Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Za Mu Yi Kokarin Shawo Kan Matsalar Cin Zarafin Mata – NAWOJ

Published

on


Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

A jiya Asabar ne kungiyar mata ‘yan jarida reshen (NAWOJ) suka gudanar da wani taronsu na shekara-shekara domin tattauna yanda za a kawo karshen cin zarafin mata da kuma yara mata a duniya a cikin bikin yaki da cin zarafin mata. masana da kuma masu ilimi a fannoni daban-daban ne suka tattauna gami da bayyana matsalolin da mata da kuma kananan mataye ke fuskanta. Taron ya guda na ne a karafin dakin taro na cibiyar ‘yan jarida da ke Bauchi (NUJ).

Wakilinmu da ya kasance a wajen ya bayyana mana cewar taron na bana kan “Cin Zarafin Mata” ya karkata ne kan cin zarafin mata musamman na fyade da kuma yawaita keta musu haddi wanda a cewan masana hakan na lalata wa mata da kuma al’umma rayuwarsu ta gaba.

Da take mana karin bayani kan halin da suke ciki da kuma hanyoyin da ‘yan jarida mata za su bi domin shawo kan matsalolin da mata ke fuskanta ko kuma rage hauhuwar matsalar, shugaban kungiyar mata ‘yan jarida reshen jihar Bauchi Bulak Afsa ta bayyana cewar a shirye suke ci kara jan damara domin fadakar da jama’a illolin lalata mata musamman yara kanana “mun shirya wannan taron ne domin mu fadakar da mataye kan wannan matsalar na cin zarafin mataye, mun fahimci cewar akwai abubuwa da dama da suke jawo cin zarafin mata. Su al’umma suna da nasu laifin, su ma matan suna da nasu laifin, maza da gwamnati kona na da hakkin da ya dace ya sauke don haka muna fadakar don ganin an samu al’umma ta gari, mata da yara Allah ya yi kowa da girmans, ba daidai bane a tura yaro makaranta a hana mace zuwa ba. idan ka kai matarka asibiti kana son macece ta duba matarka ko kannuwarka, ta yaya ne idan mace bata ce makaranta ba ta yaya ne za ta zama likita? Harta zo ta taimaki al’umma don haka ina ganin dole ne maza mu ji a ranmu yanda za a ka tura mace karatu haka ita ma mace za ak turata”. A cewar shugaban NAWOJ.

Misis Bulak Afsa ta ci gaba da ce, a matsayinsu na ‘yan jarida mata, za su ci gaba da lalubo bakin zaren shawo kan matsalolin mata da kuma kalubalen da suke fuskanta a cikin al’umma “a matsayinmu na mata ‘yan jarida mun himmatu wajen fadakar da jama’a mazanne da kuma matayen, don haka za mu ci gaba da fadi tashin shawo kan matsalolin da suke akwai”. A cewarta.

Shugaban ta NAWOJ, Bulak Afsa ta bayyana cewar a kowani lokaci za su ci gaba da yin amfani da damarsu na kasancewa ‘yan jarida wajen nemo hanyoyin taimaka wa ‘yan uwansu mata da kuma lalubo bakin zaren shawo kan matsalolin fyade da kuma rashin tura yara makaranta, haka matsalar nan na nuna fifiko a kan ‘ya mace shima za su yi kokarin fadakar da iyaye maza domin ganin an samu waraka da kuma raguwar matsalolin. Kamar yanda ta shaida.

Babban mai shari’a a kotun majistiri da ke Bauchi ‘CMC 12’ Safiya Musa ita c eta gabatar da makala kan cin zarafin mata a cikin al’umma ta bayyana cewa “gaskiya ‘ya’ya mata suna cikin wani hali na ha-u-la-I, saboda duk inda mace ta samu kanta tana cikin damuwa, a cikin gida mace bata tsira ba idan aka yi rashin dace wasu ‘yan gidan ke aikata ashsha, wasu lotukan kuma makwafta, muna gani a kotu kodayaushe kuma muna shari’un nan, sai ka ga an kawo tsoho dan shekara 60 ya wulakanta mace ‘yar shekara 9. Haka  a waje mace bata tsira ba, a hukumance ma mace bata huta ba sai ka ga kamar yanzu lokaci na gudun jihira, inda aka killace mata nan ma sai ka samu ana yi wa mata fyade gwamnati bata tsaya da kyau ta kai abinci yanda ya kamata ba, sai ka ga wani ya samu mace ya ce mata ki bani jikinki na baki abinci, bakin cikinmu an ki a dau matakin da suka dace”. A cewar mai shari’ar.

Ta bayyana cewar fadakarwa da kuma wayar da kan jama’a na taimakawa, dangane da himmar da kuma matakin da ya dace masu shari’u su dauka, mai shari’ar ta yi kira ga lauyoyi masu zaman kansu da su tashi tsaye domin taimaka wa wadanda ake yi musu fyade “shi hidimar shari’a mu alkalai akwai iyaka huruminmu, wani lokacin zaka ga an samu kes na irin wannan fyade wa macen amma kuma sai a malgwada gaskiyar lamari, wasu wadanda ake yi musu fyaden nan talakawa ne, basu da hurumin daukan lauya, don haka ina kiran ga lauyoyi masu zaman kansu ko kuma lauyoyin da suke aiki na gwamnati suke bada gudunmawarsu wajen kare yaran da aka yi musu irin wannan zalumcin”. In ji ta

Fatima Idris Danjuma, wacce itace wakilin gidan rediyon Dandal Kura ta bayyana wa wakilinmu cewar a matsayinsu na ‘yan jarida mata suna jin zafin matsalolin da ke faruwa na cin zarafin mata da kuma kananan yara, ta bayyana cewar ba daidai bane mazaje suke kauce wa hanya wajen yin lalata da yaran da basu dace ba “ka samu mutum dan shekaru 50-60 ya yi wa yarinya ‘yar shekaru 9 fyade ko ma kasa da haka, gaskiya a matsayinmu na iyaye mata ba za mu lamunci hakan ba, za mu ci gaba da yakar wannan rashin da’ar. Idan fa mutum ya ci zarafin ‘yar wani shi ma zai haifa ko kuma za a haifa masa, wani irin hali ne haka za ka yi irin wanan abun kunyar, gaskiya mu dai a matsayinmu na ‘yan jarida za mu ci gaba da yaki da irin wadannan munanan dabi’un”. In ji ta

Wakilinyar Dandan Kuran ta amsa ma wakinmu tabbatar cewar su ma matan da nasu laifi me za ta ce “eh gaskiya ne kamar yanda ka ce wasu matan suna shigan banza da kuma yin abubuwan da suke jawo hankulan na miji zuwa garesu gaskiya wannan matsalar ita ma muna kokarin shawo kanta ta fuskacin fadakarwa da kuma hawaita yn rahotoninmu kan irin wannan da kuma illolin da hakan ke jawowa a tsakanin al’umma za kuma mu ci gaba da fadakarwa”. In ji Gimbiya Fatima.

Taron na bana, kan yaki da cin zarafin mata a cikin al’umma ya samu halartar masu ruwa da tsaki a harkokin mata da suka hada da ‘yan sanda, cibil Defenses, ma’aikatan sadarwa, manyan matan jihar, bangarorin shari’a da dai sauran matan gari. An tattauna sosai, an kuma bukacin mata ‘yan jarida da su kara himma da azama domin ganin an samu nasarar kawarar da cin zarafin mata musamman matsalar nan na yin fyade da kuma keta haddin mata a cikin al’umma.

Daga cikin matan da suka halarci taron, masu sharhi a wajen wata matar ta bayyana cewar dole ne iyaye su tashi tsaye wajen kula da abubuwan da ‘ya’yenmu mataye ke yi da wayar salula na zamani, a cewarta yanzu ana aikata ashsha sosai ta wayar hanu, ta shawarci iyaye da suke lura da kuma abubuwan da ‘ya’yen nasu ke yi da wayoyin hannu.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI