Connect with us

RAHOTANNI

PDP A Nasarawa Ta Maka Gwamna Al-Makura A Kotu

Published

on

Daga Zubairu T. M. Lawal Lafia

Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Nasarawa ta maka Gwamnatin Umar Tanko Al-makura gaban kuliya.

A jiya juma’a ne jam’iyyar ta PDP ta tattara takardunta ta shigar da kara ta hannun Lauya Ucha Ulegele a babban kotun garin Lafia.

Da yake zantawa da manema labarai, lauyan masu kara Barista Ucha Ulegele ya ce, sun shigar da wannan karar ne saboda suna bukatar kotu da ta dakatar da Gwamna Umar Tanko Al-makura kan kudurinsa na sayar da kadarorin Gwamnati dake wasu jihohi har ma da na cikin gida.

Ya ce; “wadannan kayayaki an gaje su ne ta hanyoyi daban-daban kama daga tsohowar Jihar Binuwai-Filato da kuma Jihar Filato, wanda mallakinta ne na kashin kanta, kuma shekara da shekaru jihar tana amfana da su babu wani Shugaban da ya yi sha’awar sayar da wadannan kadarorin. Amma zuwan Gwamnatin Al-Makura tana bukatar ta maida hannun agogo baya ta yadda jihar za ta kasance cikin talauci.”

Barista Ucha Ulegele ya ce; “al’ummar Jihar Nasarawa ba su goyi bayan wannan kudurin ba. Duk da cewa Gwamna Al-makura ya yi amfani da ‘yan majalisar dokokin jihar saboda ya cimma burinsa. Amma suma ‘yan majalisar ba su yi amfani da kwarewarsu ba saboda an ba su abu a dunkule su kuma sun amince ba tare da sun tuntubi al’ummarsu ba.

Ya kara da cewa; “sayar da wadannan kadarorin babu abin da zai amfanarwa Jihar Nasarawa face talauci ga ‘yan baya masu zuwa zasu gada. Filayen da Jihar take gadara da su da kaddarorin da suke wasu jihohi idan aka sayar to jihar ta fada kangin talauci.

Ya ce; kowa ya san Jihar lagos jiha ce ta kasuwancin kasa da kasa, idan ba ka da komai a kasuwa da me za ka yi tinkaho. Kuma kowa ya san Kaduna jiha ce da ake tinkaho da ita masamman jihihon Arewa, idan baka da komai ai ka zama cima baya. Kuma Jihar Fiilato da muke makotaka da su a ce yaranmu idan suka taso ba za su tarar da komai na Jihar Nasarawa wanda ta gada daga Jihar Fiilato ba?

Ya ce; “hakan bai da ce ba, shi ya sanya muka shigar da kara gaban kuliya saboda kotu ta dakatar da shi dangane da wannan shirin mara amfani wanda al’umman jihar ba su yarda ba. Kuma kotu ta amince da karbar karar inda za’a fara zaman farko a ranar 27/11/2017.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: