Cece-kuce Kan Batun Makiyaya Kiyayya Ne Ga Gwamnatin Buhari — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYI

Cece-kuce Kan Batun Makiyaya Kiyayya Ne Ga Gwamnatin Buhari

Published

on


Ga dukkan wanda ke bibiyar harkokin siyasar kasar nan musamman ma a dan takadirin misali daga lokacin da sojoji suka ce sun ji sun gani ta wajen hadiye kwadayinsu na ci gaba da mulkar kasar nan da tsinin bindiga wato daga shekarar 1999 wato lokacin da gwamnatin sojan kasar nan karkashin tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalam Abubakar ya mika mulki ga zabbbiyar gwamnatin dimukuradiyya karkashin jagorancin Olusegun Obasanjo na jam’iyyar PDP dan kudancin kasar nan ya san da cewar fakewa da ake yi da batun rikicin makiyaya ba komai bane illa nuna kiyayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari don kawai yana cewar a bi gaskiya a matsayinsa na wadda ya fito daga tsatson Hausa Fulani.

Tabbatacce ne cewar, wannan tatcurza da ake yi na tsawon lokaci dangane da rikicin Fulani makiyaya da kuma manoma a bangarori daban-daban na kasar nan fiye ma da ayanzu amma ba a taba fitowa gadan-gadan ana nuna kiyayya karara ga wata gwamnati ba sai wannan

gwamnati ta Muhammadu Buhari.

Idan mai karatu zai waga baya lokacin gwamnati Obasanjo kowa ya san lokuta da dama an samu rikici mai tarin yawa tsakanin makiyaya da manoma yadda aka rika rasa rayuka da dukiyoyi tsakanin bangarorin musamman kamar a Jihohin Bauchi, Filato, Yobe, Jigawa, Borno, Adamawa, Taraba da Jihar Binuwai Jihar da rikicin da aka yi cikinta ke kokarin tada kurar da wasu ke son amfani da shi don kawo barazana ga hadin kan kasa wadda masu wadannan maganganu na cewar gwamnatin Buhari ce ke daure gindin wannan rikici sunanan a wancan lokacin amma sun gaza cewa komai don kawai shafaffe da mai ne da ya fito daga wani sashin kasar nan ke mulkarta.

Haka nan baya ga rikice-rikicen makiyaya da manoma na lokacin gwamnatin Obasanjo har ila yau lokacin takwaransa dan kudanci Jonathan dan jam’iyyar PDP ke jagorancin kasar na tsawon wajen shekaru 9 da rabi nan ma an yi ta hatsaniya tsakanin makiyayan musamman a Jihohin Adamawa, Taraba, Nasarawa, Filato, Binuwai da ma wasu bangarorin kudancin kasar nan aka yi ta kashe-kashe fiye da kima wadda a Jihar Binuwai kadai rikicin da aka rika yi ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa musanan tsakanin Fulani makiyaya da kuma ‘yan kabilar Tibi fiye ma da ayanzu amma awancan lokaci babu wani korafin rashin yin daidai daga wadancan mutane masu kokarin shafa bakin fenti ga gwamnati Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.

Hakan kuwa ta faru ne ba  don komai ba sai don shi Jonathan din na su ne da ya fito daga bangaren shafaffu da mai dake da kafafen yada labaran da kan iya mayar da fari ya koma baki don kin Allah duk da cewa kishin yankinsu da al’ummarsu ne ya yawaita gare su a kuma karkashin jam’iyyar da ta wuce doka.

Don haka alal hakika tunin an yi walkiya mun gane na duhu manufa ga duk ma’abucin gaskiya ya san da cewar, korafin da wadannan ‘yan gaza gani ke yi na cewar wai gwamnatin Buhari na jan kafa wajen kawo karshen rikita-rikitan da ake fama da shi tsakanin makiyaya da manoma a wasu Jihohi musamman na baya bayan da ya faru a Jihar ta Binuwai da ya yi sanadiyar rasa rayuka kusan 70 ba komai bane illa son rai da nuna kiyayya ga gwamnatin ceton talakawa ta Baba Buhari gwamnatin dukannin talakawan kasa ke jiran zuwa na tsawon lokaci don kai su ga

tudun tsira wadda ko a yanzu ma kwalliya na gab da biyan kudin sabulu kamar yadda mafi yawan jama’a ke cewa.

Don haka wannan marubuci ke tabbatarwa masu cewar wai gwamnatin Buhari na jan kan kafa da kuma goyon baya ga makiyaya kan wannan hatsaniya da su sani cewar suna ina lokacin da ‘yan kabilar Mambila a Jihar Taraba suka rika aiwatar ta kisan karf dangi ga makiyaya Fulani wadda aka kashe fiye da makiyaya dubu da dabbobi fiye da lissafi da gidaje fiye da 300 amma wadancan mutane su da kafofin yada labaransu suka yi gum da bakinsu basu ce komai ba.

 

Sani Gazas Chinade ya rubuto daga Damaturu,  chinade2015@gmail.com, 08036526185

 

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai