Connect with us

KIWON LAFIYA

Likitoci Sun Yi Taron Karin llimi Dangane Da Cutar Kanjamau A Bauchi

Published

on

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Likitocin al’umma na yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya sun gudanar da wani babban taron kara wa juna ilimi, da kuma koyar da junansu ilimi, fasaha domin kyautata aiki da kuma fuskantar babbar matsalar nan ta cuta mai karya garkuwar jiki wato (HIB) domin samar da hanyoyin, rage kamuwa da irin wannan cutar da ke hanzarin nakasar da bil-adama.

Masana da kuma gogaggun likitoci sun shaida cewar cutar na cigaba da fadada a tsakanin jama’a, don haka suka ga dacewar su hadu, domin nema wa al’ummominsu mafita ta fuskacin samar da hanyoyin raguwa da kamuwa da cutar, da kuma hanyoyin taimaka don shawo kan illar da cutar, ke yi. Masanan sun sahale cewar ta fuskacin koyar da likitocin al’umma sabbin ilimi ne kawai zai kai su ga samun hakikanin nasarar da suke son cimmawa.

Wudi Agwani Abubakar, shugaba mai kula da kiwon lafiya  matakin farko na kwarraun likitocin al’umma, masu ba da horo na musamman wa likitoci ,ta yarda za su samu aiki cikin a ma’aikatu, ya yi karin haske kan taron “wannan taron mukan shirya ne a ko wace shekara, duk inda aka ce maka kwararru dole ne kowace shekara, sai sun sake zama da jama’arsu domin bayyana masu sababbin ilimi kan lafiya. Cutattuka na da sukan iya dawowa, da kuma cututtukan da suka zo sababbi, don haka idan muka zo irin wannan taron ne sai mu koyar da ilimin yanda za a shawo kan irin wadannan matsalolin da suke addabar ko kuma barazana ga lafiyar jama’a a daidai wannan lokacin da shekarar ta zo dai dai.

Wudi Agwani Abubakar ya bayyana cewar a wannan taronsu na kwararru na wannan shekarar 2017 sun maida ne gaba daya akan cutar kanjamau “a wannan shekarar mun maida hankali ne kan cutar kanjamau HIB domin a kowace shekara mun fahimci abi gaba yake yi baya cin baya. Jami’an da suke kula da cutar ganjamau sune suka samu likitocin al’umma suka  ce lallai za su zo su sake inganta mana ilimi da kuma hanyoyin da za mu bi wajen kula da masu irin wannan cutar, ga kuma hanyoyin da likitocin al’umma za su bi wajen canza masu cutar fiye, da wajen da muke basu kuwa, domin ganin dai cutar nan ta karu ko kuma ta ragu a cikin al’umma”. A cewar Kwararren

Wudi Agwani ya bayyana cewar babban abinda  suke son su cimmawa  shi ne “lallai ma’aikatan kiwon lafiya mataki na farko, mu tabbatar mun kara wa juna ilimi, idan babu karin ilimi gaskiya wata rana zai zama suna yin kwaba ne a maimakon su yi aikin da bai dace ba, ko kuma ilimi ta yi masu gaba su kuma sai su zama suna tafiya a kan tsohon saninsu, don haka muna son mu cimmar da burin samar da ilimin zamani a tsakaninmu. Idan mutum baida kwarewa gaskiya ba ma za mu bashi takardar shaidai ci gaba da aiki ba, dole ne mu ke duba yanayin ilimin zamani”. A cewarsa

“Dalilinmu na zabar cutar Kwanjamau a da baya cutar ta ragu amma yanzu kuma abun ya sake dawowa, dalili kuma shine babu ma’aikatan da suka san hanyoyin da za su shawo kan matsalar, musamman a karkara, wannan dalilin ne ma ya sanya masana suka zo suka tilasta sai mun amshi wannan matakin”. Ya shaida

Shi kuma mai martaba Sarkin Dass Alhaji Bilyaminu Usman ya jinjina wa matakin ne, sai ya bayyana cewar Kwararrun likitocin al’umma suna da gaggarumin rawar takawa wajen cigaban jama’a a bisa haka ne ya nemi hadin kansu don inganta aikin. Sarkin ya yaba sosai da matakin shawo kan hauhawar cutar Kanjamau, sai kuma ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga jama’a da suke basu hadin kai domin samun nasarar tallafa ta fuskacin rage kamuwa da cutar.

Sarkin ya yi mafani da wannan damar wajen yin kira ga gwamnati da ta kansance a kowan lokaci wajen taimaka wa su wadannan kwararrun likitocin al’umman yana mai cewar ta hanyar tallafa musu ne za su samu nasarar taimaka wa jama’a musamman tun daga matakin farko. Sarkin ya bukaci gwamnatin da ya samar karin malamai da kuma kwararun likitocin domin haka ta kia ga cimma ruwa.

Taron wanda ya gudana a cikin makon nan, kimanin kwararrun likitocin al’umma su 500 ne daga yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya suka samu wannan likimin kan dabarun taimaka wa domin yakar cutar HIB, taron dai sun yi ne a dakin taro na DEC.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: