Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Sanda Sun Kaddamar Da Binciken Dalilan Da Ya Sa Kenneth Ya Hallaka Kansa A Inugu

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen jihar Enugu ta fara binciken dalilan da kuma musabbabin da suka janyo wani magidanci ya rataye kansa har lafiya a yankin Iheakpu-Obolloafor da ke karamar hukumar Udunu a jihar ta Enugu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ta jihar, SP Ebere Amaraizu, ya shaida hakan a wani takardar manema labaru da ya raba a jiya lahadi a garin ta Enugu, wadda kuma ya bayyana cewar magidancin ya rataye kansa ne a ranar 21 ga watan Fabrairu, 2018 da misalin karfe bakwai 7 na safiyar ranar.

Kakakin Amaraizu, ya ci gaba da bayanin cewar wadda ya rasa rayuwarsa ta dalilin rataye kansa shi ne mai suna Kenneth Ugwuattama ya kuma yi bayanin cewar ya giciye kansa ne a jikin bishiya. Ya ce, an yi zargin (Ugwuattama) ya rataye kansa ne a wani bishiya da ke gaban gidansa.

Al’umman yankin Iheakpu-Obolloafor sun nuna alheninsu kan aukuwar lamarin, hade da jijanta wa iyalan marigayin, aukuwar lamarin sun ankara kawai suka hangi gawar, Kenneth Ugwuattama mataccece.

“Wadda ya rasa ransa shi ne mai suna Kenneth Ugwuattama, ya mutu yana da shekaru 40 a duniya, an yi zargin cewar ya rataye kansa da kansa ne a jikin wani bishiyar da ke gaban gidansa a wannan ranar,”

Kakakin rundunar ya nuna cewar tuni aka dauki gangar jikin mamacin zuwa asibiti a Oloallafor inda aka kai gawatar tasa dakin adana gawarwaki.

Ya bayyana cewar suna nan suna ci gaba da binciken dalilan da suka jawo wannan mutumin ya rataye kansa har lahira, don haka ne ya bayyana cewar yanzu haka gawar mamacin tana ajiye a asibiti sashin adana gawarwakin da suka mutu.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: