Fim Din ‘This Is The Way’ Ya Dawo Da Martabar Kallo A Cinema — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

BIDIYO

Fim Din ‘This Is The Way’ Ya Dawo Da Martabar Kallo A Cinema

Published

on


Daga Wakilinmu, Kano

A daidai lokacin da a ke ganin kamar mutane sun fara kauracewa kallon fim da a ke nunawa a Film House Cinema da ke cikin ginin Ado Bayero Mall wanda a ka fi sani da Shoprite a birnin Kano, sai ga shi nuna fim din ‘This Is The Way’, wanda a ka yi shi da harshen Turanci na kamfanin Jammaje Productions, ya zo da wani yanayi na bazata ta fuskar masu halartar kallon, domin kuwa a ranar Juma’a 22 ga Disamba, 2017, da a ka fara nuna fim din sai da ya zamo wajen ya yi cikar da a ka dade ba a ga irinta ba, saboda irin cikar da sinimar ta yi da masu kallo.

Wannan ya sa a satin farko na nuna fim din sai ya zama abin yin muhawara a wajen matasa musamman ma dalibai ’yan gaba da sakandire, domin kuwa fim ne a ka shirya shi a kan rayuwar matasa ta fuskar neman ilimi da kuma illar cin hanci da ta ke damun al’ummarmu. Sannan kuma sai ya zama an yi amfani da shi da harshen turanci wanda duk wani dalibi yana son ya ji ana furta ingantaccen turanci, to sai ya zama fim din This is The Way ya zo da wannan salon.

Wakilinmu ya halarci wajen kallon fim din domin ganewa idonsa yadda yanayin kallon yake gudana inda kuma bayan fitowa daga kallon fim din ya nemi jin ra’ayin masu kallon fim din mai suna Ahmad Rabi’u ya shaida mana cewar, “Gaskiya na karu da kalmom na turanci a wannan fim din domin a matsayina na dalibi fim din zai taimaka min wajen yin amfani da kalmomi da kuma furta shi cikin ka’ida, sannan kuma hannunka mai sanda ne ga mu matasa shi sakon da yake dauke cikin fim din.

Hamisu Lamido Iyantama shi ma ya halarci kallon fim din a lokacin da muka tambaye shi ga abin da ya fada “Na ga fim kuma ya kayatar da ni musaman yadda aka tsara shi da turanci, kuma sakon ya gamsar, domin yadda aka tsara muryar fim din ta fita fiye da na farko da aka yi kuma kyawun hoton ma ya fi na baya da aka yi. Don haka akwai ci gaba da aka samu daga yadda na kalli na farko da na biyu. Sannan shi Daraktan Falalu Dorayi ya yi kokari da ya iya rike masu kallo daga farko har karshen fim din wanda ni kaina ina son na tashi na yi wani uzuri amma na kasa tashi saboda ina bin labarin don na ga karshensa.”

Shi kuma wanda ya shirya fim din Kabiru Musa Jammaje ya yi kokari samar da abin da ake so a fim din. Sannan jaruman sun yi abin a yaba musu ta wajen furta kalmomin turancin yadda mai kallo zai fahimta don haka wannan labarin da aka yi shi da turanci, ina tabbatar maka ko dan firamare ya kallo zai koyi wasu kalmomi na turanci a cikinsa. Don haka fim din ya yi.”

Shi ma furodusa kuma jarumi Musa Abdullahi Sufi cewa ya yi, “Gaskiya wanna fim din ya nuna mana cewar masana’antar finafinai ta Kannywood ta kai wani mataki na ban mamaki, domin yadda tsarin labarin ya tafi da kuma yadda aka yi aikin ina tabbatar maka da cewar ci gaban da muke tunani har ma mun wuce shi. Don mu da muke cikin masana’antar kuma muke yin nazari a kana bin da ake yi wannan alama ce da take ba mu karfin gwiwar cewar nan gaba za mu kai ga burinmu na kaiwa sahun wadanda suka ci gaba da duniya ta fuskar samar da finafinai masu inganci.”

Darakta Yaseen Auwal ma cewa ya yi, “Wannan fim din na This is The Way ya yi kyau sosai, kuma Daraktan ya burge ni domin aikin ya ba da ma’ana yadda ake so sai dai a bangaren isar da sako mai kallo ba zai iya fahimtar sa sosai ba, domin tunda magana ce ta cin kudi da suka yi kuma lauyan da ya fitar da shi ya wulakanta shi a farko, sakon ya yi amma kawai lokaci guda sai ya zo ya fitar da shi saboda kudin jama’ar kasa da ya ci a nan na ce ni dai sakon bai yi min ba, amma a gskiya labarin fim cin ya kayatar farkon sa da karshensa.”

Kamal S. Alkali shi ma Darakta ne. Ga abin da ya ce, “A wannan fim din This is the Way ya dauki numfashina. Tun daga yadda aka fassara labarin da kuma wanda ya tsara shi don lokacin da nake kallo sai na ji ni a matsayin mai kalo ba mai shiryawa ko ba da umarni ba. Kuma wannan hanya ta fito da finafinan Turanci da Kabiru Jammaje ya kawo ta cikin Kannywood wata mahanga ce ga duk wanda zai yi fim din turanci ya zo ya koya a wajen sa. Don haka muna jinjina masa.”

Babban furodusan fim din, Malam Kabiru Musa Jammaje, shi kuma a nasa tsokacin cewa ya yi, “To, duk da cewa ina jin ra’ayoyin masu kallo, amma dayake ba a gama ba, abin da zan iya cewa ana smaun ci gaba, domin ina shiga cikinsu na saje don na ji ra’ayoyinsu daga kuma abin da nake ji suna fada abin yana kara min karfin gwiwa.

“Haka kuma kuma a yadda nake ganin kullum baki suna kara zuwa wajen kallon to ya nuna suna samun labarin da yake gamsar da su kuma bayan nuna fim din da muke yi yanzu a nan Kano, muna sa ran akwai wasu wurare ma da za mu je mu nuna, kuma daga ciki har da kasar Ghana, amma kafin sannan za mu nuna shi a Kaduna da Abuja da Legas, domin gaskiya ba yanzu za mu saki fim din ba, sai mun nuna shi a wurare da yawa a nan da kuma kasashen waje, domin shi fim ne da aka kashe kudi mai yawa don haka idan aka ce za a sake shi akwai masu turawa a waya da kuma masu satar fasaha.

“Ba za su bari ko kudinmu mu dawo da su ba. Don haka za mu yi ta nuna shi har sai mun ga kudinmu ya dawo kafin mu sake shi,” in ji Jammaje.

Advertisement
Click to comment

labarai