Connect with us

WASANNI

Arsenal Tanason Arteta Ya Maye Gurbin Wenger A Matsayin Kociyan Kungiyar

Published

on

Daga Rabiu Ali Indabawa Abuja da Salisu Jegus

Rahotanni daga kasar ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tana zawarcin mataimakin mai koyar da kungiyar Manchester City, Mikel Arteta a matsayin wanda zai maye gurbin Mista Wenger a karshen kaka.

Arasene Wenger dai yana fuskantar matsin lamba a kungiyar sakamakon rashin tabuka komai a wannan kakar wanda hakan yasa kungiyar take zaune a matsayi na shida akan teburin na firimiya inda maki 13 ne tsakaninta da kungiyar da take matsayi na hudu sannan kuma maki 33 tsakaninta da Manchester City wadda take mataki na daya.

Arsenal dai tasha kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta Brighton Albion a ranar Lahadi daci 2-1 wanda rashin nasarar yakara rura wutar rashin tabbas din na Arsene Wenger.

Mahukuntan kungiyar dai sun amince da irin aikin da Arteta yakeyi a Manchester City karkashin mai koyarwa Pep Guardiola wanda hakan yasa kungiyar take ganin zata tuntubeshi ko zai amince yakoma kungiyar da yayi shekara biyar yana bugawa wasa daga shekara ta 2011 zuwa 2016.

Har ila yau, Arsenal tana fuskantar kalubale daga tsohuwar kungiyar Arteta wato Eberton wadda itama take zawarcinsa wanda zai maye gurbin Sam Alladyce wanda shima babu tabbas zamansa a kungiyar.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: