Connect with us

MAKALAR YAU

Me Ya Kawo Lalacewar Ilimi A Arewacin Kasar Nan? II

Published

on


08148507210   [email protected]

Idan dai ana biye da mu, muna magana ne game da yadda harkar ilimi ta lalace a kasar nan, musamman a nan Arewaci, wanda da ma can Kudanci sun yi mana fintinkayu a fannin.

Muna magana ne kan cewa lalacewar ba ta rasa nasaba da yadda aka yi watsi da Kwalejojin koyon aikin Malanta, TEACHERS COLLEGES, da kuma manyan Kwalejojin horar da Malamai COLLEGES OF EDUCATION, wadanda a yanzu haka wasu jihohin ma sam kamar ba a taba yinsu ba, wasu jihohin kuma an rage an bar ’yan kadan.

A zamanin da, a irin wadannan Kwalejoji ne ake horar da Malaman da ke shiga ajujuwa suna koyar da dalibai, wanda kuma ba za a taba samun irin abin kunyar da ke faruwa a yanzu ba, ta yadda za a ce Malami ya kasa cin jarabawar dalibinsa.

Garabasar da ake samu a irin wadannan Makarantu na Horon Malami ba ta wuce yaro tun yana dan karami yake tashi da akidar koyarwa a zuciyarsa, an sa masa ita , a cikin hikima zai kuma tashi yana ganin muhimmanci da kuma girmamata, ya tashi yana alfahari da hakan.

A da shekaru biyar dalibi ke yi a Makarantar, ana koya masa yadda zai fuskanci aikin koyarwa. Bayan ya kammala wani ya kan fara aikin koyarwa, kafin ya wuce abin da ake kira Adbance Teachers College, nan kuma ya yi shekaru uku, bayan haka ya fito da takardar shaidar NCE, daga nan kuma sai Jami’a inda zai karanta Bachelor of Education. Saboda duk wanda ya bi wadannan hanyoyi, ya za a yi same shi da wani nakasu a harkar koyarwa? Kuma yanzu a bincika a gani wane Malami ne ya bi wadannan hanyoyi kafin ya shiga aji?

Yanzu abinda ke a kasa ta hanyar koyarawa shi ne sai dalibi ya kammala Sakantare , daga nan ya je zuwa College of Education idan mai sha’awar koyarwar ne, ya yi shekaru uku ya samu NCE. Ai idan aka ce da wanda ya bi tsarin irin na da , da kuma na yanzu su kama aikin koyarwa, ai wanda ya bi ta dogon zango dalibai za su fi saurin fahimtar abubuan da yake koya masu.

Saboda haka ne na ke ganin cewa lallai akwai jan aiki a gaban Shugabanninmu, musamman Gwamnoni, wadanda su ne ke da wuka da nama a jihohinsu, su tashi tsaye wajen sun dawo wa da wannan harkar mai matukar muhimmanci martabarta.

Domin abin ya faru a Kaduna, lallai za mu iya cewa Malam Nasiru ya fasa kwai, domin na tabbata ba a jihar Kaduna ne kawai irin wadannan abubuwa ke faruwa ba, sauran jihohin ma suna ciki tsundum.

Kamar yadda aka sani, bayan da gwamnatin ta Kaduna ta yi wannan bincike da jarabawa, ta dauki matakin hukunta wadanda suka fadi jarabawar, an fito ana ta kalunlantarta, musamman kungiyar Malaman ta NUT. Ba mu san me wannan yake nufi ba, a bari wadanda ba su kware ba su gaba ci gaba koyarwar, ko kuwa?

Haka kuma baya ga sakacin da gwamnatocinmu suka yi na bari Kwalejojin horar Malamai su mutu, haka ma wata Kwalejin mai muhimmanci ita ma an bar ta, wato Kwalejojin koyon sana’o’i, TECHNICAL SCHOOLS.

Misali a nan Arewa akwai irin su Gobernment Technical Secondary School a jihar Katsina yanzu a Mashi cikin Karamar Hukumar Mashi. Sai kuma ta Soba a Karamar Hukumar Soba ta jihar Kaduna, da akwai kuma daya a Kano, wace ake kira da Technical College, suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da kwararru.

Kuma wani abin burgewa, irin daliban da suka yi wadannan Makarantu tun a can ake koya masu sana’o’i daban-daban, wadanda ko da ba su samu wucewa Makarantu ba, suna dai da sana’aa hannunsu, ba sai sun jira gwamnati ta samar masu da ayyukan yi ba, su ma suna iya dogaro da kansu, har ma wasu su zo wurinsu su koya.

Sana’o’in da ake koyarwa a matsayin darussa, sun hada da Technical Drawing, Building, Woodwork, Metal work, Carpentary, Electrical da Electronic, Plumbing da dai sauran makamantansu.

Saboda haka yanzu ashe dawo da ire-iren wadannan Makarantu na musamman ai ba karamin alheri ba ne a kasa, ba ma kamar halin da ake ciki yanzu na yadda gwamnatoci ba su iya samar wa wadanda suka kammala makarantu da ayyukan yi ba.

Haka kuma wani abu da shi ma ya taimaka wajen jefa harkar ilimi a halin da yake ciki, shi ne tun lokacin da aka bullo da Makarantun Jeka-Ka-dawo, wacce aka fi sani da ‘Day Schools,’ wanda aka fake da wai matsalar kudi ce ta sa haka, to amma daga baya kowa ya ga irin ci-bayan da aka samu, maimakon ci gaba, musamkman ta bangaren tarbiyyar da ake koya a irin wadannan Makarantun Kwana da irin ilmin da ake samu a can.

Saboda haka lallai akwai bukatar a sake duba wadannan muhuimman abubuwa, wadanda su ne ginshikan da suka taimaka wajen lalacewar ilimi a wannan yanki, kuma lallai tabbaci hakika dawo da su zai taimaka wajen dawo da martabar ilimin.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI