Connect with us

SIYASA

Ayyukan Cigaba Da el-Rufai Ke Yi Ya Sa Na Dawo APC – MS Ustaz

Published

on

ALHAJI MUHAMMAD SANI ABDULMAJID, ya kasance tsohon Mataimaki na musamman akan harkokin aikin hajji ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Namadi Sambo.  Kuma dan kasuwa ma zaunin Jihar Kaduna.  A cikin wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu IBRAHIM IBRAHIM a Kaduna.  Ya bayyana babban makasudin shi na ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC. Ga yadda hirar tasu ta kasance:

Da farko ka gabatar mana da kanka?

Suna na Muhammad Sani Abdulmajid wanda aka fi sani na da MS Ustaz, kuma ni ne tsohon Mataimaki na musamman akan harkokin aikin hajji ga Alhaji Namadi Sambo, Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna.  Sannan dan kasuwa kuma tsohon jigo a jam’iyyar PDP, wanda yanzu ya canja sheka zuwa jam’iyyar APC mai adalci.

 

Mene ne dalilin ka na barin jam’iyyar PDP?

Inaso na sanar da al’ummar Jihar Kaduna da Nijeriya cewar, bayan nazari da tattaunawa da kuma janyo hankali daga ‘yan uwa da Abokan arziki, Matasa da Dattawa wanda a kullum cikin wasa da dariya cewa Ustaz ka dawo jam’iyyar APC.  Kuma na zauna  nayi nazari musamman da yadda na dade ban shiga Garin Rigasa ba,  amma daga bisani  na shiga cikin Garin Rigasa na ga yadda Gwamnan Jihar Kaduna ya zuba masu ayyukan hanya wanda babu wata gwamnati wacce ta taba yi masu  makamancin hakan.   Sannan na shiga yankin Unguwar Dosa, Kawo, Barnawa, Kakangi da dai sauran Unguwanni, duk na ga irin yadda wannan gwamnati ta zuba masu aiki.  Sannan na zauna na tambayi al’umma cewar wai yadda na ga ana aiki cikin Garin Kaduna, haka sauran Kauyuka ake masu?  Aka ce mun kwarai da gaske, babu inda aikin wannan gwamnati bai kai ba.  Sannan a lokaci guda wani Abokina dan jam’iyyar APC ya ce mun nazo muje mitin a Sakatariyar jam’iyyar APC domin an sa  suna na cewar an gayyaceni,  kuma naje na ga yadda tsarin taron su yake  cikin tsari da ladabi ga kuma karamci.  Gaskiya wannan abin ya bani sha’awa, a cikin zuciyata  nace ya kamata nayi ma el-Rufai adalci.

Wannan na daya daga cikin dalilin da ya sanya muka zauna tare da al’ummar mazabata da ke yankin Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu,  mu ka yanke shawarar cewar,  a dalilin irin kyakkyawar aikin gwamnatin jam’iyyar APC a  karkashin jagoranci Malam Nasiru El-Rufai,  mun yanke shawarar barin  jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai adalci,  ba domin a bani kwangila,  kudi ko mukami ba,  saboda ni kudi ko dukiya basa  tsolemun ido,  saboda muna da sana’ar mu da mu ke yi,  kuma da ita mu ke ci har mu tallafa ma al’umma.  Na zauna nayi nazarin  cewar har idan ban bar al’ummata sun koma jam’iyyar APC ba,  to tabbas babu makawa sai Allah ya tambayeni, domin Allah da kansa ya ce,  kar ku bari saboda gabar da ke tsakanin ku da Abokan gaba ta hana ku bin gaskiya.  Kuma yin biyayya ga na gaba wanda bai saba ma Allah ba wajibi ne.  Kuma ko shakka babu Gwamna El-Rufai ya cancanci a bishi saboda irin kyakkyawar yakini da yake da shi ga al’ummar Jihar Kaduna.

 

Amma wasu na fadin cewar babu wani abu dake cikin APC illa kame-kame da hargagiya, domin babu wani abu da ta tsinana ma al’ummar kasar nan sai kunci da yunwa.  Sai ga shi kai da rana tsaka kana sallama za ka shigo cikin jam’iyyar APC?

Duk wanda kaji ya na fadin haka, to daman can shi cima zaune ne, irin mutanan nan ne masu ci da siyasa wanda basa aikin fari balle na baki. Amma ina gaya maka gaskiya duk wani mai sana’a yasan an sami ci gaba a wannan gwamnati.  Sannan wannan gwamnati na shinfida ayyuka sosai duk da sun zo a lokacin kudin danye gangan mai ya fadi a kasuwan duniya, domin yanzu fa litar danyen mai bai haura naira 35 ba, ba kamar a lokacin gwamnatin jam’iyyar PDP ba, wanda aka sai da litar danyen mai har naira 150.  Amma duk da haka wannan gwamnati ta jajirce wajen yi ma al’umma aiki babu dare babu rana.

 

A matsayinka na saboda dan jam’iyyar APC, me za ka iya cewa game da takun sakar dake tsakanin El-Rufai da Sanata Shehu Sani akan maganar ciwo bashi?

Wallahi maganar gaskiya ni ne mutumi na farko wanda na fara rubuta wasika na aika zuwa ga chiyam na kwamitin majalisar Dattawa akan abin da ya shafi ciwo bashi, domin yin roko akan ya sa hannu domin a baiwa gwamnatin Kaduna dama ta sami wannan kudi, domin duk wani dan kasuwa wanda yasan abin da ya ke yi yanason ganin an ciwo wannan ba shi.  Domin wannan bashi shi ne zai bayar da daman samun kudin biyan ‘yan kwangila wanda suka yi ma gwamnati aiki. Sannan kudade su shiga hannu manoma da kananan ‘yan kasuwa.   Amma duk wanda kaji suna ihu akan cewar  ka da a amso wannan bashi,  wallahi mutane ne wanda basu san abin da su ke yi ba, kuma wanda ba sa son ci gaba al’ummar Jihar Kaduna.

 

Baka tunin cewar al’ummar za su yi zargin kila dawowarka jam’iyyar APC bai rasa nasaba da kila kanaso ne ka tsaya takarar neman wani mukami?

Ai zargi ka ce, ni kuma bana aiki da zargi.  Domin Annabi (SAW), ya ce, ka yi ma dan uwanka kyakkyawar zato na alheri ba zargi ba.  Sannan mu duk inda al’umma suke nan muke. Domin al’umma sune mutum, kuma darajar su muke ci a kullum. Saboda haka idan har al’umma suka bukacemu da mu tsaya takara za mu tsaya, domin don kyautata musu muke siyasa, ba domin aljihunmu ba.  Saboda yanzu na lura da cewar mutane sun fara dafifin neman takarar kujerar Kanana Hukumomi saboda sun ji za’a sakar ma Kananan Hukumomi ragamar tafiyar da kudadensu kai tsaye.

Wallahi inaso na kara tunatar da mutane akan su ji tsoron Allah, su kwana da sanin cewar duk wanda ya ci kwabon al’umma ba bisa ka’ida ba, wallahi sai Allah ya tambaye shi.  Sannan kowa ya kwana da sanin cewar sai ya tsaya a gaban Allah ya yi bayanin yadda ya tafiyar da dukiyar al’umma.

Daga karshe ina kira ga al’ummar mu cewar da yardar Allah nan ba da jimawa ba, mai girma Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osubanjo, shi ne da kansa zai zo ya amshe mu zuwa jam’iyyar APC ni da mutane na akalla 500, idan Allah ya kai mu.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: