Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Yadda Kamarar CCTB Ta Fallasa Dan Sane A Legas

Published

on

Jami’ain ‘yan sanda na musamman dake karkashin rundunar ‘yan sanda ta jihar jihar Legas, sun cafke miji da mata a yayin da na’urar mai daukar hoto ta (CCTB) ta fallasa su  a bisa zargin yiwa wasu mutane masu wucewa fashi a anguwar Oshodi a cikin jihar.

‘Yan sanda sunce, wadanda ake zargin sune Segun Latoye da mai dakinsa Toyin Samuel, an kuma cafke su a ranar juma’ar data gabata a yayin da na’urar ta fallasa su har sau uku a yankin na  Oshodi a lokacin da suke sacewa masu wacewa kayansu.

Faifan bidiyon ya nuna yadda matar ta daukewa wata data zo wucewa wayotin ta na ta tafi da gidanka guda biyu a cikin jakar ta hannu da kuma wasu kudade.

Na’urar ta fallasa su a yayin da suka yi fashin,inda suka yi sauri suka shiga wata motar haya ta Bas suka bar anguwar ta Oshodi.

Matar da aka yiwa fashin, ta ankare ne a cikin ‘yan mintuna kadan, inda ta kai rahoto ga jami’in su kuma jami’an suka duba faifan bidiyon da Na’urar ta CCTB ta nada dake yankin  inda lamarin ya auku.

Na’urar ta bayyana hotunan wadanda ake zargin daga cikin mutanen da suke unguwar ta Oshodi a lokacin da lamarin ya auku.

Jami’an sun kuma  umarci mutanen dake yankin da lamarin ya auku, dasu tuntubi jami’ain duk idan suka ga wadanda ake zargin a yankin na Oshodi.

Wadanda ake zargin sunyi ikirarin cewar su ma’urata ne sun kuma amsa laifin su bayan da aka nuna masu faifan bidiyon dake dauke da hutunan su ayayin da suke aikata laifin a ranar Lahadin data gabata ‘Yan sandan sun kuma bayyana cewar, sun cafko wasu mutane biyu a yankin na Oshodi masu suna; Jelili Ganiu dan shakara 19 da Samson Owolabi dan shekara 23, wadanda suma sun fada komar ta ‘yan sanda ne a lokacin da na’urar ta CCTB ta fallasa su suna aikata laifi makamancin hakan.

Na’urar ta fallasa su a lokacin da suka saci wayoyin tafi da gidan daga mautane masu wucewa a kan gadar dake yankin Oshodi.

Na’urar ta tona su a yayin da suka saci wayoyin suka kuma mika su ga dayan da ake zargi wanda a yanzu jami’an na ‘yan sanda suke neman shi ruwa a Jallo.

Bayan sun aikata zargin satar da ake yi masu ne, jami’an suka bisu suka kuma cafko su a kan gadar ta Oshodi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai