Connect with us

WASANNI

Dan Tawaye Ya Zama Mamba A Hukumar Kwallon Kafar Afirka

Published

on

Hukumar kula da kwallon kafa ta Nahiyar Afrika CAF, ta zabi Patrice Edouardo Ngaissona, wani tsohon jagoran mayakan ‘yan tawayen Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, a matsayin memba a kwamitin zartawar ta.

CAF ta cimma wannan matsayar ce, yayin taronta a kasar Morocco a shirye shiryen buga wasan karshe na cin kofin nahiyar Afirka nay an wasan cikin gida tsakanin mai masaukin baki kasar Morocco da kasar Najeriya.

Ngaissona, tsohon minista ne na matasa da wasanni na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, a zamanin gwamnatin Francois Bozize, wanda ake zargi da tallafawa kungiyar ‘yan tawaye ta Anti-Balaka Kiristoci da ke yakar kungiyar ‘yan tawayen Seleka Musulmi da suka kifar da gwamnatin Bozize.

A shekarar 2015, aka haramta mishi tsayawa takarar shgabancin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, saboda zarginsa da ake da aikata laifukan yaki a kasar, zargin da har yanzu yake musantawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!