2019: Takarar Buhari Nasara Ce Ga ‘Yan Nijeriya – Sanata Ibrahim Ida — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

2019: Takarar Buhari Nasara Ce Ga ‘Yan Nijeriya – Sanata Ibrahim Ida

Published

on


Ci gaba…

 Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a 2019, sai dai za mu iya kallon irin rikice-rikicen da suke faruwa a jam’iyyar APC, da kuma rikice-rikice tsakanin gwamnoni da Sanatoci, ko gwamna da ‘yan majalisa, ba ka ganin hakan zai kawo wa jam’iyyar cikas?

To ai mulki haka ya gada, kai sai a karshen mulki a kyale k aka ci kai kadai ba wata husuma? Duk inda ake mulkin duniya ko ina ne, wanda ke mulki da ke wajen mulki, wanda jam’iyyarsa da wand aba a ciki yake ba akwai wannan kiki-kaka din, haka siyasa ta gada, kuma haka za a ci gaba, haka aka fara kuma haka za a ci gaba har gobe. Mu juyo kan maganar da kai, APC ta kafa gwamnati yau shekara uku ke nan da wani abu, in wannan wata na biyar ya zo shekara uku ke nan za a shiga ta hudu.

Dole ne gwamnanoni ka gaya min shin ina ne ake da wannan rikicin? Akwai a Kaduna, akwai a Kano, akwai a Bauchi, ka san dalili? Duk masu kawo rigimar da jam’iyyar ba ta da tasiri, da ba zata iya cin zabe ba, da za su damu da ita ba.

Ai ganin karfin jam’iyyar ne, wadanda ke kai sun tsaya sun jajirce suna yi wa jama’a aiki, akwai kura-kurai nan da can, amma ka gaya min, mu dauki jiha Kaduna me ake fada? Ka ji an ce ya saci kudin jama’a? babu, illa dai kawai ka ji an ce ya yi kaza, ya je ya kori jama’a, to gaya min in an ce ya kori ma’aikata 20,000 da wani abu, amma ya dauki 30,000 da wani abu su mayr gurbinsu, shin wai yau ka je ka gaya wa wadanda aka dauka su 30,000 din nan cewa a a daukar taku da aka yi aiki kuskure ne, sai su yarda?

Kuma wanda ya sallami 20,000 ya dauki 35,000, ai shi mishi albarka za a yi, eh ya lura cewa akaw wasu abubuwa da ake na laifi ya tsaida su. lokacin da el-Rufa’i ya zo Abuja gidaje ya rika rushewa, ya hana bara, ya hana ‘yan babur, yau ka dub aka gani kowa daga masa tuta yake. Wadannan masu kiki-kaka ba su suke zabe ba, jama’ar gari su suke zabe, yau idan ka je ka ajiye akwatin kuri’a ina tabbatar maka cewa el-Rufa’i zai ci zabe fiye da yadda ya ci a baya, ka ga shi ke nan, wannan rikicin cikin gida ne, kuma har yau duk maganar ake.

Kwankwaso yana nan cikin jam’iyyar APC bai je ko ina ba, kuma har yau har gobe in ka dubi Ganduje har yau jar hula ya ke sawa, yadda aka taho a baya an samu sabani kadan, wannan ina tabbatar maka dinkewa za ayi. Zaben ya zo, Kwankwaso ya yi gwamna shekara takwas, ba zai koma gwamna ba, Sanata yake, wannan yana iya yi har illa masha Allahu har Allah ya dauki ransa.

Gwamna ya yi shekara hudu ta farko zai koma, ba abin mamaki bne ka tarar gobe sun kama hannu ana sharholiya kamar yadda aka saba. Sai Sokoto tsakanin Wamako da shi gwamnan na yanzu ake ta ikirarin cewar akwai rashin jituwa, amma me yake faruwa? Kullum suna tare, shin wanda yake yayi hamayya da shi kan wannan abin har ya je kotu yana neman cewa Tambuwal ba shi ya kamata ba, me ya faru? Cikin satin nan tare suke ya ziyarce shi.

Duk wadan nan abubuwa ka dauki Bauchi, eh akwai amma yanzu me? Duk korafe-korafen da cikin jam’iyyar APC na wadannan jihohi, wallahi tallahi babu abinda ba zai iya gyaruwa cikin dan lokaci kankani ba. Saboda haka ina so in tabbatar maka sanarwar da Shugaban kasa ya bayar ta cewa zai nemi ya sake tsayawa, yayi shi ne bayan masana da ‘yan siyasa da ke tare da shi da ‘yan uwa sun zauna sun dubi gaba sun ga cewa APC ba ta da matsalar cin zabe a Nijeriya, sun ga cewa wadan nan jihohin da suke da korafi da rikici, abu ne mai sauki a gyara.

Saboda haka babu wani abu da zai tayarwa da dan APC na gaskiya hankali, kuma dukkanamu yanzu kalu-balenmu shi ne, mu tashi tsaye mu tabbatar cewa duk wasu korafe-korafe, duk wasu rashin jituwa tsakaninmu mun gyara. Mulki dai na Allah ne, wanda zai yi gwamna daga nan har duniya ta tashi Allah ya riga ya tsara abinsa. Amma ya ce mu nema, saboda haka su masu nema wadanda har neman yake kawo masu rashin jituwa da masu mulkin ba laifi sukai ba, illa iyaka kirana ga dukkan dan jam’iyya shi ne, eh ka nemi mulki halal ne, kuma ka yi hamayyar siyasa halal ne, abinda yake haram shi ne, ka zo ka bata ruwan kai ka san ba sha za ka yi ba, amma ka zo ka gurbata shi, to shi ne ba shi da kyau. Saboda haka ina kira ga wadan nan don Allah don Annabi a zauna a yi maslaha, domin kalu-bale garemu wannan zaben da zai zo, ba don muna jin muma da rauni ba ko ba za mu iya cin zabe ba a a, ko wane zabe ka dauke shi kamar ba z aka iya cinsa ba, to sai kai aiki tukuru. Saboda haka wadan na korafe-korafe ba za su yi wa APC illa ba domin za a gyara su.

Yekuwar da Shugaban kasa ya yin a cewa zai tsaya, wallahi ta yi dai-dai, domin kamar yadda wasu suka ce in ma da bai tsaya ba da kotu za su kai shi, to ina daya daga cikin wadanda inda takarda ce zan sa hannu, domin na san mutum ne kamili, mutum ne mai akida ta alheri ga wannan kasa

 

To akwai wani tsagi na dattawan Arewa da suke ganin shekarun Shugaba Muhammadu Buhari sun ja, saboda haka kamata yayi ya b wa matasa masu jini a jika dama shi ya je gida ya huta, ya kake wadan nan dattawa da suke irin wadan nan kiraye-kiraye? 

To na farko dai akwai tsofaffi akwai dattawa, tsufa maganar shekaru ce, dattaku kuma maganar hankali da gabata. Saboda haka duk mai hankali ya san cewa girma na shekaru, in bai yi baka komai ba shi ne ya baka tunani, da hankali da za ka kalli gaba, kuma ya hana maka wasu abubuwa na gubata rayuwar dan-adam, in ka girma akwai wasu ababuwan da ba sa ma cikin zuciyarka, na daya ke nan.

Na biyu shi mulki da tsoho da yaro kowa yana da hurumin nema, illa iyaka mutanen da za su zo su jefa kuri’a su ne za su yanke hukunci, kashi 60 bisa 100 na masu jefa kuri’a matasa ne, shi wai me zai hana matasan nan su hada kansu, jira suke sai an ba su?

Babu wanda zai ba ka mulki ko waye kai, su zo su nema, su zo a yi gwagwarmaya da su, su tashi su kira ‘yan uwansu matasa su gaya masu cewa lokaci ya yi da za ku zabi ‘yan uwanku matasa. Wato matasanmu suna da wani abu, wai sai su ce a bar masu kamar wani na dole, a a ba haka bane, kamar ko wane dan Nijeriya. Ah to ina zuwa, dan shekara 70 ya ce zabe a Amurka, dan shekara 40 ya ci zabe a Faransa, Faransa tsofanta ya fi na Amurka, saboda haka magana ake ta shin zai iya aikin nan?

Allah ya jarabce shi da rashin lafiya, kuma Allah ya sa ya warke, duk wanda ya ganshi a yanzu ya san ya wuce murmurewa ya ma warke. Saboda haka maganar wasu dattawan Arewa ni ban dauke su dattawan Arewa ba tsofaffi kawai, saboda sun ga lokacinsu ya wuce, ko sun nema ba su samu ba, ko suna nema ba za su samu ba, sai suka ga lokaci, don haka suke cewa duk wani wanda ke da shekaru irin nasu ya dawo. Nijeriya tana bukatar shugaba wanda ya san jiya ya san yau, zai iya hango gobe. Shugaba wanda ya kai lokacin da kudi da kayan zamani ba su da wani tasiri a zuciyarsa, saboda haka duk wani wanda zai zo y ace lokaci ya yi zai bari, shi ne ya kamata ya bar maganar, kuma ba wani dattijo bane tsoho ne.

Sannan kuma su matasa kada su zauna su hada ahnnuwansu a girji su ce za a kawo masu mulki, babu wanda zai baka mulki sai ka nema, su tashi su nema, idan suka tashi Allah Ubangiji sai ya taimaka masu. Matasa su ke jefa kuri’a, idan matasa suka jefa kuri’a ga mai shekaru da yawa, ashe ke nan ba laifin mai shekarun bane laifin su matasan ne.

Kuma kar su manta matasan yau su ne dattijan gobe fa, idan matashi yana tunanin shi matashi ne, sai ka ga kafin ya Ankara ya fara furfura, nan da nan sai ka ga lokacin ya wuce. Amma in ya zamana har yanzu ba su nema ba, sai ka ga dan shekara 80 ma ya zo ya karba daga hannun dan shekara 70.

 

Kana cikin kungiyar Dattawa a wannan yanki na Arewa, wanda kuma a baya-bayan nan yankin yana fama da rikice-rikice na kabilanci da kabila kaza da kabila kaza, satar shanu ne da sace garkuwa da mutane, wanda har ta tsohon Ministan tsaro wato TY Danjuma ya fito yana cewa sojojin Nijeriya ba za su iya kare jama’a ba don haka mutane su dauki makami su kare kansu. Ka san tsaro kamar yadda shi ma ya san tsaro, me kake jin wannan kalami ya za jawo?

To Alhamdulillahi wannan tambaya ce mai muhimmanci, kuma zan ba da amsar ta cikin sauki. Kamar yadda ka fada Janar dan Juma dan Arewa ne, Janar dan Juma dan Nijeriya ne, kuma gogaggen soja ne, idan zai fito yayi wannan furuci a halin yanzu, to menene dalili? Wannan dalili zan ba da shi cikin sauki.

Ina karanta ‘Whats’app’ sai na ga wani labari, ‘wai me ya kawo?’ Mutumin nan ya ce, a zamanin Abdullahi Bayero, sai aka kawo wasu ‘yan Nepu da laifin sun zagi Sarki an daure su an kawo su gaban Sarki. Tunanin kowa a fada shi ne Sarki zai sa abuge su ko ya sa a daure su, sarki ya gansu ya ce me ya faru, aka ce ai sun zagi Sarki ne, sarki ya ce a kwance su su tafi.

kowa ya yi ta mamaki, abinda sarki ya ce, “Iyayen yaran nan da kakanninsu idan za mu wuce zuwa suna jinjina suke suna gaishe mu, suna Allah ya kara mana nasara, Allah ya kiyaye ka. So suke su gammu su ga iyayenmu su ga kakanninmu, ashe idan kuwa ‘ya’yansu suka zo suna zaginmu ai mu ya kamata mu zargi kammu.” To kada mu kalli Dan juma, mutum ne zai iya kuskure, amma mu kalli abinda y ace, ni na san sojan Nijeriya kashi 99 na sojan Nijeriya sahihai ne masu kaunar kasarsu, sun sadaukar da kansu don su kare Nijeriya, amma akwai bara gurbina daya ke nan.

Na biyu, yanzu zamani ya zo mutane satar kayan soja suke ko na jami’an tsaro su tare hanya, duk wanda ya gansu zai ce soja ne, ni dinnan an taba tare ni akan hanya  mutum ya sa kayan soja, amma da hango na san ba soja bane, saboda ni na yi mu’amala da soja.

Ana sojan gona da soja ana yin abubwa, illa iyaka D juma ya kai matsayin da duk abinda zai wa Nijeriya  ya yi, amma kuma duk abinda Nijeriya za ta yi masa ta yi masa, saboda haka ya sani cewa duk furucin da ya yi a yanzu duk abinda ya fad aba wai yana fada ne a inda yake fad aba, yana mgana a Nijeirya gaba daya da duk duniya, duk Kalmar da ya fada za ta yi tasiri.

Saboda haka don Allah don Annabi irinsu wadanda yau idan cewa yayi yana neman ya ga Shugaban kasa kafin magariban nan zai ganshi. Duk abinda aka yi ya bata masa rai ya lura da cewa babba fa shi juji ne, saboda haka ya sami hanyar da zai rika yi wa masu mulki magana, ba sai ya fito ba yayi kalamai wadanda za su iya jawo wata husuma ba.

Kuma gaskiya abinda y ace din nan wallahi akwai mtsaloli a Arewar nan tsintsiya madarinki daya wadda Shugabbni su kai mulki ba tare da sun yi la’akari addininsu ko kabilancinsu ko jinsinsu ba. Saboda haka bai kamata irin wadan nan kalamai su rika fita daga bakin irinsu ba. To amma mu kuma ‘yan Arewa abinda ya kamata mu yi gaskiya mu zauna mu yi tunani, idan muna son Arewa ta zama daya, to mu zama daya, ya zama farin cikin wancan shi ne na wannan, amma ba za mu zauna haka kawai kara zube ba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai