Connect with us

WASANNI

Idan Muka Samu Nasara A Wasanni 4 Nan Gaba Mun Lashe Firimiya ­– Guardiola

Published

on

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewa kungiyarsa tana bukatar lashe wasanni hudu ne kawai domin ta zama zakara a agasar firimiya.

Guardiola ya bayyana hakane bayan da kungiyarsa ta lallasa Chelsea daci 1-0 a wasan da suka fafata a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester.

Ya ci gaba da cewa idan har yan wasansa suka cigaba da buga irin wasan da suka buga a wasan da suka doke Chelsea tabbas yasan sun kusa daukar gasar firimiya inda yace yana fatan zasu cigaba da nuna kwazo domin dai ganin sun lashe firimiya.

Manchester City ta yi fintinkau a gasar firimiya da tazarar maki 18 a kan tebur bayan da ta doke Chelsea da kwallo daya tilo wadda Bernardo Silba ya ci.

Silba, wanda yana daga cikin wadanda suka buga kwallo a raga a wasan da Manchester City ta casa Arsenal 3-0 ranar Alhamis, ya ci kwallon ne bayan da Dabid Silba ya cillo masa ita cikin dakika 35 da dawowa hutun rabin lokaci. ‘Yan wasan na Manchester City sun mamaye karawar amma sai da suka yi hakuri kan yadda bakin nasu ‘yan Chelsea suka tsare baya ba tare da wani kokari na kai hare-hare ba a wasan.

Kungiyar ta Antonio Conte ba wani hari kwakkwara da ‘yan wasanta suka kai a tsawon fafatawar, sai kokarin kare gida kawai suka yi.Yanzu an doke Chelsea a wasanta hudu daga cikin biyar na karshen nan na firimiya da ta yi, kuma ta ci gaba da zama da tazarar maki biyar tsakaninta da ta hudu Tottenham, matsayin da akalla kowace kungiya ke fafutukar ba ta samu kasa da shi ba idan ta rasa kofin na firimiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: