Connect with us

BIDIYO

Mu Dage Har ’Yan Kudu Ma Su Yi Koyi Da Mu –Ddough Abokina

Published

on

Daya daga cikin matasan da suke wakokin Ingausa (Hiphop), Ddough Abokina, wato AOTM, ya bai wa ’yan uwansa mawakan Arewa kwarin gwiwa kan cewa su ma su dage wajen nuna basirar kirkira a wakokinsu har sai mawakan Kudu sun dawo su na koyi da su.

Amma AOTM ya kara da cewa, hakan zai samu ne kawai ta  hanyar kawo sababbin abubuwa na fasaha a fannin Hiphop na harshen Hausa, ya kuma ce, “ba lallai ne mu rika daukar wakarsu mu na juyawa ba; mu ma za mu iya kirkirar namu, kuma su karbu a duniya fiye da nasu din.”

AOTM, wanda ya zanta da LEADERSHIP A YAU LAHADI, ya cigaba da cewa, “hadin kai kadai mu ke bukata. Abin da na ke nufi da hakan shi ne, mu ma manyan da su ka iya kuma su ka karbu a idon duniya mu dage mu daga na kasa da mu, don su nuna wa duniya irin baiwar da Allah Ya yi wa Arewa bakidaya.”

Ya kuma kara da cewa, “idan mu ka duba rayuwar mawakan Hiphop na Kudu, kullum burinsu su ga sun daga junansu. Daga sanda suka ga tauraruwarsu ta fara disashewa, sai su fara zakulo na kasa da su ’yan Kudu su na haska su.

“Misalin idan ku ka duba rayuwar Don Jazzy, ganin cewar ya fara sanyi, sai ya kirkiri kungiyar Mabin Record, wadda ya sanya kananan mawaka masu tasowa, kamar su Reekado Bank, Koredo Bello, Dija, Tiwa Sabage da dai sauransu.

“Haka shi ma Olamide, ganin tauraruwarsa ta na haskawa ya na wakoki su na karbuwa sosai a idon duniya, sai ya kirkiri kungiyar YBNL, don ya taimaka wa na kasa da su kuma ’yan kabilarshi, Kungiyar ta hada yara kamar su Lil Kesh, Adekunle Gold, Bictor, Sikibi da dai Sauransu. Ya rika ba su wakoki da suka haskaka su.

“Sannan idan ku ka duba irinsu Ice Prince ’yan Arewa ne da su ka shiga Kudu, sai su ka kirkiri kungiyar Chocolate City, wadda a cikinta ya hada da manyan mawakan Arewa, kamarsu Jassy Jags, MI Abaga da sauransu. Wannan kungiya ta yi rawar gani wajen haska tauraruwar ’yan Arewa sosai. To, haka ya kamata gabadayanmu mu rika yi.

“Haka zalika P.Skuare su na daya daga cikin taurarin Afrika bakidaya wadanda su ka samu karbuwa sosai na wuce misali a duniya, amma abin dubawa a nan shi ne wadannan mawakan guda biyu haifaffun Jos ne kuma a Kano su ka girma, sai dai daga lokacin da su ka fara waka sai su ka gudu su ka hade da sauran mawakan Kudu su na aiki tare. Ko sau daya ba su taba dauko wani daga cikin matasan Arewa ba don su taimaka ma sa. Ka ga idan har sauran ma su ka ce za su yi haka, babu cigaba kenan a Arewa.”

Daga nan sai mawakin ya yi jan hankali da cewa, “da wannan ne mu ke janyo hankalin ’yan Arewa bakidaya da su hada kai, mu zauna lafiya da juna. Mu ma a nan Arewa za mu iya kokarin taimaka wa juna, kuma zai taimaka ma na kwarai da gaske, ta hanyar kirkirar kungiyoyi ko saka kananan mawaka a cikin wakokinmu. Mu taimaka wa juna, don mu sake fito da sunan Arewa kamar yadda su ma su ke taimakon bangarensu.

“Sannan mu yi kokari mu kauce wa kalaman batsa a cikin wakokinmu da kuma ha’intar juna ko ganin na fi wancan; ba zan taimaka mashi ba. Mu zama tsintsiya ma daurinki daya. Hakan zai taimaka ma na kwarai kuma Arewa za ta zama abar koyi.”

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!