Connect with us

WASANNI

Kungiyar Gidano Ta Fara Da Kafar Dama

Published

on

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Kungiyar kwallon Kafa Ta Giodano da ke jihar Kano, za ta wakilci jihar a gasar cin kofin kwallon kafa ajin kwararru na kasa, wanda za a fara a wannan shekara cikin watan da muke ciki wato watan Maris. Kungiyar ta Giodano ta samu wannan gagarumar nasara ce a karkasshin jagorancin Alhaji Jamilu Wada Aliyu, wanda ya zage dantse dan ya yi tsayin daka wajen ganin kungiyar ta samu wannan tikiti.

A bangaren shirye-shiryen kungiyar na tunkarar wannan gasa kuwa, kungiyar ta gudanar da wasanni na sada zumunci da kungiyoyi daban-daban, domin tabbatar da tsayuwar kuniyar don tunkarar aikin da ke gabanta.

Babban mai horar da kuniguyar Usaini ya bayana farin cikinsa da wannan ci gaba da ‘yan wasan suka samu, abinda ya rage kawai shi ne, shirinsu na tunkarar wannan gasa ta cin kofin kasa na ajin kwararru. Ya bayyana haka ne bayan kammala atisayen da kugiyar ta yi na share fage a filin wasa na Kano Pillars dake Sabon garin Kano, don su ci moriyar samun wannan tikiti na buga wannan gasa.

“Na yi matukar farin cikin samun wannan nasara da ‘yan wasanmu suka yi gami da taimakon wasu kwararrun ‘yan wasa da suka ba da gudunmawarsu don samun wannan tikiti, wanda nake ganin shi ne makasudin samun nasaramu.

Da aka tambaye shi shin yaya zai iya kwatanta irin gudunmawa da hadin kai da Jamilu Wada ya bayar, da kuma shi kansa mai koyarwar? Sai ya ce, Dole ne in gode wa Shugaban wannan kungiya kuma mai daukar nauyinta, da tabbatar da ko da ha- maza ha-mata an samu wannan nasara, wadda kuma ita ce babban burinmu.

Jagoran samar da sabon wannan ci gaba gasar cin kofin kasa ajin kwararru Alhaji Jamilu Wada Aliyu, ya ce, ya yi imanin ‘yan wasansa na da kwarin gwiwar samun nasara.

“Ina da tabbaci da imanin akan ‘yan wasannan za su taka muhimmiyar gudunmawa a nan gab. In ji Alhaji Jamilu Wada, kuma kungiyar za ta halarci mataki na biyu na gasar.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: