Babban Taro: Jam’iyyar APC Ta Kafa Kwamitin Gudanarwa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Babban Taro: Jam’iyyar APC Ta Kafa Kwamitin Gudanarwa

Published

on


A jiya ne jam’iyya mai mulki ta APC ta fitar da jadawalin sunayen mutanen da za su jagoranci kwamitin Babban Taron jam’iyyar wanda za a gabatar.

A sanarwar da jam’iyyar ta fitar ta bayyana gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin shirya babban taron.

Jadawalin wanda Sakataren gudanarwar jam’iyyar APC, Osita Izumaso ya fitar, ya bayyana cewa membobi 68 na wannan kwamitin sun hada da gwamnonin jihohin Imo, Borno, Katsina, Oyo, Yobe, Kaduna, Filato, Adamawa, Kogi da Edo.

Haka kuma membobin kwamitin sun hada da tsoffi da sabbin Sanatoci da ’Yan Majalisa da wasu jiga-jigan jam’iyyar. Inda Sanata Ben Uwajumogu ke matsayin mataimakin shugaban kwamitin.

LEADERSHIP A Yau ta bankado cewa, da kyar aka shawo kan Gwamna Badaru har ya aminta da amsar wannan jagoranci, bayan da masu ruwa da tsaki da shugabannin jam’iyyar suka yi ta bada baki.

Haka kuma Gwamnoni hankalinsu ya kwanta kasantuwar Gwamna ne dan uwansu zai jagoranci kwamitin, wanda ko ba komi zai kare muradunsu.

 

Advertisement
Click to comment

labarai