Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Isah: Hamshaki Kuma Shahararren Mai Garkuwan Da Aka Damke A Neja

Published

on

Biloniya kuma wani babban jigo a harkar garkuwa da jama’a Chukwudumeme Onwuamadike wand aka fi sani da Ebans yana fuskantar shari’a, akan zargin da ake mashi na wasu al’amuran ayyukan aikata laifukan da yayi , musamman ma garkuwa da jama’a. Sai kuma gas hi an kamawani kasurgumi wani shi ma babbanmai kudi ne, wanda aka fi sani da Isa Maiturari an kama shi wanda rundunar ‘yansanda ta jihar Niiger ta yi.

Ba kamar Ebans ba shi Maiturari  mika kai ya yi saboda kaddara ta riga fata, saboda na riga na kama shi, inda yakecewa shi yana son ya mutu ne.

‘’Na riga na roki Allah cewar ina son na mutum wannan shekara, saboda na gaji da wannan rayuwa, ya Allah ka dauki rayuwata ina son na mutu, ina son na mutum, wannan ita ce addu’a ta.’’

Wannan addu’ar dan shekara 61 Isa Maiturari wanda wani atsabibin mai garkuwa da jama’ane, kuma dila ne a yawancin motocin da aka sace a jihar Niger.

Maiturai shi dan asalin Karamar Hukumar Paikoro ne na jihar Niger an kama shi ne, a sau takwas a cikin shekara  29, makon da ya wuce, kokacin da jami’an’yansanda daga tawaga mai suna ‘’Operation Obsolute Sanity, daga gidan shi Sauka Ka Huta,  wani wuri da yake cikin Minna jihar hedikwatar jihar Niger.

Maiturari yanamata uku,’ya’ya 29 ya dade yana damawa a al’amuranda suka shafi aikata laifuka, da suka fara daga garkua da jama’a, amsa da kuma sayar da satattun motoci da ga jihohin Niger, Kogi, Kaduna, da kuma jihar Kano, har ma da babban birnin tarayya Abuja.

A shekarun hudun da ya dauka yana garkuwa da jama’a, a jihar shi mai Turari ya bayyana cewar shi da ‘yan tawagar sa, sun sami kudaden da suka kai Naira milyan dari bakwai da ashirin N720 .

‘’ Na hadu da matsaloli da yawa daga harakar garkuwa da jama’a, shi yasa naga ya dace in bar waccan harkar, na shigata sayen satattun motoci, na sha yin haka , har shekaru 29 yanzu.’’

‘’Koda yake na bar wannan harkar cikin shekarar 2013, amma dole na dawo cikin shekarau uku da suka wuce, saboda halin rayuwar da ake ciki’’.

‘’Amma na yi addu’a ga Sarki Allah ina son na mutu  a wannan shekara, na gaji da wannan rayuwa, ina son Allah ya dauki rayuwata wannan shekara, don Allah a barni na mutu’’.

Maiturari amma duk da haka ya bayyana cewar bai da wani da na sani akan laifukan da ya aikata, adanda suka sa ya tafi kurkuku har sau bakwai.

‘’Bani da wani dana sani akan dukkan abubuwam danayi cikin shekaru 29, amma kuma yanzu lokaci ne na mutuwa, abin da nake jirayanzu ke nan, ina rokon Allah ina son na mutum wannan shekara’.’

An daisamu bayanin cewar cikn shekaru 29 da suka wuce, an kama Maiturari da kais hi kotu har sau bakwai, amma kuma daga baya yana samun ‘yancinkan shi, a wani al’amari mai daure kai.

An samu bayanin cewar duk lokacin da ya samu ‘yanci daga fursuna Maiturari yak an kira jami’an tsaro ne, ta waya, yana masu ji da kai, ya fito daga gidan fursuna zai kuma ci gaba da harkokin da ya saba kamar yadda kowa ya san shi.

A shekarar 2001 Maiturari an kore shi daga jihar Niger ne wanda tsohon gwamna marigayi Abdukkadir Kure ya yi, daga can ne ya koma jihar Kano, inda ya ci gaba da harkar shi da satattun motoci.

Babban mara tsoro kuma mai garkuwa da jama’a, an san shi a harkar arkalla ta satattun motoci ga wadanda yake hulda da su tsakanin Nijeriya da kuma Nijar.

Manyan kasuwannin shi a Nijeriya sun hada da Kano, Kaduna Abuja, Lagos, da kuma jihar Sokoto.

Majiyar tamu ta bayyana cewar Maiturari yana da wayo saboda kudaden da ya samu ta harkallar aikata laifuka, yana gidaje fiye da 35 masu kyau a jihohin Niger, Kaduna, da kuma Kano.

Ya sayi motar sata ta farko akan Naira 400 ya kuma sayar da ita akan kudi Naira 800 a Kano.

Ita dai motar an kawo ma shi ita har gida ne, wanda daya daga cikin ‘ya’yan shi yayi, ya kuma ce ma shi, mai motar yana son sayar da ita.

Wannan shi ne fara harkar arkallar shi ta sayen satattun motoci, kuma shekaru 29 da ya yi Maiturari ya sa al’ummar Paiko suna  mai kallon , ko ya fi karfin Hukuma ne.

Kuma saboda rayuwar shi ta aikata laifuka babban oga wanda shi daga iyali ne masu daraja a Paiko, ya bata da ‘yan uwansa, in banda matar shi da kuma’ya’yan sa.

Lokacin da ka kama shi shi da wani dan shi aka kuma fito dasu aka nuna shi da wasu ‘ya’yanshi, dukkannin mata uku sun zo ofishin ‘yansanda na Bosso, domin nuna mashi suna tare da sh kota halin kaka.

Tun lokacin da aka kama shi ya taimaka wa’yansanda an samu motoci 35 daga Lagos, Kaduna, Kano,  da kuma Niger, sai kuma sauran wuraren daya sayar dasu.

Koda yake dai ba daya daga cikin matan wadda ta nuna shirye take ta yi bayani akan yadda aka kama mijin nata da kuma danta, wani daga garin nasu ya ce, Maiturari, wani babban mai harkar satattun motoci ne a Nijeriya.

‘’Kowa a Paiko ya san shi a matsayin shin a mutum, amma kuma mutum ne wanda dole asa alamar tambaya, dangane da halinsa. Amma kuma mutane suna jin tsoron shi, saboda duk lokacin da ka kama shi, kafin asana bin da ake ciki sai a ga ya dawo.’’ Akwai lokacin da aka harbe shi a kafa, har yana dangyashi, wasu daga cikin ‘ya’yanshi na yin harkar da ya ke yi’’.

Jami’inhulda da jama’a na hedikwatar rundunar ‘yansanda ta kasa ACP Moshood Jimoh ya bayyana Maiturari, shi ne mai arkallar  satattun motoci, da aka dade ana nema a jihar Niger.

Ya bada tabbacin cewar wanda ake zargi da aikata laifin, zai fuskanci hukuncin da shari’a ta yanke, a wannan karo, ya kuma kara da cewar yanzu masu motoci su samu su runtsa.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!