Bauchi Ta Kudu: ’Yan Takara 21 Da Ke Neman Maye Gurbin Sanata Ali Wakili — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Bauchi Ta Kudu: ’Yan Takara 21 Da Ke Neman Maye Gurbin Sanata Ali Wakili

Published

on


Idan ba ku mance ba, Sanatan da ke wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu, Malam Ali Wakili ya rasu tun a ranar Asabar, 17 Maris 2018 a gidansa da ke Abuja bayan kwasan jiki da fadi a kasa.

Ya zuwa yanzu, jama’a daga wannan mazabar suna sake tururuwa domin neman sa’ar maye gurbin marigayin, kawo yanzu LEADERSHIP A Yau ta nakalto jerun mutane 21 da suka nuna sha’awarsu da fitowa a fafata da su daga jam’iyyu daban-daban da ake da su a kasar nan.

Wakilinmu ya kawo mana sunayen maza 17 a yayin da kuma mata 4 ke naman a zabesu domin su gaji marigayi Sanata Ali Wakili a wannan kujerar.

Jerin sunayen da muka nakalto su ne tsohon gwamnan Bauchi Malam Isa Yuguda, wanda shi ne suka fafata da Ali Wakili a zaben 2015 kan wannan kujerar ta Sanata, sai kuma Sanata Abubakar Maikafi, Dakta Danjuma Adamu Dabo, Barista Lawan Ibrahim, Honorabul Aliyu Ibrahim Gebi, Hon. Isah Abuh Yousouf, Garba Dahiru, Honorabul Maryam Garba Bagel (‘Yan majalisar dokokin jihar Bauchi mai ci a halin yanzu), Honorabul Aminu Tukur (Dan majalisar dokokin jihar Bauchi mai ci a halin yanzu).

Sauran su ne Dakta Yakubu Lame, Kwamared Sabo Mohammad, Honorabul Lawan Yahaya Gumau, Hon. Hussaini Umar (Majikiran Bauchi) Dakta Safiya Mohammed, Hajiya Hajara Yakubu Wanka, Balarabe Shehu Ilelah, Umar Faruk Gwadabe, Ahmed Shu’aibu (Raba Gardama) da kuma Malam Ladan Salihu, Malam Ahmed M. Salihu na ashirin da dayan da muka nakauto kuma shi ne Prince Mohammed Sani Hassan.

Kawo yanzu dai kowani dan takara na ci gaba da nuna bajintarsa gami da neman jama’a su zabesa, haka kuma wakilinmu ya labarto mana cewar baya ga wadannan 21 akwai wasu ma da suke sha’awar da a ce su ne masu maye gurbin marigayin, sai dai wadannan sune suka fi fito da bukatarsu a fili domin neman sa’a.

Yanzu yanzu dai kowa na jiran tsarin da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fitar kan wannan maye gurbin wannan kujerar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai