Connect with us

WASANNI

Yanzu Na Fara Jin Dadin Kwallon Kafa, In Ji Batchuayi

Published

on

Dan wasan Chelsea, Michy Batshuayi ya ci kwallaye biyu a wasan farko da ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund a gasar Bundesliga da ta je ta ci FC Koln 3-2 a karshen satin nan..

Batshuayi wande ke buga wa Dortmund wasanni aro ya ci kwallon farko tun kafin aje hutu, bayan da aka dawo ya kara kwallo ta biyu.

Simon Ziller da Jorge Mere ne suka ci wa Koln kwallayen ta, daga baya Batshuayi ya bai wa Andre Schurrle kwallon da ya ci na uku a karawar.

Da wannan sakamakon ya sa Dortmund ta koma ta biyu a kan teburin Bundesliga bayan an buga wasanni 25 a gasar ta bana.

Sai dai dan wasan yace wannan ba karamar rana bace a wajensa kuma bazai taba mantawa ba saboda haka yanzu yasamu inda zai nuna kwarewarsa.

Yaci gaba da cewa burinsa shine daman yasamu damar buga wasanni domin ta hakane za’a gane kwarewarsa da kuma baiwar da yake da ita.

Ya kara da cewa yana fatan zai cigaba da zura kwallaye a raga domin dai yaci gaba da buga wasa a kungiyar sannan kuma yana fatan zai wakilci kasarsa a gasar cin kofin duniya da za’a buga a kasar Rasha a wannan shekarar.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!