Connect with us

SIYASA

Shugabanci PDP: Mun Yaba Da Kokarin Sanata Makarfi —Dingyadi

Published

on

Daga Bello Hamza, Kaduna

Matasan jam’iyyar PDP sun yaba da kokarin da shugabannin jam’iyyar suka yi na tabbatar da an samu fahimtar juna tare da kawo hanyoyin zaman lafiya a jam’iyyar ta hanyar kwamitin shugabancin rikon kwarya, karkashin jagorancin Sanata Ahmed Makarfi a haduwar da dukkan ‘yan takarar suka yi a Inugu da Abuja.

Shugaban matasan na Arewa Alhaji Yusuf Abubakar Dingyadi ne ya bayyana haka ranar Alhamis din da ta gabata a Sakkwato.

Ya ce, hukuncin da shugabannnin jam’iyyar da suka hadu a Inugu shi ne, dukkan ‘yantakarar sun yarda da su fahimci juna don a kawo ci gaba a jam’iyyar, a hanyar goya wa dukkan dantakarar da ya samu nasara a zaben da za ayi a watan Disanba. Saboda haka wannan taro na kasa da za a yi wanda shi ne karo na tara ana sa ran ya kawo karshen cece-kucen da aka dade ana yi a jam’iyyar, yadda jam’iyyar za ta samu nasara a zaben 2015,

Saboda haka ya ce ‘yan takarar sun nuna dattako ganin yadda suka zauna suka tattauna, kuma aka samu matsaya, a kan yadda za ciyar da jam’iyyar gaba

Irin wannan tattaunawar da ahugabannin jam’iyyar suka yi da fahimtar junan da suka yi shi zai farfado da jam’iyyar ta PDP yadda za ta fuskanci kalubalen zabe mai zuwa.

Shugaban matasan ya bayyana cewa, jam’iyyar ta samu karin mtunci da ci gaba sakamakon kokarin da shugaban kwamitin rikon kwaryar ahmed Makarfi yay i, tun lokacin da ya hau.

Saboda haka matasan sun shawarci shugabannin jam’iyyar da su yi watsi da maganganun da ake yi a kafafen watsa labarai wadanda ka iya kawo sabanin fahimta a tsakaninsu

Shugaban kungiyar matasan na PDP din sun cewa, dole ne su ma a tsakaninsu su kawar da son rai, yadda jam’iyyar za ta kara samun karbuwa cikin al’ummar kasa baki daya.

A karshe, ya ce, ya yi kira da babbar murya kan matasan su fahimci cewa, akwai wadanda ake bas u kudi domin su haifar da abin da zai kawo sabani a tsakanin ‘yan jam’iyyar, saboda sai su kiyaye kada su fada tarkon irin wadannan mutane.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: