Connect with us

MAKALAR YAU

Alkalamin Fadilah: Wace Rawa Mata Za Su Taka A Lokacin Zabe?

Published

on

08035416669               [email protected]

A daidai lokacin da muke hararar shekarar ta 2018, wanda a cikinta ne ake tsammanin guguwar siyasar kasar nan za ta fara kadawa a ko’ina, haka zalika da yadda ‘yan siyasa suka kurawa tukunyar da aka aza ido domin ganin wane irin romo za ta sauke ya dace aka kallin abubuwa da yawa wadanda sune kashin bayan samun zaman lafiya a kasa.

Mata na cikin jinsi da ke taka rawa wajen ci gaban kasa da tattalin arzikinta, wannan tasa masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa ke mayar da hankulansu kan mata domin sanin irin muhimmancin da suke da shi a rayuwar al’umma, da kuma irin rawar da za su iya takawa a lokutan zabe.

Masu iya Magana suna fadin “Mata su ne ginshikin al’umma” har wa yau su ne bango da ake jingina da shi idan har ana son samun daidaito a cikin al’amura. Mace tamkar gishiri ce a cikin miya, wanda dole sai da shi sanwa ke dadi. Allah (SWT) Ya halicci mace domin ta daukin nauyin kula da al’umma tun daga farkonta har karshe. Mata su ne ke da alhakin kula da tarbiyya da ilmin kowace al’umma. Duk al’ummar da ta rasa mata nagari babu shakka ta yi asara mai girma.

Haka zalika mata su ne ke rike da akalar duniya ta fannin daukar nauyin kula da dimbin al’ummar da ke cikinta, hakan na nuni da cewa ba don su ba, da ba a samun yawan jama’ar dake yawo a doron duniya ba. Mata suna da wani irin sinadari da za su iya canja yanayin rayuwar mutane kama daga zamantakewa har zuwa harkokin yau da kullum. Idan har sun yi amfani da tunaninsu a inda ya dace, shi ne ya sa a lokutan irin wannan da matasa ke fitowa kwansu da kwarkwata domin gudanar da wasu ayyuka hankula ke karkata kan iyaye mata saboda masaniya da a ke da ita kan cewa, suna da tasiri babba wajen sa wa ko hanawa a sha’anin rayuwa.

Haka abin yake a tafiyar siyasa musamman ta kasar nan. Kima da mutuncin mata a idanun ‘ya’yaye bai zube ba, saboda haka ne masu fashin baki ke ganin har yanzu matan suna da gagarumar rawar da za su iya takawa wajen dakile matsalolin da ka iya zuwa su dawo a lokacin gudanar da zabe.

Har ila yau, a zabukan da suka gabata, mun ga irin gudunmawar da mata suka bayar wajen kawo sauyi da kua fita kwansu da kwarkwata domin kada kuri’a. baya ga wannan, mata sun fito tare da tsayawa takara a matakai daban-daban.

Babban misalin da za a kalla shi ne, Hajiya Aisha Jummai Alhassan, da tsaya takarar gwamna a jihar Taraba. Duk da cewa ba ta samu nasara ba, amma hakan ya nuna irin yunkuri da mata suka yi domin a dama da su a tafiyar siyasar kasar.

Sannan, da yawan mutane sun yi tsammanin za a gamu da tashin hankali matukar aka sanar da sakamakon zabe, amma cikin ikon Allah da kuma irin tsayuwar daka da iyaye mata suka yi wajen wayar da kai ‘ya’yansu kan muhimmancin zaman lafiya, ya sanya abubuwan da aka rika zato ba su faru ba.

Haka zalika, babu mutumin da zai musa irin gagarumar gudunmawar da uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Muhammadu Buhari ta bayar wajen tabbatar da zaman lafiya a zaben shekarar 2015.

Idan muka kalli kasashen duniya tuni mata suka zama wani ginshinki a tafiyar harkokin rayuwa; ilmi, tattalin arziki, siyasa da mulki, saboda a cikin matasan da ke kai kawo cikin lamura mata na da iko a kansu wajen tankwara su, da hana su aikata munanan dabi’u, musamman tayar da tarzoma a lokutan zabe.

Kungiyar Kare Hakkin Mata karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya ta yi wata Makala ranar 20 ga watan Janairun 2015 kan irin rawar da mata suka taka a zaben da aka gudanar a kasar Jamhuriyyar Congo. A cikin Makalar suka ce, mata suna da gagarumar rawar takawa domin tabbatar da ci gaban dimokradiyya ta hanyar wanzar da zabe mai tattare da zaman lafiya, duk kuwa da irin kalubalane da suke fuskanta wajen cudanya da maza, musamman a sha’anin tsaro da ayyukan jam’iyya. Suka kuma ce, bai kamata mata su tsaya a matsayin masu kada kuri’a kawai ba, a’a, su rika shigowa cikin lamura ana damawa da su.

A shekarar 2010, kasar Kenyan ta yi wa Kundin Tsarin Mulkinta garambawul, wanda zai bawa mata cikakkiyar dama a lokutan zabe, wanda ya hada da; gabatar da Kasidu, Mujallu da manyan taruka da za a rika gabatar da lakcoci domin karkato da hankulan matasa masu yunkurin tayar da zaune tsaye idan ba su samu sakamakon zabe yadda suke so ba. Tun daga wannan lokaci Kenya ta shiga cikin sawun kasashen masu gudanar da sahihin zabe a duniya.

Nijeriya kasa ce da ta yi fama da rikice-rikicen zabe a shekarun baya, wanda ya yi sandiyar da salwantar rayuka da dukiyoyi. Wannan na da nasaba da irin saniyar ware da ake mayar da mata a cikin al’amuran siyasa da zabe. Abin da ake kallon mata da shi kawai bai wuce ranar zabe su kada kuri’a su koma gida ba. ‘Ya’yan da ya kamata su bawa kulawa, da kuma dora su kan hanya madaidaiciya, sun bar su a filin zabe suna gararamba, wanda daga haka sai a ji mummunan labari ya faru.

Mata suke rike da akalar rayuwar al’umma, saboda haka kamata ya yi su yi amfani da wannan dama wajen wayar da kan matasa; maza da mata wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a cikin tafiyar siyasa. Wannan shi ne aikin da fitacciyar ‘yar siyasa, Marigayiya Gambo Sawaba ta tsaya a kai, har zuwa lokacin da ta amsa kirana Mahalicci. Ta yi gwagwarmaya iya karfinta wajen dora mata kan hanyar shiga lamuran siyasa domin sai suna ciki ne za su iya samun damar da ke akwai wajen jan hankalin ‘ya’yansu kan inda siyasar ta sa gaba.

Tashin hankali ba shi da wata rana a zamantakewar rayuwa, ta shi ne ake samun rabuwar kawuna tsakanin jinsin al’umma mazauna kasar nan. Saboda haka akwai bukatar mata su tashi tsaye domin nusar da ‘ya’yansu inda dimokradiyya ta sa gaba.

Dimokradiyya tsari ne da ya bai wa kowane dan kasa damr zabar abin da yake so, saboda haka, kuskure ne iyaye su bar ‘ya’yansu a rika sanya musu mummunar akidar tsanar wani dan takara, kuma makauniyar soyayya ga wani da har za su rika jin idan ba shi ya ci ba, to babu wata hanya ramawa sai ta tashin hankali da kone-kone. Wannan gurguwar dabara ce, domin kuwa shi tashin hankali.

Matukar iyaye mata suka tashi tsaye, suna nusar da ‘ya’yansu muhimmancin zaman lafiya da kaucewa ‘yan siyasa masu tunzara kantu ya fada ruwa, babu shakka abubuwan da suke faruwa a maras dadi a kasar nan za su ragu. Fatanmu Allah ya sa al’umma ta gane.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: