Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Jirgin Kasa Ya Ci Rayuwar Wani Ma’aikacin NUC A Abuja

Published

on

Ya rasa ransa mintuna kalilan bayan ya gana da mahaifinsa mai sun Francis Idoko, marigayin mai suna Paul Francis ya rasu ne a lokacin da ke kan hanyarsa ta zuwa wajen aiki, inda wata Jirgin Kasa ta kashe shi a titin Arab da ke yankin Kubwa, a birnin tarayya Abuja da safiyar ranar Juma’a.

Da yake jawabi wa kamfanin dillacin labarai ta Nijeriya a gidansa da ke yankin Arab, kilomita kadan da inda tsautsayin ya auku, Francins Idoko ya ce, dansa mai shekaru 27 mai suna Paul Francis ya gamu da hatsarin ne a lokacin da ke hanyarsa ta zuwa wajen aiki. Ya bayyana cewar marigayi dansa, ma’aikaci ne a hukumar da ke kula da jami’o’ ta kasa (NUC).

Ya bayyana cewar, “Wajajen karfe 7:15 na safiya, a lokacin da ke kokarin zuwa aiki, Paul ya zo dakina muka yi magana domin yana son wucewa wajen aiki,”

“A lokacn da Paul ya shigo, mahaifiyarsa wacce ita ma take kwance kan gado, ya bukaci ta bashi canjin naira hamsin idan tana da ‘yan canji domin daga  wajen zuwa titin Maitama kudin hayar da ake amsa don zuwa wajen aikinsa,”

“Mahaifiyarsa ta shaida masa cewar ba ta da kananan kudi, ya dai samu aron dari biyu ya yi fatan cewar Allah ya sa masu Tadi din suna da canji, ya min bankwana ya fita,”

Ya ci gaba da bayanin yadda kuma ya samu labarin mutuwar dan nasa, “A lokacin da ya tafi ofis wajajen karfe 10:30 na safiya, wani abokina ya kirani a kayar salula ya bukaci na sake kiransa daga baya domin yana cikin halin gaggawa. Na kirashi daga bayan kamar yadda ya bukata, ya shaida min cewar dana ya mutu, na ce masa karya ne, hakan ba mai iyuwa ba ne, yaron da aka bashi kudin mota da safen nan, abun mamaki, ana haka sai wani makwafcinmu mai suna Hassan ya sake kirana shi ma ya shaida min hakan,”

Ya ci gaba da bayyana yadda aka yi ya rasa dan nasa “na kira matata, wacce a lokacin take tsaka da kallon TB, na shaida mata halin da ake ciki,”

Idoko ya bayyana cewar ‘yan sanda sun taimaka musu wajen kai yaro zuwa asibiti.

Mahaifin na wadda ya rigamu gidan gaskiyar dai ya misalta dan nasa a matsayin hazikin ma’aikaci mai ladabi sosai.

Wadda lamarin ya auku a kan idonsa, Sunday Garba, wadda kuma abokin marigayin ne ya shaida cewar suna kan hanyarsu ta zuwa wajen aiki ne hatsarin ta auku musu.

“Hatsarin ta auku ne da misalin karfe 8 zuwa 9 na safiya, a lokacin da Jirgin Kasan ke kokarin ketarewa, na kirasa a waya wayarsa a kashe, na ci gaba da lellekawa domin in ganosa bayan da motar ta sallake, me zan gani a lokacin kawai sai na ga gangar jikinsa. Ban san me zan yi a lokacin ba; sai kuka kawai,”

Majiyarmu ta tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sandan brnin tarayya Abuja Anjuguri Manzah, ya shaida cewar baida masani kan lamarin a lokacin da aka tuntubesa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: