Connect with us

MANYAN LABARAI

Zaben 2019: Ban Ce Kar Buhari Ya Tsaya Takara Ba, In Ji IBB

Published

on

  • Jam’iyyun Siyasa Na Bukatar Sauyi
  • Ba Zan Ba Buhari Shawara A Fili Ba

Tsohon Shugaban mulkin soja na kasar nan Janar Ibrahim Badamasi Babangida IBB ya gargadi ‘yan siyasa da su guji furuce-furucen da zai iya kawo wa tsarin dimokradiyyar kasar nan matsala, irin furuce-furucen da ka iya tayar da tsimin rikincin kabilanci da na addini, ya ce lallai jami’yyun siyasan da ake das u a kasar nan na tsananin bukatar kwaskwarima.

Ya yi wannan bayani a wata sanarwa da ta sanya wa hannu, ya kuma yi mata lakabi da “My counsel to the nation”, IBB ya karyata rahotannin da ake danganta shi da ita waddda ta fito ta hannun mataimakinsa na musamman Mista Kassim Afegua cewar wai ya ce kada Shugaba Muhammadu Buhari ya sake tsaya wa takarar shugabancin kasar nan a zaben shekara 2019, “Wannan ra’ayinsa ne ba nawa ba”

Ya ce, “An jawo hankali na a kan wannan bayanin ne a sanarwa da aka yi a kan halin da kasa ke ciki musamman zaben shekara 2019 da sauransu, saboda haka ina son bayyana wa jama’a cewa a matsayi na na Dattijo kuma tsohon shugaban kasa ina da hanyoyin isar da sako kai tsaye ga masu jagorancin kasar nan ba tare da na bayyana abin da nake son isar wa ba a budadiyar wasika, saboda haka ra’ayi da maganganun da ke cikin sanarwa ra’ayi ne na wanda ya rubuta”

Ya ci gaba da cewa, shi mutum ne da ya yi imani da tattaumawa tsakanin bangare biyu a dukkan matsalar da ta taso, “Ni mutum ne da na yi imani da fuskantar lamurra a bayyane ba tare da tilasci ba, na yarda da warware matsala ta hanya bani gishiri in baka manda” in ji shi

Ya kara da cewa, abubuwan dake faruwa a ‘yan kwanakin nan a fagen siyasar kasar nan na tayar da hankali kuma ba za su taimaka wa talakan da ke cikin radadin matsanacin tattalin arziki ba, wanda kullum sai ya nemi abin da zai saka a bakin salati”

“Tun zamanin ina aikin soja har na zama shugaban kasa a mulki soja da tarihin rayuwa na bayan na tube kakin soja na koma farar hula a kullum buri na guda daya ne shi ne kuwa samar da ‘yanci ga mutanenmu kuma na tabbatar da cewa wannan ‘yancin ba zai samu ba sai ta hanyar tsarin mulkin dimkradiyya, wasu sun dauka wannan ‘yancin ya zama wani hanyar kawo wa tsarinrin dimokradiyya cikas da zagon kasa ta hanyar banbadanci da yada kalaman batanci suna boye wa a karkashi inuwar kabilanci da addini” in ji IBB

Ya ce, duk da irin dimbim kalubalen da ake fuskanta ya yi imanin cewa, ‘yan siyasan mu zasu yi tsayin daka wajen yin aiyukan da zai rage matsalar da alumma kasar nan ke ciki.

Ya kuma kara da cewa, harkokin da ke faruwa a fagen siyasar kasar nan a halin yanzu tsakanin ‘yan siyasa da jama’ar kasa abu ne mai tayar da hankali, “Hankoron da ‘yan siyasa ke yi na canza sheka da tsare-tsare musamman ganin zaben 2019 na nan tafe abu ne da ya kamata ayi maraba da shi amma dole ne ya zama wadannan hankoron ana yin su ne da zuciya daya kuma a karkashi tsarin mulkin kasar nan, duk wani kokari da ya yi nesa da wannan tsari na dimokradiyya ya zama yaudara kuma abu ne da zai iya tarwatsa kasa ya kuma jefa ta cikin rudani”

Saboda haka, “Tsarin jamiyyun siysar mu na bukatar madogara mai karfin gaske da zai karfafu da akidu na gari, amma a halin yanzu jamiyyun siyasun da muke dasu da na tsananin bukatar kwaskwarima”

“Daman can ni ma’abocin tsarin jamiyyu guda biyu ne, amma a halin da kasar nan ke ciki hakan zai yi wuya, saboda haka wasu jamiyyun suna iya hadewa su karfafa juna domin samar da jamiyyar adawa mai karfi da zata fuskantar jam’iyya mai mulki” in ji shi

Janar Babangida ya kuma kara da cewa, “Tarihi ya nuna yawancin kasashen da suka ci gaba a harkar tsarin dimokradiyya jamiyyun siyasun su guda biyu ne sai dai a kan samu wasu kanana da ke zama masu gyara in manyan sun dan kauce ko farin jininsu ya fara gushewa, har yanzu ina nan da imani na na cewa kasar nan tsarin jam’iyyu biyu ne ya fi dacewa da ita”

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: