Abin Da Ya Sa Na Ke Sukar Gwamnatin Mijina –Aisha Buhari — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Abin Da Ya Sa Na Ke Sukar Gwamnatin Mijina –Aisha Buhari

Published

on


Matar Sugaban kasa Aisha Buhari ta bayyana cewar, tana suka da barazanar janye goyon bayan data ke bai wa yunkurin neman tazarcen shugaban kasan ne saboda kasancewar ta mace mai tsananin son adalci a rayuwarta.

Ta yi wannan bayanin ne ranar Asabar a yayin da take kabar takardar karamawar da jaridar Banguard ta yi mata na gwarzuwar mako. Misis Buhari ta shiga takaddama ne lokacin da ta tattauna da sashin Hausa na BBC a watan Oktoba na shekarar 2016 in da ta nuna fargabanta na cewa wannan gwamnatin ta kauce wa turbar da jama’a suka dora ta a kai a da kuma alkawuran data yi yayin yakin neman zabe.

Ta kara cewa, da wuya ta kara goyon bayan ta ga hankoron sake zaben da mijin nata ke yi in har bai sake tsarin wadanda suke kusa da shi ba da kuma tsarin tafiyar da mulkinsa.

“Har yanzu bai gaya mani ko zai sake tsayawa takarar zabe ba, in ma ya gaya mani to sai nayi shawara domin kuwa in har abubuwa suka ci gaba da tafiya yadda suke tafiya a halin yanzu, ba zan fita yawon yakin neman kuri’ar mata ba kamar yadda na yi a shekarun baya, ba zan sake tafka irin wannan kuskuren ba” inji Aisha Buhari.

A lokacin da Aisha Buhari ta zargi gwamnatin Buhari kwanakin baya, ya mayar mata da martanin cewar, ta rike ra’ayin tat a kuma tsayar da kanta a harkokin a matsayin matar aure, abin daya tayar da cecekuce a cikin al’umma.

Fiye da shekara 2 kenan, shugaba Buhar har ya fara shirye shiryen neman sake zabe a karo na 2 amman har yanzu bai yi wa majalisarsa garanbawul ba kamar dai yadda matarsa ta bukata.

Misis Buhari ta yi bayanin cewa, garabawul a gwamnatin na da matukar mahimanci  domin a bai wa wadanda suka yi aiki tukuru wajen samun nasarar Buhari a shekara 2015 suma su bayar da nasu gudumawa wajen tafiyar da mulki.

A bayanin nata na karbar karramawar da jaridar Banguard ta yi mata Misis Buhari bata yi bayanin ko ya zuwa yanzu an cimma hankoron abin da ta ke bukata ba ko a a, amma a watan Janairu ta watsa wasu faifan bidiyo dake nuna wasu sanatoci na yin tir da irin mulkin Shugaba Buhari.

“Daya daga ciki dalilanku na karrama ni shi ne wanna tattaunawar da na yi da kafar BBC, wadansu na ganin ina sukar gwamnati da nake wani bangaren ta, wasu da yawa basu ji dadin bayana dana yi ba”. Bayanan nata ya fito ne ta bakin jami’in wasta labaranta mai suna Suleiman Haruna. “Ina son bayyana cewa, na dauki wannan matsayin ne saboda hali na son adalci a tsakanin al’umma ba wai saboda rashin ladabi da biyyaya bane, kamar yadda kuka sani an zabi wannan gwamnatin ne saboda tarda da mijina da jama’a suka yi”

“A saboda haka ina mai amfani da wannan daman na bayyana cewar, ina nan tare da miji na a wannan hankoron na sake neman zabe a karo na biyu” inji ta.

Advertisement
Click to comment

labarai