Connect with us

RAHOTANNI

ICPC Ta Cafke Tsohon Alhali Kan Wawure Milyan 220

Published

on

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, da Khalid Idris Doya

 

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da (ICPC) ta shaida cewar ta kame gami da cafko toshon Alkalin Babban Kotu a jihar Kano, Mai shari’a Kabiru Auta kan zarginsa da yaudara da kuma damfara gami da yin sama da fadi da zunzurutun kudi har naira miliyan  dari biyu da ashirin N220.

Bayanin kamen na tsohon alkalin na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga hukumr ICPC wacce Kakakinta Mrs Rasheedat Okoduwa ta rattaba wa hanu gami da rabawa ga manema labaru a ranar larabar da ta gabata.

Okoduwa ta ce wanda suke zargin dai sun tsare sa ne a ranar talata bayan da ya amsa koron gayyatar da hukumarsu ta aikesa masa kan zarginsa da aikata cin hanci da amsar rashawa gami da yaudara da kuma aikata laifin yin amfani da jabun hanya don samun ya damfari wani.

Kamar yanda ta shaida, shi dai wanda suke zargin wato mai shari’a Auta suna zarginsa da ne da kulla makirci da hada kai da shi da wasu mutane domin yaudari wani dan kasuwa mai suna Alhaji Bashir Yakasai kudi har naira miliyan N220.

“Bayan da muka samu labarin lamarin, mun sanar da hukumar shari’a ta kasa inda aka kafa kwamiti domin zurfafa bincike kan lamari na zargin da ake yi wa tsohon mai shari’an”. Ta cikin sanarwar

“Kudin da Alkali Auta da abokinsa Bashir Sufi suka amsa daga hanun Alhaji Yakasai sun yaudaresa da cewar suna aiki a madadin tsohon babban alkalin Nijeriya Hon. Justice Aloma Mukhtar, inda suka samu nasarar amsar kudin daga hanunsa ta wannan barauniyar hanya na yin karyan”. In ji Rashidat

Ta ci gaba da bayyana cewar “Auta ya shaida wa hukumarmu cewar ya maida wa Yakasai miliyan ashirin 20 daga ciin kudin da ya amsa a hanunsa baya da lamarin ta tashi masa”. Ta shaida

Rashidat Okoduwa sai ta bayyana cewar wanda suka kamen sun sakesa a bisa sharadin beli za su ci gaba da zafafa bincie a kansa da kuma zargin da ke malale a duwawunsa domin yin abun da ya dace.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: