MAHANGA: Barace-baracen Kananan Yara A Titinan Kasar Nan: Ina Mafita? — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MAKALAR YAU

MAHANGA: Barace-baracen Kananan Yara A Titinan Kasar Nan: Ina Mafita?

Published

on


Tare da

Musa Muhammad 08148507210   mahawayi2013@gmail.com

Akwai abubuwa da dama, wadanda idan mutum ya yi dubi zuwa garesu za su dagula masa rayuwa ya ma rasa abin da ke masa dadi, musamman idan aka yi dubi da yadda wasu abubuwan ke jawo wa ga rayuwar al’ummar da abin ya shafa.

Wasu daga cikin wadannan abubuwa, wadanda kuma zan iya cewa babu wani mai farin ciki da shi, shi ne yadda ake samun kananan yara masu kananan shekaru suna bara a kan tituna, musamman a wasu manyan garuruwan kasar nan.

Irin wadanan yara, wasu lokuta ma za ka tarar da cewa kanana ne matuka, ta yadda in da suna gidan iyayensu ne, hatta wanki ko wanka mai sai an yi masu, wasu ma ba su wuce kwana da iyayensu mata a gado daya ba. To amma sai ya zama an raba su da iyayen nasu an jefa su bariki, wa zai yi masu wanka, wa zai yi masu wanki da sauran hidindimu?

A irin wannan ne wata rana yi kicibis da wasu yara makale da dan kwanonsu wai suna bara. Wadannan yara, yara ne kanana, wadanda idan da kai ne mahaifinsu, ko ke ce mahaifiyarsu, ba za ku iya sa su kowane irin aiki ba. Kuma kamata ya yi a ce suna zaune tare da iyayeynsu suna zuwa makarantar Islamiyya da ta boko.

Idan aka rinka kwasar irin wadannan yara ana turasu wasu garuruwa da sunan wai karatun allo, to wane irin karatu ne wadannan yara za su yi, wadanda hatta abincin kirki ba ishesu ba? Ya ake son su yi rayuwarsu, ya ake ganin tasowarsu za ta kasance?

Idan duk aka je aka dawo za a taras da cewa wadannan matsaloli ne da suka dabaibaye kasar Hausa, abin takaici! Kuma yawanci ana fakewa ne da addini, sai a ce wai yaro zai tafi neman ilimin addini, alhali ga yara nan suna haddace Alkur’ani mai girma a gaban iyayensu, suna zuwa makaranta su dawo gidajensu ana lura da lafiya da tarbiyyarsu.

Shi kuwa wancan an tura shi wani gari an hada shi da wasu, ba uwa ba uba, Malaminsu, wanda shi kuma yaran sun yi masa yawa, wasu lokuta ma yaran kan fada cikin wani mawiyacin hali, ko ya kwashi wasu miyagun halaye, shi Malamin bai ma sani ba.

A matsayina na dan jrida na sha haduwa da irin wadannan matsaloli da dama, na sha samun labarai masu bakanta rai game da irin halayen da wadannan yara kan shiga, wanda wasu labaran ma ba a iya yadasu saboda takaicin da ke ciki. Domin akwai wani lokaci da ake samun yanayin da ake kama irin wadannan yara da aikata luwadi.

Saboda haka ne nake ganin wannan aiki ne da ya rataya a wiyan kowa, musamman iyaye, gwamnati da shugabannin al’umma. Domin ita tarbiyya ta kowa da kowa ce, idan ta gyaru, to al’umma ce za ta ji dadi, idan kuma ta lalace, to al’umma ce za ta kwashi kashinta a hannu.

Ina so a yi mani kyakkyawar fahimta a nan, ba wai ina so ne in hana masu ra’ayin tattara yara don koya masu karatun allo ba, abin da nake nufi a nan shi ne, a samu yaran da suka san inda ke masu ciwo mana, wadanda za su iya yi wa kansu hidindimu, wadanda za su iya bambance damansu da hagunsu.

A kwanakin baya na dan rubuta irin wannan abu na lika a shafina na facebook, domin abin ya dameni. To irin yadda na ga jama’a na mayar da martani, sai na gane ashe dai abin yana damun kowa.

Ga abin da na rubuta da kuma wasu daga tsokacin da aka yi:

Abin da na rubuta

Lallai akwai hisabi!

Dubi wadannan yaran, wadanda ba su wuce kwana da iyayensu mata a gado daya ba, amma an tura su wani gari na nesa, su ke fita su nema wa kansu abinci. Anya babu matsala a nan Duniya da gobe kiyama, musamman ga iyayensu?

Wasu daga cikin martanin da aka yi.

HASAN GARKO

Mutane suna Daukar wa kansu nauyi, kuma sai su kasa  saukewa. Iin ka  bincika uban su  ba  matarsa  daya  ba.

MUHAMMAD IBRAHIM

Malam, yau din nan wadannan yaran sun shigo NUJ suna ’yan tsince-tsince har suka zo shan ruwa a masallaci, ina kallansu. Akwai dai matsala a Arewa. Allah ya ganar da mu.

HAJIYA RABI SALISU

Allah ya kyauta. Ina da guda biyar a cibiyata ta kula da marayu ‘orphanage’ yanzu haka. Imanin Malam Bahaushe na da bukatar gyara don ya yi daidai da addinin musulunci da hankali !!!

ABDULRAZAK YAHUZA

Gaskiya kam, Malam… Abin sai dai addu’a kawai!!! Amma akwai rashin imani a ciki.

AWWAL BAUCHI

Tabbas akwai matsala.

ALHAJI UMARU DIKKO

Jahilce ne ke kawo shi.

NASIRU YAKUBU

Matsala fa ai sai dai Allah ya yauta

RABI’U INDABAWA

Allahu Akbar, Allah ya kyauta

JIBRIL SHUAIBU

Hakkun

SANI HASAN

Bahaushe mai ban-haushi.

Zan rufe wannan rubutu nawa na wannan makon da yin kira ga Hukumomin da abin ya shafa su dubi wannan lamari, don a san gyaran da za a yi don gyaran al’umma. Su kuma iyaye su sani ’ya’yan da Allah ya ba su, ya ba su ne amana, don haka zai tambayesu amanar da ya ba su.

 

Advertisement
Click to comment

labarai