Connect with us

SIYASA

Na Yi Nadamar Yakin Neman Zaben el-Rufai – Sanata Hunkuyi

Published

on

SANATA SULEIMAN OTHMAN HUNKUYI, shi ne ke wakiltar mazabar Kaduna Ta Arewa Majalisar Dattawa, a wannan tattaunawa da ya yi da MUBARAK UMAR, Sanata ya yi fashin baki kan takardar da aikewa masu rike da masarautun gargajiya a Kaduna, inda yak enema afuwarsu kan rawar da ya taka a zaben Gwamna Malam Nasiru el-Rufa’i.

Akwai takardar da ka fitar inda kake bawa masu rike da masarautun gargajiya hakurin kan rawar da kuka taka na zabar gwamnatin el-Rufa’I, shi wane karin haske z aka yi?

To alhamdulillahi, a nan maganganu guda biyu; na daya na jagoranci dukkan karakainar da aka yi wajen jawo hankali jama’ar jihar Kaduna, matasa maza da mata, ‘yan kasuwa, masarautu da sauran jama’a, su zabi Malam Nasir el-Rufa’i domin mua tsammanin zai jagoranci gwamnati a jihar Kaduna bisa adalci, ta yadda jama’a za su samu ci gaba da karuwar arziki fiye da gwamnatin da ta shude.

Na biyu, an wayi gari na yarda dan Adam ajizi ne, abin da na hanga ko na yi tsammani, wannan gwamanati karkashin Malam Nasir el-Rufa’i za ta yi na adalci na gudanarwa na sauraron jama’a ba ta kai bantenta ba, wanda a tunanina abinda na ji, da wanda na gani, da wanda na yi tuntube da shi, na yarda gwamnati ta bi wata hanya daban, ba ainihin hanyar da aka taho a kai ba.

To wadannan su ne dalilai guda biyu, a matsayina na wanda ya ga abinda yau yake faruwa, na ga ya zama wajibi tilas, ba mun yi da nufi ba ne, tsammani ne, sani ne wanda muke ganin mun yi wa shi gwamna na abinda muka san shi ajiya zai aiwatar, sai muka ga abin ya sha bamban da tunaninmu, kuma mutane ba su ji dadi ba, na yarda na gamsu cewa tabbas ba a kyauta min ba.

Don haka wannan takarda da kake cewa ka gani, takarda ce kashi biyu na abinda ya shafi masarautu. An wayi gari gwamnatin jihar Kaduna ta rushe dukkanin gundumomi da suke karkashin wadannan Hakimai, ta kuma rushe dukkan Hakiman, ta kuma kori dukkan Hakiman, ta kuma kori dukkan ma’aikatan dake karkashin wadannan Hakiman. Haka nan kuma ta kori dukkanin Dagatai da ma’aikatan da suke aiki a karkashin wadannan Dagatai.

Wannan a nawa ra’ayin da abinda na san Jihar Kaduna na ciki, na gamsu ba a yi wa wadannan masarautu da Dagatai da ma’aikatansu adalci ba, ba a yi wa al’ummar jihar Kaduna adalci ba, ba ai amfani da hankali da lura akan menene musabbabin kirkiraro wadannan gundumomi da gwamnatocin jihar Kaduna na baya suka yi ba, a matsayinsu na wakilai kuma shugabanni na jama’a.

Don haka nan na ga ya dace duk da ba ni ke dauka ko in kora ba, ba kuma za a yi shawara da mu ba, ba kuma za a yarda idan mun ba da shawara a yi aiki da ita ba. Ina ganin mafi kankantar abin da ya kamata in yi a matsayina na wanda na yi tallan nan kuma aka saya shi ne in koma wa jama’a in ba su hakuri akan abinda ake tsammanin nan wanda a yau ya sha bamban da ake aiwatarwa, wannan ina jin shi ne bayani mafi kankanta da zan yi maka.

A cikn takardun da muka aika har wa yau akwai takardu da na aika wa  shugabannin ‘yan Kwadago na jihar Kaduna, shugaban Malaman Makarantu na jihar Kaduna, shugaban ‘yan kwadago na kasa reshen jihar Kaduna, shugaban ma’aikatan kananan Hukumomi na jihar Kaduna, shugaban ‘yan jarida da gidajen rediyo da talabijin na jihar Kaduna, da shugaban TUC, wato manyan ma’aikata da suke jihar Kaduna, wato duk wadannan rukuni guda biyar, akwai abinda gwamnatin jihar Kaduna ta aiwatar a kansu da ma’aikatan da suke karkashinsu wanda yake rashin adalci ne.

Abinda ya shafi ‘yan jaridu ni ina tsaye aka yi, aka kawo wadada ba su mallaki hankalin kansu ba, aka kawo wadanda sai da aka tabbatar an rabaa su da hankalinsu, muna cikin wurin nan  aka kawo su aka juye suka dauki makamai munana suka farfasa motocin mutane, aka farfasa wannan gida na NUJ, aka yayyanki wadansu, aka sassari wadansu, sannan aka koma aka ce wai mune muka zo da wadannan mutane.

Da muka nemi wakilan ‘yan jaridu a lokacin da ake Kamfe, a cire waccan gwamnatin ta PDP, daga cikin abubuwan da mu kai masu bajakoli a gabansu shi ne, waccan gwamnatin ta PDP tabbas ba ta da da’a kuma ba ta yi wa jama’a Jihar Kaduna da’a ba. To sai kuma ga wannan, ka ga ya zama wajibi ni da nake shugaban tallan wannan gwaamnati in durkusa in cewa shugabannin ‘yan jaridar nan, ku yi hakuri, ka kan haifi mutum ba ka haifi halinsa ba.

Mun tabbatar abinda mu kai tsammani ba shi muka tarar ba, saboda Allah da ya halicce mu, akan wayi gari wasu su farraka su bijire masa, don a yau idan mun zo wanda muke jin zai jagoranci gwamnati, kuma ya bijire wa jama’a, to mu da muka zo wannan gwamnati wajibi ne mu fuskanci jama’a mu roke su su yafe mana, wallahi ba mu yi da niyya ko nufi ko sani ba. Mun yi cikin kuskure, kuma kuskuren nan an hadu da shi don haka nan a yafe mana a yi hakuri, wannan a takaice shi ne bayani na.

 

Kuna cikin APC kuma duk wanda yake nazartar al’amuran siyasar Nijeriya ya kwana da sanin rikicin cikin gida da ke damun jam’iyyarku, musamman a Kaduna, baka ganin wannan zai taba ku a daidai lokacin da ake tunkarar zaben 2019?

To ai rikici a harkar jam’iyya wani lokaci ya kan zama gishiri, shi kuma gishiri ka sani a miya in yayi yawa ya kan hana miyar ta ciwu, don haka rikici ba ya hana jam’iyya ta kai bantenta. Kin gaskiya shi ke batar da zare da allura ya kasa dinki, don haka maganar rikici, idan jama’a suka gane, su waye masu rikicin mene hujjar rikcin? Shi ya sa muke kira ga jama’a su duba su san mai sonsu, su san mai gaskiya, a bar kuri’a a hannun talaka ya kada abarsa.

Wannan shi ne kiran da na yi satin da ya wuce cewa, Shugaban kasa na yau Muhammadu Buhari ba zai gina hanyar da wani Shugaban kasa bai taba gina wa ba, ba zai je ya yi wani Dam da wani Shugaban kasa bai taba yin irinsa ba, ba za aje a yi jirgi wadda wani bai taba yin irin sa ba. Abinda muka san Shugaban kasa zai yi wanda zai bari a baya, muddin yana da rai a ga yayi kama da shi shi ne, dukkan wani abu da ya shafi murdiya ta hanyar zabe shugaban kasa ya toshe shi duk wanda ba a yarda da shi ba a kyale shi jama’a su kwada shi da kasa. Ta hanyar kuri’a ko fidda gwani na jam’iyya, ko na zabe na gari wanda Hukumar gudanar da zabe take yi. Abinda Buhari zai biya talakan Nijeriya da shi Kenan. Goro na gwagwarmaya wanda talakan Nijeriya yayi don ya tsaya masa a matsayinsa na mai gaskiya wanda ake sa ran zai jagoranci jama’ar Nijeriya cikin adalci.

Rashin yin wannan ko rashin samar da wannan a ganina shi ne rashin kai banten gwamnatin kuma rashin kai banten APC, kullum muna gaya masu abinda ya kashe PDP, a kaucewa gaskiya, kuma yawan mutane su ne kasuwa ba rumfuna ba.

 

Kai da takwaranka Sanata Sheshu Sani ta bayyana kuna adawa da wannan gwamnati, mu dauka yanzu el’Rufa’i ya tsallake zaben fidda gwani, shin za ku hadu ku goya masa baya a tafi tare ko kuwa?

To ka raba magana daya ta zama biyu, na farko ba na fada da Malam Nasiru, amma ina fada da akidar da ya zo da ita, saboda ni a matsayina na dan siyasa shekara kusan talatin ina harkar nan, zama lafiya da jama’a shi ne ya fi komai muhimmanci ga dan siyasa, idan abu ya taso wajibi a taushi jama’a. Shi ne mulkin Dimukaradiyya, ita ce ma’anar Dimokaradiyya.

Abinda nake karanta maka yau ganina da Malam Nasir na karshe na karanta masa wannan, cewa idan ya saki hanyar gaskiya aka yi abinda bai shafi jama’a ba, aka saki hanyar da jama’a suke bukata, to anan za a raba hanya da ni. Na biyu a wannan yanayi da nake gaya maka ni Hunkuyi, shugabanni da jama’ar jihar Kaduna ba za su layi su sake zaben Nasir el’Rufa’i ba, ni na gaya maka, ba duba nake ba, fassara nake maka, saboda karatun a rubuce yake.

To an saki jama’a, an bata da jama’a, an muzguna wa jama’a, an nuna masu ba su isa ba, an nuna masu abinda gwamnati za ta yi ko sun yarda ko ba su yarda ba, ko suna so, ko ba sa so haka za a yi. Hanya ta riga ta fandare, sun nufi daji sun bar jama’a a gari. Babu yadda za a yi a shiga layi dan jam’iyyar APC mai kati, ba tursasawa ba karya a mika mashi Tikitinshi na zabe a kada kuri’a a jihar Kaduna. ‘Ya’yan jam’iyyar APC su zabi Nasir el-Rufa’i yanzu baza ta yiwu ba.

 

Me za ka ce game da yunkurin gwamnati na korar Malaman Makaranta furamare da suka kasa cin jarabawa?

Ai tuni na bayyana ra’ayina akan wannan, ni Malamin Makaranta ne, na san abinda ya kamata akan ma’aikaci wanda yake karantarwa, daya daga cikin abin ya kamata Malami ya yi shi ne, ya koya ya iya tsarin yadda zai gudanar da darasinsa ga dalilibansa. Daga cikin abin ya wajabta akan hukumar daukar Malamai na Firamare ko na gaba da Firamare, wadda gwamnatin jihar Kaduna ke jagoranta shi ne, ta biya shi hakkinsa na albashinsa, idan fansho ya zo ta biya shi.

Akwai Malaman da sun fi shekara ashirin suna aiki da hukumar ba a taba yi masu bita ko ba su horo ba. Me ya sa ba a yi ba? Me ya sa ba za a yi ba, har ake kokarin dauko wasu sababbin Malamai daga wasu wurare? Malamin da ya koya min karatu har yau yana nan a Zariya, ya karantar da ni na kuma na karu matuka da bin da ya karantar da ni.

Duk duniya babu inda Hunkuyi bai taka ba, wannan din nan da ake ganin bai kware ba, ko ba kowa bane ba, don haka nan wadanda ake shirin korar nan ‘yan jihar Kaduna ne, suna da hakki akan gwamnatin jihar Kaduna da kuma hukumar gudanar da ayyukan nan, lallai ta fitar da kudi ta ba su horo, domin su ci gaba da gudanar da abinda ya kamata su gudanar. Tun dai wadannan din da ake shiri daukar su ma jami’a ko kwalejojin da wadanca suka yi, su ma ita suka yi.

Ba fa lallai ne mai mulki shi zai ce ga yadda yake so ba, a’a, wadanda ake mulka ne za su zabi abinda suke so. Sai a duba tsakanin biyun a gyara, wannan shi ne abinda ya wajabta ko wane shugaba yayi ke nan, tare da fatan Allah ya gyara mana.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: