Connect with us

KASASHEN WAJE

Shugaban Equatorial Guinea Ya Rushe Gwamnatin Da Ya Kafa

Published

on

Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema, ya rushe majalisar zartarwar gwamnatinsa, ciki har da mukamin Firaministan kasar da kuma baki dayan mataimakansa guda 3.

Nan da kwanaki masu zuwa ne ake sa ran shugaban zai sanar da kafa sabuwar gwamnati.

Obiang ya kafa gwamnatin da ya rushe mukamanta ne, a watan Yunin shekarar 2016, bayan lashen zaben shugabancin kasar da ya yi a watan Afrilun shekarar ta 2016 da kashi 93.7 na kuri’un da aka kada.

A watan Nuwamban da ya gabata kuma aka yi zaben ‘yan majalisun kasar da na kananan hukumomi, wanda shi ma jam’iyya mai mulki ta lashe kujerun majalisar kasar 99 daga cikin 100.

Shugaba Theodoro Obiang wanda ya ke mulkin Ekuatorial Guinea tun daga shekarar 1979, yana fsukantar suka bisa zargin dankwafe ‘yan adawa, tafka magudin zabe da kuma cin hanci da rashawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!