Sharhin Fim Din ‘Ranar Aurena’ — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Ranar Aurena’

Published

on


09097438402  habibsaddika@gmail.com

Suna: Ranar Aurena

Tsara labari: Yakubu M Kumo

Furodusa: Abdul Amart

Bada Umarni: Ali Gumzak

Kamfani: Abnur Entertainment

Jarumai: Ali Nuhu, Adam M Adam, Isa I Isa, Mustapha Musty, Asiya Ahmad, Garzali Miko, Asma’u Sani, Salisu Chali, da Babangida Jalingo.

Sharhi: Saddika Habib Abba

 

A farkon fim din an nuna taron bikin Nasir (Ali Nuhu) da Jamila (Asiya Ahmad) a na rawa a na waka a na gwangwajewa, ango ya na yin waka da kansa, abokansa su na ta ya shi rawa. Bayan nan an nuna Nasir a gidansa ya tare tare da amaryarsa a daren ranar angoncin, an nuna ya hawo wa kan bene gurin da dakin amaryarsa ya ke ya shiga ya umarce ta da su sauko kasa, domin ta raka shi sallamar abokansa, sannan ta taya shi yi mu su godiya, saboda hidimar biki da su ka sha. Jamila ba ta yi ko musu ba ta tashi ta bi angon nata su ka fito.

Sun zo matattakalar bene su na saukowa sai Nasir ya yi tuntube ya fadi. Jamila ta kwalla kururuwa; abokan su ka ji su ka taho a guje. Su na zuwa su ka tarar Nasir tuntuni ma ya riga ya sume. Su ka dauke shi ranga-ranga su ka ta fi asibiti. Su na zuwa likita ya yi gwaje-gwajensa ya tabbatar mu su da cewar kashin bayansa ya sami matsala. Sakamakon haka daga kugunsa zuwa kasa ya daina aiki.

Jamila tare da abokan Nasir suka shiga cikin tashin hankali su ka dauko shi su ka dawo da shi gida. Jamila ta fara jinyar sa tare da kaninta, Habib. Duk abinda ya ke so shi su ke yi ma sa. Ba su taba gazawa ba har tsahon shekara guda, kuma a tsahon shekara gudar nan Jamila ta na fita aiki, domin a yadda a ka nuna tun kafin su yi aure da Nasir ta ke yin aikin.

To, wannan aikin da ta ke fita sai Nasir ya fara zargin ta a kan ko ta na kula wani a waje sakamakon shi ba wani amfani ya ke yi ma ta ba tunda ba shi da lafiya. Nasir ya fara canja ma ta ya na ta yi ma ta kananan abubuwa, ta na shanyewa har sai da wataran maigidan Jamila a gurin aiki, wato darata din kamfaninsu, ya gan ta a hanya za ta tafi gida, ya rage ma ta hanya ya kai ta gida. Daga nan ya shiga cikin gidanta, domin ya duba mijinta. Su na shiga sai Nasir ya kara tabbatar da zargin sa a kan cewa, ta na kula wani. Ya kare mu su ta tas! har ya sake ta.

Tun lokacin da Nasir ya saki Jamila rayuwarsa ta fada cikin garari. Ba shi da mai kulawa da shi, mahaifiyarsa ta kawo ma sa kannensa, mace da namiji, domin su dinga kulawa da shi, amma dukkaninsu su ka gaza; ba sa yi ma sa abinda ya ke so a kuma lokacin da ya ke so, sabanin yadda Jamila da kaninta, Habib, su ke kulawa da shi a baya.

Har sai da ta kai mahaifiyarsa ta gaji ta zo ta dauke shi ta mai da shi gidanta ta na cigaba da kulawa da shi. A lokacin Nasir ya fara nadamar rabuwa da Jamila. Ita kuwa Jamila duk da sun rabu, amma ta na cigaba da bibiyar lamarinsa. Ta je gurin likitansa ta tambaye shi ko zai iya yiwuwa a yi ma sa aiki lafiyarsa ta dawo? Likitan ya ce ma ta, a na yi, amma sai a kasar waje.

Jamila ta tafi ta je ta sayar da gidanta na gado da wasu kadarorinta ta hada ta ba wa abokan Nasir Naira milyan 30 su ka fita da Nasir kasar waje a ka yi ma sa aiki ya sami lafiyarsa ba tare ya san wane ne ya biya ba.

Sai bayan sun dawo su ke fada ma sa. A nan ya kara nadamar abinda ya yi ma ta, sannan ya tafi gidansu a kan amai da aurensu. Sai mahaifiyarta fafur ta ki amincewa. Ya tura abokansa, ta ki amincewa, Ya tura mahaifiyarsa, ta ki amincewa, domin mahaifiyar Jamila ta ce ‘yarta ba za ta koma ba tunda ya yi mata mummunan zargi na zina. A haka har mahaifiyar Jamila ta aurar da ita ga wani a cikin zawarawanta. Nasir ya kara shiga cikin matsananciyar damuwa.

A ranar da Jamila ta tare da mijinta saboda halin da ta ke ciki na tunanin Nasir ya zama na babu abinda ta ke yi sai kuka. Mijinta ya na ganin haka ya tabbatar cewa zuciyar Jamila ba ta tare da shi. Hakan ta sa a daren ya sauwake ma ta. Bayan ta dawo gida, da safe mahaifiyarta ta ci ma ta mutunci ta kuma tabbatar ma ta cewar ba za ta koma gidan Nasir ba.

Sai daga baya Habib ya je ya sami Nasir ya ba shi shawara a kan akwai wani kawunsu a Zariya; mahaifiyarta ta na jin maganarsa sosai, idan ya same shi, za ta amince ko da a waya ya yi ma ta magana.

Ba da bacin lokaci ba Nasir da Habib su ka dauki hanyar Zaria su ka je su ka sami Kawu. Nasir ya ba shi hakuri sosai a kan abinda ya faru. A take Kawu ya kira wo mahaifiyar Jamila a waya ya ba ta umarni, kuma ta amince ba da bacin lokaci ba. Kawu ya kirawo wasu abokan arzikinsa a ka maida auren Nasir da Jamila.

Nasir da Habib su ka kama hanya su ka dawo gida, amma har a lokacin mahaifiyar Jamila ta na fushi da Nasir; ba ta goyon bayan komawarta; dole kawai a ka yi ma ta. Sai daga baya Nasir ya ba ta hakuri sosai, sannan ta yarda kuma ta hakura ta saka mu su albarka, Nasir ya dauki matarsa su ka ta fi.

 

Abubuwan Birgewa:

1- Wakar fim din ta yi dadi sosai kuma ta nishadantar da masu kallo.

2- Jaruman fim din sun yi kokari sosai gurin isar da sakon, musamman Asiya a matsayinta na sabuwar jaruma.

3- Daraktan ya yi kokari gurin gudanar da aikin fim din.

 

Kurakurai:

1- A cikin fim din ba a nuna cewar Nasir mawaki ba ne kuma a cikin tsarin biki wanda su ke faruwa a kasar Hausa ango ba ya zama mawaki a gurin bikinsa ko da mawakin ne; abokansa mawaka su ne za su yi ma sa kara tunda shi ango ne, amma sai ga shi Nasir shi ne mawaki a gurin bikinsa, amaryarsa tana can kujerar amarya ta na zaune, gurin ango kuwa babu kowa, saboda ya na can filin rawa ya na wakarsa. Wannan abin babu tsari a ciki. Idan so a ke yi lallai sai an yi wakar, za a iya saka wani ya zo a matsayin mawaki ya hau kan wakar, idan ta dace da lafazan.

2- Akwai gurin da Nasir ya kirawo Jamila su na magana a kan maganar komawarta gidansa, an ji Nasir ya ce, ‘abinda ya sa na kirawo ki, wani waje saboda mu yi magana’, amma mai kallo ya ga ne gurin da Nasir ya kirawo ta ai ba wani waje ba ne, kamar yadda Nasir ya fada; cikin gidansu ne, amma yadda Nasir ya nuna kamar wani wajen su ka fita daban.

3- Akwai gurin da Nasir ya zo ya na yi wa mahaifiyar Jamila magiya a kan ya na so ta bari matarsa ta koma gidansa, amma sai mai kallo ya ga Nasir a tsaye ya na nuna ta da hannu a matsayinta na surukarsa, sannan ma shi da ya zo rokon ta, ai a tsarin biyyaya da tarbiyya Nasir durkusawa zai yi tunda an nuna shi mutumin kirki ne. Hakan bai kamata ba.

4- Shin Nasir ba shi da wani dan uwan mahaifi ko mahaifiya babba namiji, wanda zai shigo lamarin aurensa ne? Tunda harka ce ta aure, ai maza yakamata a gani a ciki, ba mata ba, a al’adar Bahaushe, amma sai a ka ga Nasir daga shi sai mahaifiyarsa sai abokai su ne su ke taka rawar ganinsu.

5- Lokacin da a ka ji Kawu ya buga wa mahaifiyar Jamila waya a kan maganar komawarta, sai a ka ji Kawu ya fada ma ta cewar, ga Nasir kuka ya ke yi tunda ya zo, don a yanzu ma haka kuka ya ke yi, amma mai kallo bai ga Nasir ya na kuka ba a lokacin; idonsa kamas ya ke. A matsayin yadda a ka nuna Kawu a fim din babban mutum ne tsoho kuma mai fadar gaskiya, bai kamata a ji ya fadi wannan maganar wadda ba haka ta ke ba, wato karya.

6- Shigar da Jamila ta ke yi ta na fita ba ta kamata ba a matsayinta na matar aure, domin mayafin da ta ke sakawa ma ba shi da bambanci da na budurwa a kasar Hausa.

7- Lokacin da Nasir ya zo tafiya da Jamila bayan an mai da aurensu, sai a ka ji Jamilar ta fito falo ta fada wa Nasir har a lokacin ummanta fushi ta ke yi, sai a ka ga Nasir ya danna kai ya shiga cikin dakin ummar, domin ya ba ta hakuri. A matsayin Nasir na siriki bai kamata a ce ya danna kai dakin kwanan sirikarsa ba, ba tare da wani iso ba, saboda bai san a halin da zai riske ta ba kuma ya kamata a ce akwai alkunya a tsakaninsu har lokacin. Hakan bai kamata ba.

 

Karkarewa:

Fim din Ranar Aurena ya fadakar kuma ya yi kyau, amma akwai abubuwan da ya kamata a buda wa mai kallo, sannan kuma fim din ya yi kama sosai da fitaccen tsohon fim din Aisha da a ka yi a can shekarun baya ba tare da an sanar da mai kallo cewa shi a ka sake kwaikwaya ba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai