe masu asusun tun wasu lokuta a baya, amma dai wasu dalilai suka hana bankin buɗe asusun.

Wasu daga cikin manyan jaridun ƙasar nan sun rawaito, a makon da ya gabata, Majalisar Tarayya ta kafa wani kwamiti domin jin yadda Bankin Diamond ya rufe asusun kamfanin Cashflow tsawon shekaru, ta yadda ba su da damar ci gaba da hada-hada da abokan hulɗarsu aƙalla na tsawon shekaru bakwai, shugabannin kamfanin sun iya bakin ƙoƙarinsu don ganin an buɗe asusun domin su bawa abokan cinikiyyarsu damar hulɗa kamar yadda suke yi a baya.

Wannan lamari ya tagayyara dubunnan mutane, domin masu hulɗa irin waɗannan bankuna suna da yawan gaske, kuma da suna kwastomomi a ƙarƙashinsu waɗanda ke zuba hannayen jari ko karɓ ar rance.

Abin lura shi a nan, mutane da yawa waɗanda suke hulɗa da ire-iren waɗannan kamfanoni sun shiga wani hali, wanda kamata ya yi a ce hukumomin da abin ya shafa su kalli lamari da idon basira domin fitar da jaki daga duma. Sha’anin kuɗi abu ne mai wuyar gaskiya, domin a wannan zamani suna cikin sinadaran gyara rayuwar ɗan adam da kuma lalata su.

Waɗanda suka tsinci kansu a wannan yanayi sun shiga mummunan hali, da yawansu sun kasa biyawa ‘ya’yansu kuɗaɗen makaranta, wasu abinda za su saka a bakin salati ma gagararsu yake yi.

Ɗaya daga cikin wanda bala’in kulle asusu da bankin Diamond ya shafa, a wata hira da aka yi da shi a gidan jaridu, ya bayyana irin wahalar da suka sha tsawon shekaru bakwai suna fama a buɗe masu asusu amma lamarin ya ci tura. Ya koka matuƙa, a cewarsa da kuɗinsu na haram ne ai da tuni hukuma ta kama su, amma kuɗaɗen da suke juyawa na hada-hadar ciniki ne da tallafawa mutane da jari, amma yanzu komai ya tsaya cak saboda maƙarƙashiyar da aka shirya masu.

A wannan gaɓ ar, da lamarin ya kai Majalisar Wakilai, har ma ta gayyato Babban Bankin Ƙasa, Bankin Diamond da Hukumar EFCC, hatta jagoran kwamitin da Majalisa ta kafa don binciken badaƙalar, Nkem-Abonta, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda CBN ke haɗa kai da bankunan ‘yan kasuwa ana cutar da kwastomomi, inda ya ce bankunan da suka yi ƙaurin suna a wannan fanin sun haɗa da First Bank, Sky Bank da sauran su.

A ƙarshe ya buƙaci a samar da wani wuri na musamman domin haɗuwa da dukkan waɗanda abin ya shafa don duba yiwuwar dawo masu da hakkinsu. Cikin waɗanda ake sa ran za su halarci zaman a 30 ga watan nan, akwai Babban Sufeton ‘Yan Sanda Ibrahim Idris.

A namu ra’ayin, muna ganin adalci ya kamata a yi wa ire-iren waɗannan mutane da suka himmantu wajen neman na kansu da kuma tallafawa marasa ƙarfi da sana’o’i ta yadda za su dogara da kansu. Bai kamata a ce mutumin da yake ƙoƙarin kafa kasuwancinsa har ma ya taimaki wani, a haɗa baki da wasu tsirarun mutane a tagayyara shi ba, wajibi ne ga mahukunta su yi nazarin halin da waɗannan bayin Allah suke ciki domin fitar da su daga mummunan yanayi.

Kowa yana sane da irin halin da ake ciki a ƙasar nan na talauci da rashin gilmawar kuɗi, kuma gwamnati na iya bakin ƙoƙarinta wajen ɓ ullo da sabbin dabarun warware matsalolin da al’umma suke ciki, a hannu guda, ɗaiɗaikun mutane suna amfani da nasu ikon domin ganin an haɗa hannu da ƙarfe wajen samawa matasa ayyukan yi.

Lallai lokaci ya yi da ya kamata a daina kashin dankali a ƙasar nan, a sakarwa ‘yan ƙasa nagari mara su fitsari, ba wanda zai cutar da al’umma ba, wanda zai taimaka wajen ci gaban ƙasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!