Kannywood A Zamanin Afaka… — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

BIDIYO

Kannywood A Zamanin Afaka…

Published

on


Nada Babban Sakataren hukumar tace finafinai ta jihar Kano, Isma’il Na’abba Afakallah, da gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi ya na da dogon tarihi, domin an yi nadin ne ba don cancanta ba, illa don wasu dalilai na siyasa da nufin kyautata masu sana’ar shirin fim a jihar ta Kano. To, amma daga dukkan alamu babban daraktan bai fahimci hikimar da Gwamna Ganduje ya yi ta nada shi ba, idan a ka yi la’akari da yadda a kullum ya ke raba gari da mafi yawan ’yan fim.

Idan dai za a iya tunawa, masu sana’ar shirin fim a jihar sun sha mummunan kalubale da azabtarwa a zamanin tsohuwar gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau lokacin da a ka nada Abubakar Abdlkarim Rabo a matsayin shugaban hukumar ta tace finafinai ta Kano bayan bullar bidiyon badala na Hiyana.

Irin salon mulkin da Rabo ya gudanar a kujerar shugabancin hukumar ya bude wagegiyar baraka tsakanin gwamnatin da masu sana’ar, inda shi kansa Afakallah ya na daya daga cikin wadanda su ka yi ta faman gwagwarmayar kalubalantar salon mulkin na Rabo.

To, amma fa kafin zuwan Rabo tabbas gwamnatin Shekarau ta dama da ’yan fim kuma ta taimake su ta hanyoyi da dama. A takaice ma dai, har kawo yanzu ba a yi wata gwamnati a jihar Kano da ta zuba jarin kudi a cikin masana’antar Kannywood kamar gwamnatin Shekarau ba, domin ko a bangaren hukumar A Daidaita Sahu da duk mako sai hukumar ta dauki nauyin shirya fim guda daya, wanda a ke nuna wa a gidan talabijin, don wayar da kan jama’a, kuma ’yan fim a ke bai wa kwangilar shirya wadannan finafinai.

Hakan ya farfado da tattalin arzikin masana’antar ya kara ma ta yalwa da walwala. Baya ga wannan kuma, masu sana’ar da dama sun amfana da kwangiloli ko rancen kudi, don habaka sana’ar.

To, amma duk da wannan kyakkyawar alaka ta taimakon juna da a ke akwai a tsakanin ’yan fim da waccan tsohuwar gwamnati, yayin da Rabo ya fara kama su ya na daurewa, ya na kuntata mu su, sai dangantakar ta yi tsami.

Hakan ya bai wa babbar jam’iyyar adawa a jihar lokacin wancan zamani, wato PDP, karkashin jagorancin Injiya Rabiu Musa Kwankwaso fara zawarcin ’yan fim, domin taya PDP din yakin neman zabe tare da yi mu su romon bakan cewa, za a kyautata mu su a ba su ’yancinsu, sannan a daina tsangwamar su a jihar matukar sun taya ’yan adawar yakin kafa gwamnati.

Wannan ya sanya mafi yawan ’yan fim su ka fara yin tururuwa su na mara wa Kwankwaso da tawagarsa baya, saboda neman ’yanci kansu daga mulkin Rabo. Daga nan ’yan fim su ka fara yin wakoki na sukar gwamnatin da kuma yabon ’yan adawa.

A lokacin da wannan dangantaka ta fara yin tsami, gwamnatin Shekarau ba ta iya fahimtar irin illar da Rabo ya yi ma ta ba har sai da zabe ya karato, lokaci ya riga ya kure ma ta. Daga nan wasu daga cikin gwamnatin su ka fara farautar kuri’ar ’yan fim a na rarrashin su a kan su zo a sake tafiya tare a na yi mu su romon bakan ba za a sake ba.

To, amma idanun mafi yawan ’yan fim ya riga ya rufe, ba za su sake gaskata gwamnatin Shekarau ba, domin a ganinsu ya na ji ya na gani a ke kama su a na daure su. A haka a ka tafi zaben 2011; Allah Ya amsa bakin ’ya fim, gwamnatin Shekarau ta fadi, a ka sake kafa ta Kwankwaso.

Babbar hikimar da Kwankwaso ya yi a dawowarsa mulki karo na biyu shi ne, kin yarda a dauki ’yan fim a matsayin batattu ko ’yan iska. Karewa ma umarni ya bayar cewa, su je duk inda su ke so su gudanar da sana’arsu, ciki kuwa har da sabuwar unguwar da ya gina ta rukunin gidan Kwankwasiyya, saboda a cewarsa, fim ma sana’a ce mai muhimmanci. Sannan kuma Gwamna Kwankwaso ya hana malamai yawan aibata ’yan fim da kallon su a matsayin kishiyoyinsu a jihar.

Sa’innan a zamaninsa, gwamnatin ba ta dauki mataki na matsin lamba ta hanyar yawan kamawa da daure masu sana’ar ba. Sai a ka fito da dabara ta jan kunne, idan an yi kuskure tare da yin afuwa.

Wannan ya taimaka matuka gaya wajen rage matsalolin da ke cikin finafainai, domin duk wanda a ka daga wa kafa, ya kan ji dadi kuma ya kiyaye gaba. Haka a ka yi har zuwa karshen gwamnatin Kwankwaso, inda a ka zauna da lafiya da ’yan fim ba tare da samun badala ko rigingim masu zafi a tsakani ba.

Wannan ne dalilin da ya sanya mafi yawan ’yan Kannywood su ka yiwa Kwankwaso kara su ka zabi Ganduje bayan jam’iyyarsa ta tsayar da shi takarar gwamna a matsayinsa na mataimakin Kwankwaso a lokacin.

Lokacin da Ganduje ya kafa gwamnati, sai ya yi niyyar kyautata wa masu sana’ar fim fiye da yadda Kwankwaso ya yi tunda da ma a yakin neman zaben sa ya yi alkawarin cewa, dorawa zai yi daga inda Kwankwaso ya tsaya.

Tabbas Gwamna Ganduje ya cika wannan alkawari, domin sai ya dauki kujerar hukumar sukutum ya damka wa ’yan fim, inda ya dauki daya daga cikin, wato Afaka, ya nada shi a matsayin babban sakataren hukumare, wato shugabanta kenan a gwamnatance kuma a gwari-gwari.

Hakika ba za a ce Afaka bai yi kokari ba ko kuma bai taka wata rawar gani a hukumar ba ga ’yan fim, to amma salon mulkin Rabo da hukumar tasa ta dauko a karkashinsa ya na kawo rauni ga hikimar da ta sanya gwamnatin Ganduje ta nada shi.

Misali a nan shi ne, a zamanin Afaka ne a ka bude ofisoshin hukumar a dukkan kananan hukumomi 44 da ke jihar da nufin bunkasa kasuwancin fim, to amma a zamani nasa ne kasuwar fim ta yi durkushewar da ba ta taba yin makamanciyarta ba, saboda hukumar ta hana yawancin manyan ’yan kasuwar fim sakat, wadanda su ne su ke raba kudade ga furodusoshin da su ke fita su dauki finafinan da a ke kai wa kasuwar.

Ga wanda ya san ta kan kasuwancin fim a Kano, zai iya gaya ma ka cewa, wannan dalili kadai ya isa ya hana a amfana da ofisoshin na kananan hukumomi 44 da a ka sa gwamnati ta kashe makudan kudi ta bude, ta saya mu su baburan aiki, sannan a ka dira wa gwamnatin nauyin biyan su albashi ba gaira babu dalili. Wannan kenan.

A zamanin Afaka ne a ka hade yawancin kungiyoyin fim waje guda a karkashin uwar kungiyarsu ta MOPPAN da nufin kawo ingantaccen tsari mai dorewa a masana’antar, amma a zamaninsa ne kuma hukumar ta ke farautar shugabannin kungiyoyin a wajen ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da nufin a kama su a daure. Ko a makon jiya sai da Afaka ya kai shugabannin kungiyar MOPPAN da na furodusoshi gaban hedikwatar rundunar ’yan sanda ta jihar ya na tuhumar su. Shin mene ne amfanin aikin da a ka shafe shekaru a na yi na hade kan kungiyoyin, idan har ba za a bar shugabanninsu su yi aikinsu ba?

Wani cigaba da Afaka zai iya yin ikirarin ya kawo shi ne, na shirya semina ta mutum 450, don bunkasa ilimin masu sana’ar da samar mu su da kwarewa. Kuma hakika gwamnatin Ganduje ta yi rawar gani, saboda yadda ta fitar makudan kudi wajen daukar nauyin wannan semina. To, amma babban abin takaici shi ne mafi rinjayen wadanda su ka amfana da semina din ba ainihin ’yan Kannywood ba ne, saboda tsarin da a ka bi wajen daukar mahalarta semina din ta hanyar intanet ne.

Kowa ya na da damar ya bude intanet ya latsa ya cike fom ya tura a dauke shi, maimakon a kira kungiyoyin ’yan fim a nemi su bayar da sunayen ma’aikatan da masana’antar za ta fi amfana idan sun kammala semina din. Wannan dalilim ya sanya a cikin mutane 450 din nan da su ka halarta, a na jin cewa, ba su kai rabi ba wadanda su ke yin sana’ar fim. Sauran kawai sun halarci semina din ne sun tafi ba tare da za su iya gwada abinda su ka koya ba. Wannan ba karamar asara ba ce ga Kannywood kuma ba karamar asarar kudi a ka saka gwamnati ta yi ba.

A zamanin Afaka ne kuma kullum idan an tashi hira da shi a kafafen yada labarai ya ke cewa, yaki hukumarsa ta ke yi da badala da munanan dabi’u a cikin finafinan Hausa. To, amma babban abin kunyar shi ne a zamaninsa ne ma’aurata su ka fara koyi da finafinan Hausa su na kashe junansu, kamar yadda shi da kansa ya furta a wata wasika da ya taba aike wa shugabannin kungiyoyin masu shirin fim.

A lokacin Kwankwaso, wanda ba a yin irin wannan ikirari na batanci ga ’yan fim ba, ba a taba samun Hausawa su na koyi da finafinan Hausa su ka kashe kawunansu ba, sai a lokacin Afaka ‘sarkin yaki da badala’!

Daga dukkan alamu dai Afaka bai gane cewa, Ganduje ya nada shi ne domin ya kyautata wa masu sana’ar shirin fim ba, domin gwamna ya na ganin sun cancanci a saka mu su, amma ba wai don Afaka ya gyara wani abu a tattare da su ba, saboda tare da taimakonsu a ka kafa gwamnatin. To, lallai hakika wanda duk a ka kafa abu da shi kuwa, ai don an yarda da nagartarsa ne kenan!

 

Za mu cigaba insha Allahu!

 

Advertisement
Click to comment

labarai