Connect with us

KASASHEN WAJE

Akwai Yiwuwar Amurka Ta Daina Sayan Mai Daga Benezuela

Published

on

A kokarinta na tilastawa kasar Benezuela ta gudanar da sahihin zabe mai adalci, Amurka ta soma tunanen takaita ko daina sayen man fetur din kasar a cewar Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Red Tillerson

Sakataren harkokin wajen Amurka Red Tillerson ya ce Amurka tana tunanin takaiata ko aza takunkumin sayen man fetur daga Benezuela a kokarin ta na matsawa kasar.

Ya bayyana hakan ne a zaman tattaunawar da suka yi da manyan kasar Argentina jiya Lahadi a ziyarar da ya kai kasar. Ya ce suna ganin yin hakan zai taimaka wajen tilastawa kasar ta gudanar da sahihin zabe mai adalci..

Amman Tillerson ya kara da cewa yana so a samo hanyoyin da zasu rage illar da takunkumin zai haifar ga kamfanonin man Amurka da wadansu kasashen da suka dogara ga samun mai daga kasar ta Benezuela.

Benezuela ita ce kasa ta uku mafi da ta fi sayar wa Amurka man fetur, kuma kamfanonin mai na Amurka sun ce hana shigo da man fetur daga kasar zai shafi ma’aikata a nan Amurka, kuma zai sa farashin man ya yi tashin goran zabi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!